Isra’ila Na Barazanar Sake Shiga Wani Sabon Yaki Da Kasar Lebanon
Published: 28th, November 2025 GMT
Ministan yakin Isra’ila ya yi barazanar kai wa kasar Lebanon hari gadan-gadan, inda ya bukaci kungiyar Hizbullah ta kwace damarar makamai.
Ministan yakin Isra’ila, Isra’ila Katz, ya yi gargadin cewa Tel Aviv a shirye take ta kaddamar da wani sabon yaki kan kasar Labanon matukar kungiyar gwagwarmayar Hizbullah ta ki mika makamanta zuwa karshen shekarar 2025.
Da yake jawabi ga Knesset na Isra’ila, Katz ya yi ikirarin cewa Washington ta ba Beirut wa’adin kwance damarar Hezbollah zuwa karshen shekara, amma ya ce ba ya tsammanin kungiyar za ta mika makamanta.
“Ban yi imani cewa Hizbullah za ta mika makamanta bisa radin kanta ba,” kamar yadda ya shaida wa ‘yan majalisar. “Idan Hezbollah ba ta yi watsi da makamanta a karshen shekara ba, za mu sake yin aiki da karfi a Lebanon, za mu kwance damarar su.”in ji shi.
Katz ya kara da cewa gwamnatin Isra’ila ba za ta lamunci abin da ya kira barazana ga matsugunan da ke kan iyakar Lebanon ba.
“Ba za mu yarda da duk wata barazana ga mazauna arewa ba, kuma za a ci gaba da aiwatar da doka har ma da kara yin amfani da karfi.”
A halin da ake ciki dai Washington na matsawa kasar Lebanon lamba kan ta tilastawa kungiyar Hizbullah ta kwace damarar makamai, ko da kuwa hakan yana tattare da hadarin fadawar kasar a cikin yakin basasa, kuma ta fito fili ta goyi bayan barazanar da Isra’ila ke yi, tana mai gargadin cewa Lebanon na fuskantar wani babban hari idan har Hizbullah ba ta mika makamanta ba.
A yayin da yake mayar da martani game da batun da ake yi, dan majalisar dokokin Lebanon Hassan Fadlallah ya jaddada cewa, babu inda za a yi wata tattaunawa ta siyasa da Isra’ila yayin da take ci gaba da karya yarjejeniyar tsagaita bude wuta.
Fadlallah ya ce, har yanzu ba a gabatar da wata shawara ta siyasa ga kasar Labanon da za ta iya dakatar da kai hare-haren ‘yan mamaya yadda ya kamata ba, yana mai yin Allah wadai da tsoma bakin kasashen yammacin duniya da kuma Amurka suke yi a cikin harkokin cikin gidan kasar ta Lebanon.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Petro: Man fetur shine burin Amurka a Venezuela ba yaki da fataucin kwayoyi ba November 28, 2025 Tarayyar Afirka ta yi Allah wadai da juyin mulkin a Guinea-Bissau November 28, 2025 Najeriya : Ana ci gaba da alhinin rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi November 27, 2025 Iran ta yi tir da Australiya kan alakanta IRGC, da mai tallafawa ta’addanci November 27, 2025 Ramaphosa ya soki Trump kan hana shi halartar taron G20 na badi November 27, 2025 ECOWAS ta yi Allah wadai da juyin mulki a Guinea Bissau November 27, 2025 Faransa, Jamus, Italiya, da Burtaniya sun yi tir da “karuwar rikici” a yammacin kogon jodan November 27, 2025 Rasha A Shirye Take Ta Taimaka Wa Najeriya A Fada Da Ta’addanci November 27, 2025 Palasdinawa Sun Karbi Gawawwakin Shahidai 15 Daga ‘Yan Mamaya November 27, 2025 Makaman Iran Masu Linzami Ne Kandagarkon Dake Takawa Makiya Birki November 27, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Uganda: An Kama Fiye Da ‘Yan Hamayyar Siyasa 300 A Lokacin Yakin Neman Zabe
Majiyar ‘yan hamayyar siyasar kasar Uganda sun sanar da cewa, jami’an tsaron kasar sun kama magoya bayan Bobi Wine dake takarar shugabancin kasar 300 a tsawon yakin neman zabe.
Mai magana da yawun Bobi Wine dan takarar shugabancin kasar ya fada a jiya Talata cewa; jami’an tsaron kasar sun kama fiye da mutane 300 da suke goyon bayansa tun da aka fara yakin neman zabe daga watan Janairu zuwa yanzu.
Bob Wine wanda shahararren mawaki ne ya juye zuwa dan siyasa, yana yin takara a karo na biyu da shugaban kasar mai ci, Uweri Musaveni. A zaben 2021 Bob Wine wanda sunansa na yanke shi ne Robert Kyagulanyi,, ya zo na biyu.
Kakakin jam’iyyarsa ta NUP,ya ce, a cikin wannan makon ma an kama mutane da dama, kuma ana tsare da su ne a cikin babban birnin kasar Kamfala.
Majiyar jam’iyyar hamayyar ta kuma ce, a ranar Litinin da aka bude yakin neman zabe kadai na kame mutane sun kai 100, sai kuma wani adadi mai yawa a jiya Talata.
Jami’an tsaron kasar sun sanar da kame mutane 7 bayan da su ka yi jefe-jefe da duwatsu a lokacin yakin neman zabe.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label Name* Email* Website Label Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Reuters: Kungiyar Likitoci Ba Da Iyaka Ba Ta Fice Daga Asibitin Darfur Bayan Bude Wa Ma’aikatanta Wuta November 26, 2025 Shugaban Iran: Kasuwar jarin cikin gida sirrin nasarorin gwamnati na tattalin arziki November 26, 2025 Larijani: Hadin gwiwar Iran da Pakistan na taimaka wa zaman lafiya a yankin November 26, 2025 Al-Houthi ya yi ta’aziyyar shahadar babban kwamanda na Hizbullah November 26, 2025 UNIFIL: Isra’ila tana sabawa wa kudurorin MDD a cikin Lebanon November 26, 2025 Matsalolin Tsaro A Yankunan Bakin Ruwa A Kasar Siriya Ya Kai Ga Zanga-Zangar Lumana November 26, 2025 Aljeriya Ta Bukaci Kasashen Duniya Su Dauki Mataki Don Kawo Karshen Ta’asan HKI A Yankin Asiya Ta Kudu November 26, 2025 Shugaban Majalisar Koli Ta Taron Kasa Iran Ya Yabawa Pakistan Saboda Goyon Bayanta November 26, 2025 EU da AU na taro kan diyya ga laifukan mulkin mallaka da cinikin bayi November 25, 2025 Hizbullah: Isra’ila na kure idan ta na tunanin kashe-kashe zai kawo karshen kungiyarmu November 25, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci