An rantsar da Samia Suluhu Hassan a wa’adin mullki na biyu a Tanzaniya
Published: 3rd, November 2025 GMT
An rantsar da Samia Suluhu Hassan a wa’adin mullki na biyu a matsayin shugabar Tanzaniya, duk da tarzomar da ta ɓarke bayan zaɓen da aka gudanar a makon jiya.
A wani ƙwarya-ƙwaryar biki da aka gudanar cikin matakan tsaro a Dodoma, babban birnin ƙasar, an rantsar da shugabar a wani wurin da ba a bai wa mutane da dama sun halarta ba.
Riƙe da Al-Qura’ni a hannu guda, Shugaba Hassan ta ce “na yi alƙawalin yi wa ’yan ƙasa aiki tuƙuru, zan yi biyayya ga dokoki na ƙasa da mutunta kundin tsarin mulki.”
Baƙin da aka gayyata ne kawai aka bai wa damar halartar rantsar da Shugaba Hassan a bikin da aka haska duk da katse intanet, yayin da ake ci gaba da zaman ɗar-ɗar a ƙasar kan sakamakon zaɓen.
An ayyana Hassan, wadda ta hau mulki a shekarar 2021 bayan rasuwar tsohon shugabanta, a matsayin wadda ta lashe zaɓen Larabar makon da ya gabata da kashi 97.66% na ƙuri’un da aka kaɗa.
Sai dai ’yan hamayya sun yi watsi da sakamakon kan zargin maguɗi, suna mai cewar an yi amfani da ƙarfin da ya wuce ƙima kan masu bore bayan ɓarkewar zanga-zangar adawa da sakamakon zaɓen.
Hassan, mai shekaru 65, ta tsaya takara ne kawai da ’yan takara daga ƙananan jam’iyyu bayan da aka hana manyan masu ƙalubalantarta daga manyan jam’iyyun adawa biyu shiga takarar.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
An kashe ’yan bindiga 19 yayin wani hari a Kano
Sojoji sun daƙile wani harin ’yan bindiga a ƙaramar hukumar Shanono da ke Jihar Kano, inda suka yi nasarar hallaka 19 daga cikin ’yan ta’addan.
Bayanai sun ce sojojin sun fafata da ‘yan bindigar ne da yammacin ranar Asabar bayan samun bayanan sirri a yankunan Unguwar Tudu da Unguwar Tsamiya.