HausaTv:
2025-11-28@17:52:53 GMT

Senegal: Hambararren Shugaban Kasar Guinea Bissau Ya Isa Kasar Senegal

Published: 28th, November 2025 GMT

Ma’aikatar harkokin wajen kasar  Senegal ta sanar da cewa hambararren shugaban kasar Guinea Bissau UOumar Sissoko Embalo ya isa kasar a cikin wani jirgin sama na musamman.

Sanarwar ta ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Senegal ta fitar a jiya Alhamis ta ce an dauko shi ne a cikin jirgin sama na musamman bayan da kungiyar tattalin arziki ta yammacin Afirka ( Ecowas) ta tsoma baki.

Juyin mulkin bayan nan da aka yi wanda ya hambarar da gwamantin Umar Sisoko shi ne na tara da aka yi a cikin shekaru biyar a wannan kasar.

Sojojin kasar sun sanar da ayyana  Horta N’Tam a matsyain shugaban gwamnatin soja an kuma rantsar da shi.

Kungiyar raya Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) ta yi Allah wadai da juyin mulkin da  na  kasar Guniea Bissau, kwanaki uku bayan zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisu, inda ta kira shi da “barazana kai tsaye ga zaman lafiyar kasar da yankin.”

Wannan “juyin mulkin soja” ya zama “mummunan keta tsarin mulki” kuma “barazana kai tsaye ne ga zaman lafiyar kasar da yankin baki daya,” in ji ECOWAS a cikin wata sanarwa da ta fitar.

Dama kafin hakan Shugabannin tawagar masu sa ido kan zaben na Guinea Bissau na kungiyar Tarayyar Afirka da ECOWAS, sun bayyana ” matukar damuwa game da sanarwar da sojoji suka yi na yin juyin mulki a kasar.” 

Majalisar Dinkin Duniya ta ce tana bin diddigin lamarin da “matukar damuwa,” tana kira da a girmama bin doka.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Limamin Tehran: Hadin Kai Ne Sakamakon Imani Da Ayyukan Kwarai Ne November 28, 2025 Yamen Ta Soki Kasashen Birtaniya Da Amurka Da Tsoma Baki Kan harkokin Kasarta November 28, 2025 Isra’ila Ta Kashe Mutane 10 A Wani Hari Da Ta Kai A Birinin Damaskas Na Kasar Siriya November 28, 2025 Jagoran : Amurka Tasha Kashi A Yakin Kwanaki 12 Duk Da Manyan Makamai Na Zaman Da Take Da Su. November 28, 2025 Ministocin Tarayyar Turai Sun yi Tir Da Karuwar Hare –Haren Da Yahudawa Ke Kai wa Falasdinawa November 28, 2025 An Rantsar Da Sabon Shugaban Mulkin Soja Na kasar Guinea-Bissau November 28, 2025 Isra’ila Na Barazanar Sake Shiga Wani Sabon Yaki Da Kasar Lebanon November 28, 2025 Petro: Man fetur shine burin Amurka a Venezuela ba yaki da fataucin kwayoyi ba November 28, 2025 Tarayyar Afirka ta yi Allah wadai da juyin mulkin a Guinea-Bissau November 28, 2025 Najeriya : Ana ci gaba da alhinin rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi November 27, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

China Ta Gargadi Amurka Akan Batun Yakar Kasar Venezuela

Mai Magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar China ta bayyana cewa: Beijing ba ta lamunta da duk wani kokarin tsoma bakin kasashen waje a harkokin cikin gidan wannan kasar.”

Mao Ning wacce ta gabatar da taron manema labaru a brinin Beijing a kasar China ta yi kira ga kasar Amurka da ta fasa Shirin kai wa kasar Venezuela hari wanda ba ya kan doka,mai makon haka ta karfafa sulhu da zaman lafiya a cikin yankin Latin.

Kamfanin dillancin labarun Xin Hua na kasar China ya nakalto mai Mao Ning tana cewa; Kasar China ba ta kuma lamunta da kakaba wa kasar ta Venezuela takunkumi ta gefe daya wanda baya kan doka ba, kuma take dokokin kasa da kasa ne, saboda ba a yi shi a karkashin amincewar kwamitin tsaro na MDD ba.

Mao Ning ta kuma ce; Beijing tana son ganin dukkanin bangarori su girmama hurumin kasar Venezuela, su kuma kaucewa haddasa hargitsi.

A ranar 24 ga watan Nuwamba  ta sanar da haramta wata kungiya wacce take mai fataucin muggan kwayoyi ce, kuma shugabanninta  su ne shugaban kasar Venezuela Nicholas Maduro da kuma wasu jami’an gwamnatinsa.

Kasar Venezuela ta karyata abinda Amurkan ta riya, tare da bayyana shi a matsayin ‘karya bai sa dariya” sannan kuma tana son fakewa da haka ne domin tsama baki a harkokin cikin gidan kasar.

A cikin watannin bayan nan dai Amurkan tana kai hare-hare akan kananan jiragen ruwa a tekun Carrebea bisa riya cewa suna dauke da kwayoyi daga Venezuela zuwa Amurka.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Palasdinu: Kwamandoji Biyu Na Rundunar “Sarayal-Quds” Sun Yi Shahada A Yammacin Kogin Jordan November 28, 2025 Kungiyar ‘Yan’uwa Musulmi Ta Soki Shirin Donald Trump Na Bayyanata A Matsayin Kungiyar ‘Yan Ta’adda November 28, 2025 Kasashen Qatar Da Jordan Sun Yi Allawadai Da Harin “Isra’ila” A Kasar Syria November 28, 2025 Senegal: Hambararren Shugaban Kasar Guinea Bissau Ya Isa Kasar Senegal November 28, 2025 Limamin Tehran: Hadin Kai Ne Sakamakon Imani Da Ayyukan Kwarai Ne November 28, 2025 Yamen Ta Soki Kasashen Birtaniya Da Amurka Da Tsoma Baki Kan harkokin Kasarta November 28, 2025 Isra’ila Ta Kashe Mutane 10 A Wani Hari Da Ta Kai A Birinin Damaskas Na Kasar Siriya November 28, 2025 Jagoran : Amurka Tasha Kashi A Yakin Kwanaki 12 Duk Da Manyan Makamai Na Zaman Da Take Da Su. November 28, 2025 Ministocin Tarayyar Turai Sun yi Tir Da Karuwar Hare –Haren Da Yahudawa Ke Kai wa Falasdinawa November 28, 2025 An Rantsar Da Sabon Shugaban Mulkin Soja Na kasar Guinea-Bissau November 28, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • China Ta Gargadi Amurka Akan Batun Yakar Kasar Venezuela
  • Kasashen Qatar Da Jordan Sun Yi Allawadai Da Harin “Isra’ila” A Kasar Syria
  • An Rantsar Da Sabon Shugaban Mulkin Soja Na kasar Guinea-Bissau
  • Hamɓararren Shugaban Guinea-Bissau ya gudu Senegal
  • ECOWAS ta yi Allah wadai da juyin mulki a Guinea Bissau
  • An Rutsa Da Tsohon shugaban Kasar Najeriya A Guine Bissau Bayan Juyin Mulki
  • Sojojin Sun Sanar Da Kwace Mulki A Kasar  Guinea Bissau
  • Shugaban Majalisar Koli Ta Taron Kasa Iran Ya Yabawa Pakistan Saboda Goyon Bayanta
  • Shugaban Majalisar Koli Ta Taron Kasa Iran Ya Yawaba Pakistan Saboda Goyon Bayanta