Za A Samu Mamakon Ruwan Sama Da Hazo Daga Litinin Zuwa Laraba A Nijeriya
Published: 2nd, June 2025 GMT
Ranar Laraba, ruwan sama da hazo za su afkawa jihohin Zamfara, Adamawa, Kaduna, Sokoto, Kebbi da Taraba. Daga baya kuma, za a samu ruwan sama a jihohin Katsina, Bauchi da Sakkwato. Arewa ta rsakiya za ta fuskanci ruwan sama a Abuja, Nasarawa, Neja da Binuwe da safe, yayin da yamma za ta shafi Nasarawa, Filato, Kwara da Kogi.
A Kudu, ana hasashen ruwan sama da safe a Ogun, Ondo, Oyo, Edo, Enugu, Ebonyi, Cross River, Rivers da Akwa Ibom, sannan daga bisani a rana, za a sami ruwan sama a fadin yankin.
NiMet ta gargjama’a su ɗauki matakan kariya, musamman inda hadari zai faru, domin iska mai ƙarfi na iya gabatar da haɗari. An shawarci mutane su guji tuƙi a lokacin ruwan sama mai ƙarfi, su cire na’urori daga soket, su guji tsayuwa kusa da manyan itatuwa, sannan masu jirgin sama su nemi rahoton yanayi daga NiMet kafin tafiya. Ana kuma shawarci jama’a su dinga bin sahihan bayanan yanayi daga shafin NiMet:
www.nimet.gov.ng.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Ruwa
এছাড়াও পড়ুন:
Xi Jinping Ya Halarci Kwarya-Kwaryan Taron Shugabannin APEC Na 32 Tare Da Gabatar Da Jawabi
Shugaba Xi ya kuma bayyana cewa, cikakken zama na 4 na kwamiti na 20 na JKS ya amince da shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 15. Sin za ta yi amfani da wannan damar don ci gaba da gyare-gyaren tattalin arzikinta, da kuma fadada bude kasuwancinta mai zurfi ga ketare, ta haka za ta ci gaba da ba da sabbin damammaki ga yankin Asiya da Pasifik da sauran kasashen duniya ta hanyar zamanantar da al’ummarta. (Amina Xu)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA