An kama mutum 8 kan faɗan daba a Kano
Published: 12th, April 2025 GMT
’Yan sanda sun cafke wasu mutum takwas da ake zargi da faɗan daba a yankin Ƙofar Na’isa zuwa Ƙofar Ɗan Agundi da ke ƙwaryar birnin Kano.
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan cikin wani saƙon bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Ziyarar da Atiku ya kai wa Buhari ba ta dami APC ba — Ganduje Yadda bom ya tashi da ɗan gwangwan a LegasKiyawa ya ce a ranar Alhamis da ta gabata ce suka samu kiraye-kirayen waya cewa wasu sun fito da makamai suna faɗan daba, lamarin da ya sanya aka tura jami’ai domin ɗaukar mataki.
Kakakin ’yan sandan ya ce a wannan lokaci babu wanda aka kama sakamakon arcewa da masu faɗan daban suka yi.
“Wasu sun fito faɗan daba, sun ji wa kansu raunuka a Ƙofar Na’isa, amma ba wanda ya zo wajen ’yan sanda a kai shi asibiti,” a cewar Kiyawa.
Sai dai Kiyawa ya ƙara da cewa jami’ansu sun sake komawa unguwar da daddare, inda suka cafke mutum takwas da raunuka a jikinsu da wuƙaƙe.
Kazalika, ya ce sun tattara sunayen mutane daban-daban da ake zarginsu da faɗace-faɗacen daba kuma nan ba da jimawa ba za su shiga hannu.
Aminiya ta rawaito yadda ake zaman ɗar-ɗar a yankin Ƙofar Na’isa da kuma Ƙofar Ɗan Agundi tun bayan dawowar faɗan daban a yayin bukukuwan sallah ƙarama da aka yi kwanan nan.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Faɗan Daba Jihar Kano Ƙofar Ɗan Agundi Ƙofar Na isa faɗan daba
এছাড়াও পড়ুন:
’Yan bindiga sun harbe ɗan sanda har lahira a Edo
An harbe wani jami’in ɗan sanda har lahira, yayin da yake tsaka da binciken ababen hawa a Benin a Jihar Edo.
Kakakin rundunar, CSP Moses Yamu, ya ce lamarin ya faru da misalin ƙarfe 12 na ranar Juma’a, lokacin da jami’an rundunar suka tsayar da wata baƙar mota ƙirar Lexus, amma ta ƙi tsayawa.
’Yan sanda sun ceto yara 2 da aka yi garkuwa da su a Borno Ƙasashen waje na taimaka wa ’yan ta’adda a Najeriya —Sheikh GumiƊaya daga cikin mutanen da ke cikin motar ya buɗe wa jami’an da ke shingen wuta, sannan suka tsere.
A dalilin haka ne suka harbe wani ɗan sanda wanda ba a bayyana sunansa ba har lahira.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, Monday Agbonika, ya umarci a farauto waɗanda suka aikata laifin.
Ya roƙi jama’a su bayar da sahihan bayanai, musamman idan suka ga irin wannan motar da aka zayyana.
Rundunar ta tabbatar wa jama’a cewa an ƙara tsaurara tsaro a faɗin jihar.