Gwamnatin Kano za ta kafa hukumar kula da masu buƙata ta musamman
Published: 11th, February 2025 GMT
Gwamnatin Kano ta bayyana aniyarta na kafa Hukumar Kula da Masu Buƙata ta Musamman a wani mataki na tabbatar da adalci a tsakanin al’ummar jihar.
Kwamishiniyar Mata da Yara masu bukata ta musamman, wacce Daraktar Jin Daɗi ta ma’aikatar, Binta Muhammad Yakasai, ta wakilta, ta bayyana hakan yayin wani taron tattaunawa na yini guda da masu ruwa da tsaki kan kafa Hukumar Kula da Mutanen da ke da Bukatu na Musamman (PWDs) a Jihar Kano.
Tana jaddada aniyar gwamnati na ƙarfafa PWDs, Yakasai ta ce, “Wannan taro ba kawai haɗuwar ra’ayoyi ba ne, amma wani mataki ne na tabbatar da adalci, haɗawa da ƙarfafa wani muhimmin ɓangare na al’ummarmu.”
Ta bayyana manyan dalilai guda biyar da ke nuna bukatar kafa hukumar PWDs a Kano, waɗanda suka haɗa da kare Haƙƙoƙin PWDs – hukumar za ta kasance mai sa ido don tabbatar da an kiyaye haƙƙoƙinsu da kuma magance wariya.
Sauran sun hada da kirkira da aiwatar da tsare-tsare, inganta samun sauƙin shige da fice, karfafawa da gina kwarewa da haɗin gwiwa da masu ruwa da tsaki.
Yayin da tattaunawa ke ci gaba, masu ruwa da tsaki sun buƙaci a daina tsaya kan dokoki da manufofi kawai, a mayar da hankali kan tasirin su ga rayuwar jama’a.
“Wannan ba kyauta ba ce, buƙata ce. Kafa wannan hukuma al’amari ne na adalci, mutunci, da daidaiton haƙƙi. Mu haɗa kai don ganin ta tabbata,” in ji Yakasai.
Wannan taro, wanda Giving Promise, ƙwararre a shugabanci da haɗin gwiwar matasa a VSO Nigeria, ya shirya, ya bayar da damar tattaunawa kan gaggawar buƙatar samar da hukuma da za ta kula da matsalolin da PWDs ke fuskanta.
Promise ya jaddada muhimmancin hukumar wajen tabbatar da tsare-tsare da suka dace da PWDs a Kano.
“Gwamnati dole ta haɗa kowa a ci gaban jiharmu. Barin PWDs a baya yana hana cigaba. Manufofin SDGs (Sustainable Development Goals) sun jaddada buƙatar kada a bar kowa a baya, kuma kafa wannan hukuma wani mataki ne na tabbatar da cewa PWDs ba wai kawai an haɗa su ba, har ma suna da tasiri a cikin manufofin da suka shafe su,” in ji shi.
Ya bayyana manyan matsalolin PWDs guda biyu da suka haɗa da ƙarancin damar shiga da buƙatar tsarin haɗin gwiwa na musamman.
Ya ce kowane rukuni na PWDs yana da bukatunsa na musamman, kuma ba tare da hukuma ba, za su ci gaba da fuskantar ƙalubale.
“Idan har Kano na son ci gaba, dole a bai wa kowane ɗan ƙasa dama don bayar da gudunmawa. Kafa wannan hukuma ba kawai buƙata ba ce, wajibi ne,” in ji shi.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Hukumar Kula da Masu Buƙata ta Musamman Jihar Kano kafa hukumar tabbatar da
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Jihar Kano Ta Kaddamar da Manufar Sauyin Yanayi
Gwamnatin jihar Kano tare da hadin gwiwar wata kungiya mai suna Partnership for Agile Governance and Climate Change (PACE) ta kaddamar da manufofinta na sauyin yanayi a hukumance. Wannan manufa mai mahimmanci ta samar da taswirar dabaru don ragewa, daidaitawa, da tsarin tafiyar da yanayi mai hadewa a duk sassan ci gaba a jihar.
Da yake jawabi a wajen taron kaddamar da taron wanda aka gudanar a dakin taro na Armani Event Centre dake Kano, Gwamna Abba Yusuf wanda sakataren gwamnatin jihar Ibrahim Farouk ya wakilta, ya bayyana taron a matsayin wani babban ci gaba a kokarin gwamnatinsa na mayar da jihar Kano a matsayin mai ci gaba a harkokin tafiyar da yanayi da muhalli.
Gwamna Yusuf ya jadadda cewa, manufar tana cike da shirin aiwatar da sauyin yanayi, wanda ke fassara kudirin siyasar gwamnati zuwa tsarin aiwatarwa a aikace.
Ya kuma yi tsokaci kan shirye-shiryen da gwamnati ke yi na samar da makamashi ta hasken rana da ababen more rayuwa.
Gwamnan ya nanata shirin gwamnatin sa na dasa itatuwa miliyan 5 a shekarar 2025 domin rage zaizaiyar kasa, da inganta iskan shaka, da inganta kyawawan birane.
ABDULLAHI JALALUDDEEN KANO