BUA ya raba wa asibitoci magunguna a Sakkwato
Published: 11th, February 2025 GMT
Kamfanin Siminti na BUA ya raba magungunan cututtuka daban-daban na kimanin naira miliyan 35 a ƙananan asibitoci da ɗakin shan magani 16 da ke cikin Ƙaramar Hukumar Wamakko a Sakkwato.
Daraktan Kamfanin BUA, Injiniya Yusuf Halliru Binji, a wurin rabon tallafin maganin ya ce BUA ya ba da tallafi ga asibitoci da ɗakunan shan magani 16 a tsarin da yake da shi na sadaukarwa ga al’ummar da suke kusa da shi, a kowace shekara akan bayar da magani don saukaka samun magani ga jama’ar.
Binji ta hannun Alhaji Sada Suleiman da ya wakilce shi ya ce kamfanin BUA a tsarinsa na rama alheri ya ɗauki wannan da muhimmanci domin ƙarfafa dangantaka.
“Babu tantama dole mu bayyana farin ciki ga irin goyon baya da haɗin kai da muke samu ga jama’a tsawon lokaci.
“Nasarar da kamfanin yake samu tana da alaƙa da haɗin kan jama’ar da ake makwabtaka da su. Saboda haka za mu ci gaba da kula da bunƙasa rayuwar jama’a
“Nan gaba kaɗan za mu ƙaddamar da rijiyoyin burtsatse guda 7 masu amfani da hasken rana a faɗin Sakkwato, bayan raba tufafin makarantar firamari biyar da za a yi ga mutanen yankin.
Daraktan ya gargaɗi waɗanda suka samu tallafin a kan kar su sayar da magungunan domin kyauta ne ga kowa.
Ya ce kamfanin zai haɗa kai da gwamnati don tabbatar da waɗanda aka yi don su sun amfana.
Wasu daga cikin asibitocin da aka yi rabon magungunan sun haɗa da Asibitin garin Bakin Kudu da Gidan Bailu da Kalambaina da Sabon Garin Alu da Gidan Boka da Asare da Arkilla da Guiwa da sauransu.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Jihar Sakkwato
এছাড়াও পড়ুন:
Remi Tinubu ta ba da tallafin Naira biliyan ɗaya ga waɗanda harin Benuwe ya shafa
Uwargidan Shugaban Nijeriya, Sanata Remi Tinubu ta bayar da tallafin naira biliyan daya ga wadanda harin nan ya rutsa da su a yankin Yelwata na Ƙaramar Hukumar Guma a Jihar Benuwe.
Sanata Tinubu wadda ta miƙa cakin kuɗin ga Gwamna Hyacinth Alia ta sanar da bayar da tallafin ne a jawabinta na jaje wanda ta kai Fadar Gwamnatin Benuwe da ke Makurdi.
Gwamnatin Zamfara ta amince da naɗin sabon Sarkin Katsinan Gusau Ambaliya ta yi ajalin mutum 30 a ChinaUwargidan shugaban ƙasar ta buƙaci a yi amfani da wannan tallafin a matsayin gudunmawar farfaɗo da yankin da waɗanda suka tsallake rijiya da baya a yayin harin musamman yaran da yanzu ke buƙatar komawa makarantu.
Ana iya tuna cewa, tun a daren ranar 13 ga watan Yuni zuwa wayewar gari 14 ga watan ne aka kashe fiye da mutum 100 a ƙauyen Yelwata, lamarin da ya janyo Allah wadai daga sassa daban-daban a faɗin ƙasar.
Jihar Benuwe dai na daga cikin jihohin da ke fuskantar matsalar tsaro a Nijeriya, musamman rikicin manoma da makiyaya da kuma na ƙabilanci, wanda ke sanadiyyar salwantar rayuka da dama.