Aminu Bayero ya naɗa Sanusi a matsayin Galadiman Kano
Published: 28th, April 2025 GMT
Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya naɗa babban ɗan uwansa, Alhaji Sanusi Ado Bayero, a matsayin Galadiman Kano, bayan rasuwar Abbas Sanusi.
A gefe guda kuma, Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, wanda ke ta ƙaddamar kan sarautar Kano da Aminu Ado Bayero a gaba kotu, ya naɗa Mannir Sanusi a matsayin Galadiman Kano.
Wannan lamari na nuni da cewa rikicin Sarautar Kano ya ɗauki sabon salo, inda kowanne daga cikin ɓangarori biyun ya naɗa nasa Galadiman Kano, inda masu riƙe da sarautun biyu za su gudanar da ayyukansu daban-daban.
A cikin wasiƙar da ke ɗauke da wannan sanarwar, wadda Alhaji Awaisu Abbas Sanusi, babban jami’in gudanarwa na Majalisar Masarautar Kano ya sanya hannu, naɗin Sanusi Ado Bayero ya biyo bayan taron majalisar da Sarki Aminu ya jagoranta a ranar Laraba, 16 ga Afrilu, 2025.
Yadda matsalar ƙwacen waya da faɗan daba ke addabar Kano Dalilin faɗuwar farashin kayan abinci a kasuwannin Arewa NAJERIYA A YAU: “Dalilin da muke sauya sheƙa zuwa jam’iyya mai mulki”A baya an naɗa Sanusi a matsayin Chiroman Kano, dan Majalisar Masarautar Kano, kuma Hakimin Gwale a zamanin mahaifinsa Sarki Ado Bayero.
Bayan rasuwar mahaifin nasa a shekarar 2014, a matsayinsa na babban ɗa kuma magaji, an ɗauka cewa Sanusi Ado ne wanda ya cancanci ya gaje shi, War wasu rahotanni na farko sun sanar da shi a matsayin Sarki.
Sai dai, a ranar 8 ga Yuni, 2014, aka naɗa ɗan ɗan uwansa, Sanusi Lamido Sanusi, a matsayin Sarkin Kano. A sakamakon haka, Sanusi Ado ya ƙi yin mubaya’a a gare shi kuma, don nuna rashin amincewa, kuma ya yanke shawarar barin Kano.
Bayan raba Masarautar Kano, da cire Sarki Sanusi II, da kuma naɗin ƙanensa, Aminu Ado Bayero, a matsayin Sarki na 15 a watan Yulin 2020, an mayar da Sanusi Ado Bayero kan matsyinsa a Majalisar Masarautar Kano kuma aka ba shi sarautar Wamban Kano.
Tarihin Sanusi Ado BayeroSanusi kammala digirinsana farko a fannin shari’a a shekarar 1983 kuma an rantsar da shi a matsayin lafiya a shekarar 1984.
Tsohon ma’aikacin Gwamnatin Jihar Kano ne inda ya yi aiki daga 1985 zuwa 2015, har ya kai matsayi mafi girma na Babban Sakataren.
Daga baya aka naɗa shi a matsayin Manajan Daraktan Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa ta Najeriya, muƙamin da ya riƙe har zuwa lokacin da aka cire shi a watan Agustan 2015.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Sanusi Ado Bayero Sanusi Bayero Sarkin Kano Sanusi Ado Bayero Masarautar Kano
এছাড়াও পড়ুন:
Karamar Hukumar Birnin Kano Ta Kaddamar Da Kula Da Lafiyar Ido Kyauta
Shugaban Ƙaramar Hukumar Birnin Kano, Alhaji Salim Hashim Idris Gwangwazo, ya kaddamar da shirin kula da ido kyauta domin tallafawa jama’a da ke fama da ‘Glaucoma’ da ke lalata rijiyoyin ido, da ‘Cataract’ wato yanar ido da sauran cututtukan ido.
An gudanar da shirin ne a Asibitin Kwalli tare da haɗin gwiwar gwamnatin jihar, ƙarƙashin Gwamna Abba Kabir Yusuf, da Hukumar Lafiyar Farko ta Jiha, da ƙaramar hukumar da masu bada tallafi daga kasashen waje.
Shirin ya haɗa da gwaje-gwajen lafiyar ido, da bayar da magunguna da kuma rarraba tabarau kyauta, musamman ga marasa ƙarfi a cikin al’umma.
Shugaban ƙaramar hukumar, ta bakin Kwamishinan Lafiya Alhaji Mustapha Darma, ya bukaci jama’a da su ci gaba da tallafawa gwamnati wajen samar da ingantaccen kulawa.
A baya-bayan nan, gwamnatin jihar ta dauki nauyin kula da lafiyar ido ga mutum sama da 500 daga Birnin Kano da sauran kananan hukumomi.
Shugaban kula da lafiya am matakin farko na ƙaramar hukumar, Alhaji Lawan Jafar, ya ce wadanda lalurar su ba ta tsananta ba za a ba su shawarwarin kula da lafiyar su, da magunguna, wa su ma har da tabarau, yayin da wadanda ta su ta tsananta kuma za a musu tiyata.
Wasu daga cikin wadanda suka amfana sun nuna godiya tare da yi wa gwamnati addu’a don samun nasara.
Shugaban tawagar likitocin, Dr. Kamal Saleh, ya tabbatar da cewa shirin ya samu nasara sosai.
Daga Khadijah Aliyu