Hamas ta musanta kalaman Witkoff game da batun mika makamanta
Published: 5th, August 2025 GMT
Kungiyar Hamas, ta musanta kalaman da wakilin Amurka Steve Witkoff, inda ya yi ikirarin cewa kungiyar ta bayyana aniyar ta na yin watsi da makamanta.
Kungiyar ta tabbatar da cewa, tsayin daka da makamanta hakki ne na kasa kuma na shari’a matukar dai an ci gaba da mamaye Falastinu, kuma dukkanin dokoki na kasa da kasa sun amince da hakan a ka’idojin MDD.
Kungiyar ta jaddada cewa, “wadannan makamai ba za a yi watsi da su ba sai ta hanyar dawo mana da cikakken ‘yancinmu na kasa, wato kafa kasar Falasdinu mai cikakken ‘yanci, mai cin gashin kanta tare da Kudus a matsayin babban birninta.”
A baya can, Hamas ta zargi Witkoff da gudanar da wani shiri a ziyarar da ya kai cibiyoyin rarraba agajin da ke karkashin kulawar gidauniyar jin kai ta Gaza, tana mai imani da cewa manufar hakan it ace cimma wani buri na siyasa, da kuma yin amfani da yunwa ta wata hanyar don ci gaba da kashe fararen hula a zirin Gaza.
A cikin wata sanarwa da aka fitar, kungiyar ta bayyana cewa, kalaman karya na Witkoff, tare da hotunan farfaganda na rangadinsa a Gaza, ba sa nuna hakikanin gaskiyar abin abin da yake faruwa a kasa,” inda Falasdinawa sama da 1,300 ne yunwa ta lakume rayukansu a Gaza a cikin ‘yan lokutan baya-bayan nan, sabanin abin da shi kuma yake bayyanawa kan cewa ana ci gaba da raba agaji da kuma tallafawa al’ummar Gaza da abinci da abubuwan bukatar rayuwa.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Araqchi: Namijin kokarin al’ummar Iran abin yabawa ne August 4, 2025 Khatibzadeh: Iran ba za ta amince da saryar da hakkokinta ba a duk wata tattaunawa da Amurka August 4, 2025 Rahotonni: Agajin Jin kai Da Ake Jefawa Ta Sama A Gaza Ba Shi Da Tasiri August 4, 2025 Wa’adin Da Shugaban Amurka Ya Gindaya Na Kawo Karshen Yaki A Ukraine Ya Karato Ba Tare Da Alamun Karewarsa Ba August 4, 2025 Sojojin Somaliya Sun halaka Mayakan Kungiyar Al-Shabab Fiye Da Hamsin A Kudu Maso Yammacin Mogadishu August 4, 2025 Pakisatan: Iran Ce Madogara Ga Al-ummar Musulmi August 4, 2025 Wakilin Hukumar FAO A Iran Yace Sauyin Yanayi Ya shafi Dukkan Yankin August 4, 2025 Malamai A Najeriya Suna Goyon Bayan Iran A Yadda Take Fuskantar HKI August 4, 2025 Shugaban Kasar Lebanon Ya Yi Alkawalin Adalci Ga Wadanda Feshewar Beirut Ta Shafa August 4, 2025 Iran Ta Ce Ba Wani Ma’aikacin Hukumar IAEA A Kasar A Halin Yanzu August 4, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Kungiyar ta
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Kasar Lebanon Ya Yi Alkawalin Adalci Ga Wadanda Feshewar Beirut Ta Sha
Shugaban kasar Lebanon Josepth Aoun ya yi alkawalin adalci ga iyalan wadanda fashewar tashar jiragen ruwa na Beirut ya sha bayan shekaru 5 da aukuwar hakan.
Shafin yanar gizo na labarai Arab News ya nakalto shugaban yana fadar haka a yau litinin. Ya ce har yanzun ba wanda aka kama ko ake tuhuma da haddasa wannan fashewar tun aukuwarsa a ranar 4 ga watan Augustan shekara 2020.
Labarin ya kara da cewa Fashewar tashar jiragen ruwa na Beirut shi ne fashewa mafi muni bayan na manyan manyan makamai kare dangi, inda a wannan karon taki wanda aka yi shi da sinadarin ‘Amonium nitrate’ ya fashe ya kuma kashe mutane 220 sannan wasu kimani 6,500 suka ji rauni da kuma asarar dukiyoyin wanda ya kai biliyoyin dalar Amurka.
Shugaba Aoun ya cewa sai gudanar da bincike tun asalinsa, don gano yadda aka ajiye takin a inda aka ajiye shi da kuma musabbabin fashewarsa. Ya ce ba wanda za’a bari idan har bincike ya kai kansa.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran Ta Ce Ba Wani Ma’aikacin Hukumar IAEA A Kasar A Halin Yanzu August 4, 2025 Pezeshkian ya yaba da irin goyon bayan da Pakistan ta baiwa Iran a lokacin yaki August 4, 2025 Bloomberg: FBI ta cire sunan Trump daga Fayilolin badakalar Epstein August 4, 2025 Jerin gwanon nuna goyon baya ga al’ummar Gaza a Sydney Australia August 4, 2025 MDD ta yi gargadi game da mummunar matsalar da yunwa ka iya haifarwa ga al’ummar Gaza August 4, 2025 Rasha da China sun fara wani gagarumin atisayen soji na hadin gwiwa a tekun Japan August 4, 2025 Araqchi Ya Bayyana Makomar Sinadarin Uranium Da Iran Ta Inganta A Lokacin Yaki August 3, 2025 Dakarun Kare Juyin Juya Halin Musulunci Sun Bayyana Cewa: Masu Shirin Halaka Gaza Suna Son Mamaye Duniyar Musulmi Ne August 3, 2025 Iran Ta Jaddada Cewa: Karfin Makamai Masu Linzami Da Jiragen Sama Marasa Matuka Ciki Suna Nan Cikin Shiri August 3, 2025 Gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila Tana Kokarin Boye Barnarta A Zirin Gaza August 3, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci