Masarautar Fika ta buɗe gasar ƙwallon ƙafa karo na uku a Potiskum
Published: 3rd, February 2025 GMT
Masarautar Fika da ke Jihar Yobe ta buɗe gasar ƙwallon ƙafa karo na uku a filin wasa na Dabo Aliyu da ke garin Potiskum.
An buɗe gasar ƙarƙashin jagorancin mai Martaba Sarkin Fika, Alhaji Dr. Muhammad Ibn Abali Muhammad Idris wanda kuma shi ne Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Yobe.
Ya je Maiduguri daga Legas a kan keke Rikicin rusau ya yi ajalin mutum 4 a KanoGasar wacce aka fara a shekarar 2011 ta bunƙasa zuwa wani gagarumin taron wasanni a yankin, wadda ke haɗa ƙungiyoyi daga ƙananan hukumomi huɗu na yankin da suka haɗa da Fune, Potiskum, Fika, da Nangere.
A shekarar 2017 aka gudanar da gasar karo na biyu, lamarin da ya ƙara tabbatar da gasar a matsayin ɗaya daga cikin manyan wasannin ƙwallon kafa a jihar.
A wannan shekarar ta 2025 an buɗe gasar ce da wasa tsakanin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Total Pillars FC Potiskum da Parma FC ita ma a garin na Potiskum.
Ƙungiyoyin biyu dai sun ƙare zagayen farko ba tare da an zura ƙwallo a raga ba, amma ana minti 19 bayan dawowa daga hutun rabin lokaci Abdulzabi na Parma ya zura ƙwallo daya tilo da aka tashi a wasan, inda ƙungiyar tasa ta samu nasara da ci 1-0.
Gasar ta bana ta samu halartar ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa 64 daga ƙananan hukumomi huɗu da suka shiga gasar.
Wani muhimmin abin da ya fi ɗaukar hankali a bikin buɗe gasar shi ne bayar da lambobin yabo ga fitattun mutane domin nuna irin gudunmawar da suke bayarwa wajen wasanni da ci gaban al’ummar wannan masarauta ta Fika.
Waɗanda aka karrama sun haɗa da Alhaji Garba Mohammed, FIFA Lamido, Aliyu Abba Bulama (AFCON), Sadik Rabiu Alkali da Alhaji Ba’aba Abba (Aljino na Fika).
Ana sa ran za a ci gaba da gudanar da gasar nan da makonni masu zuwa, inda za a haɗa haziƙan ’yan ƙwallon ƙafa da masu sha’awar ƙwallon ƙafa daga sassan yankin na Masarautar ta Fika.
Mai Martaba Sarkin Fika, Alhaji Muhammad Ibn Abali Muhammad Idris ya yi fatan alheri ga waɗanda suka samu damar shiga wannan gasa tare da yi musu addu’ar kammala gasar lafiya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Jihar Yobe Masarautar Fika ƙwallon ƙafa buɗe gasar
এছাড়াও পড়ুন:
Tinubu ya bar Abuja zuwa Japan da Brazil
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya bar Abuja domin ziyarar aiki zuwa ƙasashen Japan da Brazil.
Ya tashi daga Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe da misalin ƙarfe 11:15 na safiyar Juma’a, inda zai tsaya a Birnin Dubai na Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.
Matsalar ƙofa ta hana fasinjoji 58 hawa jirgin Abuja zuwa Landan Matsalar tsaro na iya hana mu ci gaba da rijistar masu zabe a Borno – INECManyan jami’an gwamnati da suka raka shi, sun haɗa da Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkar Tsaro, Nuhu Ribadu.
Sauran sun haɗa da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila; da Ministan Kuɗi, Wale Edun.
A Japan, Shugaba Tinubu zai halarci Taron Ci Gaban Afirka karo na tara (TICAD9) wanda zai gudana a birnin Yokohama daga ranar 20 zuwa 22 ga watan Agusta.
Taken taron shi ne “Haɗa Hannu Wajen Samar da Ingantacciyar Mafita ga Afirka”.
Taron zai mayar da hankali kan inganta tattalin arziƙin Afirka, kyautata yanayin kasuwanci, da samar da zaman lafiya, tsaro, da ci gaba mai ɗorewa ta hanyar jari-hujja da ƙirƙire-ƙirƙire daga kamfanoni masu zaman kansu.
Bayan taron Japan, Tinubu zai nufi ƙasar Brazil, domin ziyarar aiki ta kwana biyu daga ranar 24 zuwa 25 ga watan Agusta.
Tinubu zai je ƙasar ne bayan gayyatar da Shugaban Brazil, Luiz Inacio Lula da Silva ya yi masa.
A Brazil, zai gana da shugaban ƙasar, sannan zai halarci taron kasuwanci, kuma ya tattauna hanyoyin bunƙasa dangantaka tsakanin ƙasashen biyu.
Tawagarsa za ta kuma yi aiki wajen ƙulla yarjejeniyoyi da haɗin gwiwa da gwamnatin Brazil.