2025-06-22@20:52:13 GMT
إجمالي نتائج البحث: 955
«Kayan Mata»:
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi wanda yake ziyar aiki a kasar Lebanon bayyana cewa kasarsa tana goyon bayan hadin kan mutanen kasar Lebanon. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadar haka bayan ganawarsa da shugaban majalisar dokokin kasar ta Lebanon a yau Talata a birnin Beirut babban birnin...
Iftila’in ambaliyar ruwa a garin Mokwa a Ƙaramar Hukumar Mokwa ta Jihar Neja ta yi ajalin mutane sama da 200, yayin da wasu sama da 500 suka bata. Ambaliyar, wadda ita ce mafi muni a yankin cikin shekaru 60, ta shafi yankunan Tiffin Maza da Anguwan Hausawa, bayan ruwan sama kamar da bakin ƙwarya...
Sojojin mamayar Isra’ilan sun sake aiwatar da wani sabon kisan kiyashi a birnin Rafah, inda suka kashe mutane da dama a kusa da cibiyar rarraba kayan agaji Fararen hula 23 ne suka yi shahada yayin da wasu kusan 200 suka jikkata a yau Talata lokacin da sojojin mamayar Isra’ila suka bude wuta kan mai uwa...
Ya ce yanzu lokaci ne da Arewa za ta nuna adalci ta hanyar barin shugaba daga Kudu ya kammala wa’adin mulkinsa. Ya ƙara da cewa, “Idan za a fitar da wani ɗan takarar shugaban ƙasa daga ‘yan adawa a nan gaba, to ya dace ya fito daga Kudu maso Yamma. Wannan ne dai-daito da adalci.”...
Farashin kayan miya, musamman kayan gwari ya yi tashin gwauron zabo a yayin da Babbar Sallah ta bana ta kawo jiki. Kuɗin kayan lambu ya ninka sau uku a cikin mako biyu, a yayin da Babbar Sallar ta zo wa iyalai da dama a Najeriya a hagunce, a sakamakon fama da matsananciyar matsalar tsadar rayuwa....
Masu sayar da rago a jihar Zamfara sun nuna damuwarsu kan rashin samun ciniki gabanin bikin Eid-el-Kabir, duk da cewa ana samun dabbobi a kasuwanni. Shugaban kungiyar masu sayar da dabbobi ta jihar Zamfara, Malam Saidu Ibrahim Gusau ya bayyana haka a wata tattaunawa da gidan rediyon Najeriya a Gusau. Malam Gusau ya...
’Yan bindiga sun sako wani magidanci da suka yi garkuwa da shi da amaryarsa na tsawon wata bakwai, bayan sun bindige matar tasa tare da karɓar kuɗin fansa Naira miliyan 30 daga iyalansa. A watan Oktobar 2024 ne ’yan bindiga suka yi garkuwa da mutumin suna Yakubu Dada tare da amaryarsa, a yayin da ma’auratan...
’Yan bindiga sun sako wani magidanci da suka yi garkuwa da shi da amaryarsa na tsawon wata bakwai, bayan sun bindige matar tasa tare da karɓar kuɗin fansa Naira miliyan 30 daga iyalansa. A watan Oktobar 2024 ne ’yan bindiga suka yi garkuwa da mutumin suna Yakubu Dada tare da amaryarsa, a yayin da ma’auratan...
Jami’an Tsaron Saudiyya sun kori mutane sama da 205,000 da ke neman yin aikin Hajji ta barauniyar hanya daga birnin Makka a yayin da aikin Hajjin bana ya kawo jiki. Daraktan Tsaron Jama’a kuma Shugaban Kwamitin Tsaron Hajji, Laftanar-Janar Mohammed Al-Bassami, ya bayyana cewa hukumomin kasar sun hana mutane sama da 269,000 marasa...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta bayyana cewa: Rahoton IAEA na nuna son kai kuma an shirya shi ne a karkashin tasirin wasu kasashe Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Rahoton da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya ta fitar ya kunshi maimaici da wuce gona da iri, yana mai jaddada cewa,...
Wasu ’yan daba sun yi wa Mataimakin Firinsifal na wata makarantar sakandare dukan tsiya a wani mummunan harin da suka kai masa saboda ya hana wani ɗalibi satar jarabawa. A yayin da ake ci gaba da jarabawar kammala sakandare ta WASSCE da ake yi a halin yanzu ne, Mista Rotifa, mataimakin shugaban wata makaranta mai...
Ya buƙaci shugabannin haɗakar su fara tsarin kafa sabuwar jam’iyyar da za ta kasance mai suna ɗaya, falsafa ɗaya, da tsarin shugabancin da zai haɗa kan kowa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don...
Jami’ai a Falasdinu sun ce akalla mutum 31 ne sukayi shahada sannan wasu sama da 150 sun jikkata, bayan wani hari da Isra’ila ta kai kusa da wurin rabon abinci a birnin Rafah. Dama shugaban hukumar MDD da ke kula da yan gudun hijirar Falasdinawa, Philippe Lazzarini, ya ce rabon kayan agajin ya zama tarkon...
Ma’aikatar lafiyar kasar Sudan ta bayyana cewa: Ana ci gaba da daukan matakan ganin an shawo kan ci gaba da yaduwar masifar kwalara a kasar Gidan talabijin na Al-Alam ya watsa rahoton cewa: A halin da ake ciki a fannin kiwon lafiya a birnin Khartoum fadar mulkin kasar bayan bullar cutar kwalara yana ta kokarin...
Hon. Nasiru ya kara da cewa Gwamna Radda ya yi kokari wajen yaki da matsalolin tsaro wanda suka addabi Jihar Katsina, inda ya bayyana cewa ana samun sauki sosai a wannan bangare. Ya ce gwamnati ta gyara makarantu da asibitoci a fadin Jihar Katsina, inda aka maida su na zamani tare da daukar ma’aikatan lafiya...
A nasa jawabin, shugaban kwamitin shirya musabakar karatun alkurani na karamar hukumar Igabi, Malam Abubakar Sadik Muhammad (Abu Asim), ya ce duk irin nasarar da kwamitin ya samu, ya samu ne bisa goyon bayan da Honarabul Yusuf Ibrahim Zailani yake ba su. Ya ce shi ne kashin bayan samun nasarar da suka yi a fadin...
Bayan mintuna 90 na wasan ba tareda wani ya doke wani ba sai alkalin wasa ya bayar da damar bugun daga kai sai mai tsaron raga, Jamaica ta ci kwallaye 4 inda Nijeriya ta ci dukkan kwallaye 5 da yan wasan suka buga, hakan ya sa yaran na Eric Chelle suka lashe gasar Unity Cup...
“Gane amfanin lamarin da ya shafi ilimi shi yasa, Gwamna Lawal ya kaddamar da dokar ta baci a bangaren ilimi a watan Nuwamba 2023,matakin da aka dauka an yi sa’a ya haifar da da mai ido a bangaren ilimi a Jihar Zamfara. “Fiye da makarantu 500 aka y masu kwaskwarima da samar masu abubuwan da...
A karon farko, rundunar tsaron Indiya ta tabbatar da cewa ta rasa wasu jiragen yaƙi a yayin arangama mai tsanani da suka fafata da Pakistan a farkon watan Mayu. Wannan sanarwa ta fito ne daga bakin Babban Hafsan Tsaro na Indiya, Anil Chauhan, a taron Shangri-La Dialogue, babban taron tsaro na Asiya, a Singapore. Tun...

Cutar Kwalara Ta Yadu A Sudan Baya Ga Matsalar Tashe-Tashen Hankulan Da Suke Ci Gaba Da Yuduwa A Kasar
Cutar kwalara ta yadu a Sudan, kuma ‘yan tawayen dakarun kai daukin gaggawa sun kai hare-hare kan asibitoci biyu a Jihar El Obeid na kasar Sudan na ci gaba da fama da tabarbarewar yanayin tsaro da lafiya bisa la’akari da abubuwan da ke faruwa a baya-bayan nan. A bangaren tsaro kuma, Dakarun Kai Daukin Gaggawa...
A jawabinsa a wajen rabbata hannun yarjejeniyar, jami’in shirin na jihar ta Gwambe, Farfesa Usman Bello Abubakar, ya danganta wannan aiki a matsayin wani babban ci gaba a jihar. Ya kara da cewa, aikin ba kawai wurin yanka dabbobi ba ne, akwai kuma batun zuba hannun jari ga ci gaban kiwon su kansu dabbobin. A...
Jami’in kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya ya ce matakin da Isra’ila ta dauka na hana agajin abinci ga Falasdinawa da ke fama da yunwa a yankin Zirin Gaza da aka yi wa kawanya ya zama laifin yaki. “Muna ganin abinci dake jibge a kan iyakoki kuma ba a ba da izinin...
Ya ce a nemi bayani daga wurare daban-daban kamar Kungiyar Ma’aikatan Kananan Hukumomin Nijeriya (NULGE) da Ma’aikatar Kudi, ya kara da cewa sakataren gwamnatin tarayya shi ne shugaban kwamitin aiwatar da hukuncin. Abubuwan da mutane yawa suke gnin ya janyo jinkirta aiwatar da hukuncin shi ne, shigar da sabon sharadi daga Babban Bankin Nijeriya (CBN),...
Wani mutum mai suna Adamu Muhammed Tenimu ya suma bayan da samu labarin cewa matarsa ta haifi jarirai ’yan uku a asibitin koyarwa na Jami’ar Tarayya da ke Lokoja babban birnin Jihar Kogi ranar Juma’a. Shaidu sun ce, mutumin da ya ji cewa matarsa ta haifi ‘ya’ya mata uku, sai ya faɗi ya suma a harabar...
MDD ta yi gargadi akan yunuwar da mutanen Gaza suke fama da ita, sannan ta kara da cewa: Isra’ila ta hana shigar da kayan agaji, kuma rabin cibiyoyin kiwon lafiya na yankin sun daina aiki saboda rashin isar da kayan agaji daga waje.” Ofishin MDD wanda yake kula da ayyukan agaji ne ya yi wannan...
Wasu jami’an diplomasiyyar turai sun yi wa gwamnatin Benjamin Netanyahu da cewa za ta fuskanci Karin matsin lamba idan har ba ta sauya halayyarta akan Gaza ba. Jaridar “Washington Post” ta Amurka ta ambato jami’an diplomasiyyar turai suna cewa; sabon tsarin da ake yin aiki da shi na raba kayan agaji a Gaza, ya juya...

Han Zheng Ya Halarci Bikin Bude Tattaunawa Ta Hudu Kan Musaya Da Koyi Da Juna A Tsakanin Al’ummomi Ta Fannin Wayewar Kansu
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Kasar Faransa ta ce daga ranar daya ga watan Yuli mai zuwa ta haramta shan sigari a wuraren taruwar jama’a. Kasar ta ce wuraren da haramcin ya shafa sun hada da makarantu da tashoshin mota ko na jirgi, wuraren shakatawa, wuraren wasanni ko kasuwanni saboda kada yara kanana su gani. Yadda ambaliyar Neja ta ci...
A tsawon kwanaki 602 a jere, sojojin mamayar Isra’ila suna ci gaba da aiwatar da kisan kiyashi kan Falasdinawa a yankin Zirin Gaza Sojojin mamayar Isra’ila na ci gaba da yakin da suke yi na kisan kiyashi a zirin Gaza, inda suka sake kaddamar da wani sabon yaki kan Gaza bayan tsagaita bude wuta. Hakan...
PUNCH Metro ta tuna cewa a kwanakin baya jami’an hukumar EFCC shiyyar Ilorin sun kama wasu mutane 17 da ake zargi da damfarar yanar gizo a cikin hadaka a Kananan Hukumomin Ilorin da Ifelodun na jihar. Oyewale ya ce an tare wadanda ake zargin ne a madatsar ruwa ta Asa da yankin Jami’ar Al-Hikmah da...
Wasu mutum 12 ’yan gida daya da almajirai sama da 50 na cikin mutanen da suka rasu a ambaliyar ruwan da ta afka wa yankin Tiffin Maza da Anguwan Hausawa na karamar hukumar Mokwa a jihar Neja a ranar Laraba. Ambaliyar, wacce ta biyo bayan wani mamakon ruwan sama da aka tafka a daren na...
Kasar Brazil ta jaddada goyon bayanta ga ‘yancin Jamhuriyar Musulunci ta Iran na amfani da makamashin nukiliya na zaman lafiya A yayin ganawarsa da sakataren kwamitin kolin tsaron kasar Iran, mataimaki na musamman ga shugaban kasar Brazil ya sanar da cewa kasarsa tana goyon bayan ‘yancin Jamhuriyar Musulunci ta Iran na yin amfani da makamashin...
Sanarwar bayan taron koli na hadin gwiwar Sin da kungiyar tarayyar kasashen kudu maso gabashin Asiya wato ASEAN, da kwamitin hadin gwiwar kasashen Larabawa na yankin Gulf wato GCC, ta jaddada burin sassan uku na bunkasa hadin gwiwar raya tattalin arziki, musamman ta hanyar gudanar da cinikayya marar shinge, da kammala yarjejeniyar gudanar da cinikayya...
Shugaban kwamitin kungiyar Tarayyar Afrika (AU) Mahmoud Ali Youssouf, ya nanata godiyar kungiyar bisa irin goyon bayan da kasar Sin ke ba ta da ma kasashen Afrika a muhimman bangarori kamar na cinikayya da raya ababen more rayuwa da aikin gona da kiwon lafiya da bunkasa kwarewar jami’ai. Wata sanarwa da aka fitar jiya Laraba,...
Ɗaruruwan ɗalibai ne suka suka tsallake rijiya da baya a lokacin da ajujuwan da suke rubuta jarabawar kammala sakandare (SSCE) a ranar Laraba. Lamarin ya faru ne a makarantar sakandiren gwamnati da ke Namne a Ƙaramar hukumar Gassol a Jihar Taraba. Ko kwabo ban ciyo bashi ba tun da na zama Gwamnan Kaduna – Uba...
Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya ce tun da ya hau kujerar mulki shekaru biyu da suka wuce ko kwabo bai ciyo ba a matsayin bashi. Ya bayyana hakan ne lokacin da yake zantawa da wasu ’yan jaridu a Kaduna ranar Alhamis, albarkacin cikarsa shekaru biyu a mulki. A cewar Gwamnan, bankuna da dama...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A yau shekara biyu ke nan cif tun bayan da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya karɓi mulkin Najeriya a matsayin shugaban ƙasa na 16 tun bayan samun ‘yancin kai. Daya daga cikin abubuwan da shugaban kasar ya fara yi yayin jawabin karbar mulkin shi ne sanar da...
A ci gaba da tafka laifukan yakin da HKI take yi a Gaza,Fiye da Falasdinawa 60 ne su ka yi shahada a jiya Laraba. A wani harin da sojojin mamayar su ka kai a yankin Jabaliya, Falasdinawa 5 sun yi shahada, yayin da wani adadi mai yawa su ka jikkata. Wani jirgin sama maras matuki...
Daya daga cikin maniyyata Aikin Hajjin bana daga jihar Filato mai suna Hajiya Zainab ta mayar wa da wani dan kasar Rasha kudinsa da ta tsinta a birnin Makka na kasar Saudiyya, har kimanin Naira miliyan takwas da dubu 200. Rahotanni sun nuna matar ta tsinci guzirin maniyyacin ne a Masallacin Harami na Makka a...
Shugaban rundunar mayakan sama ta kasa,Air Marshal, Hassan Abubakar, ya bukaci tsoffin daliban makarantar ‘ya’yan sojoji dake Zaria watau NMS da su kasance masu kwazo da da’a a duk inda suke kamar yadda suka koya a makarantar. Ya bayyana haka ne lokacin da ya ke jawabi a matsayin Babban bako na musamman a wurin bukin...
Kunngiyar Tarayyar Turai, ta ce ba ta gamsu da sabon tsaron raba kayan agajin jin kai da Amurka da Isra’ila ke shirin aiwatarwa a Gaza. Babbar jami’ar diflomasiyyar kungiyar, Kaja Kallas, ta bayyana cewa Tarayyar Turai ba ta goyon bayan sabon tsarin raba agajin jin kai da Amurka da Isra’ila ke kokarin aiwatarwa wanda ke...
Dakarun sojojin Najeriya sun dakile wani harin hadin gwiwa da ‘yan ta’addar Boko Haram da ISWAP suka kai a yankin Marte da ke jihar Borno, inda suka kashe wasu da dama daga cikin maharan. Majiyar leken asirin hedikwatar sojan Najeriya ta tabbatar da cewa harin ya faru ne da misalin karfe 1:35 na wayewar safiyar...
Falasdinawa da dama ne suka ji rauni a jiya Talata a lokacinda yahudawan Sahyoniyya suka bude rumbunajiyar kayakin abinda ga Falasdinawa a garin Rafah na kudancin gaza. Shafin yanar gizo na Afirka News ya bayyana cewa dubban Falasdinawa wadanda suka yi kwanaki 90 basu sami abinci ba saboda rufe kofar shiar da abinci zuwa gaza....
Gwamnatin kasar Ireland ta yi doka a jiya Talata wacce ta hana a shigar da duk wasu kaya da aka kera a matsugunan ‘yan share wuri zauna da a karkashin dokokin kasa da kasa ake daukarsu a matsayin haramtattu. Mai Magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Ireland ya fada wa kamfanin dillancin labaurn Faransa cewa;...
Sun kara da cewa, kasashen Afirka za su kafe kai da fata wajen mutunta ka’idar Sin daya tak a duniya, da goyon bayan duk kokarin da kasar Sin ta yi na kare ikon ’yancinta da cimma burin sake hadewar kasar, da yin adawa da tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Sin, kana suka ce,...
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da wasikar taya murna ga taron kasa karo na tara na kungiyar yara jagorori na kasar Sin (CYP), wanda aka bude a yau Talata a birnin Beijing. Xi ya jaddada muhimmancin ganin kungiyar ta bi sawun jam’iyyr kwaminis ta kasar Sin a da kuma yaye hazikai masu gina...
Tabbas a halin yanzu, wasu kasashe ba su ba da’a muhimmanci ba, kana suna ta daukar matakan kashin kai yadda suka ga dama, lamarin da ya sa al’amuran kasa da kasa suka shiga rudani. Dangane da wannan batu, dole ne Sin da kasashen Afirka masu da’a su karfafa hadin kai, su yi adawa da...
Gwamnatin Jihar Kano ta amince da kashe Naira miliyan dari da hamsin da ɗaya da dubu dari takwas da sittin da uku (N151,863,895.97) domin sake gina wani masallaci da wani matashi ya cinna wa wuta a yayin da jama’a ke tsaka da sallar Asuba a cikin jam’i a Tiga Gadan da ke Karamar Hukumar Gezawa,...
Babbar Kotun Musulunci a Jihar Kano ta yanke wa Shafiu Abubakar hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda cinna wuta a wani masallaci a kauyen Gadan, Karamar Hukumar Gezawa, yayin da jama’a ke tsaka da jam’in sallar asuba a ranar 15 ga Mayu, 2024. Harin ya yi sanadiyar mutuwar mutane 23 tare da raunana wasu. An...