Aminiya:
2025-11-03@07:14:17 GMT

Mu daina zagin malaman addini idan muna son zaman lafiya — Uba Sani

Published: 5th, August 2025 GMT

Gwamnan Kaduna, Malam Uba Sani, ya gargadi ’yan siyasa da masu amfani da kafafen sada zumunta da su daina zagin malaman addini da a yanzu ya zama ruwan dare a ƙasar nan.

Gwamnan ya bayyana cewa irin wannan mummunar ɗabi’a ta cin zarafi malaman addini na iya lalata zamantakewa da tubalin zaman lafiya a tsakanin al’umma.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin tattaunawarsa da malaman addini da na gargajiya a birnin Kaduna, inda ya jaddada muhimmancin rawar da shugabannin addini ke takawa wajen ƙarfafa zaman lafiya da haɗin kai.

Tinubu ya bai wa ’yan wasan ƙwallon kwandon mata kyautar Dala dubu 100 da gidaje Gwamnatin Kano ta karɓi rahoton binciken Kwamishinan da ya yi belin Danwawu

“Ina nanata cewa, idan muka bari shugabannin addini suka zama abin zagi da cin mutunci ba gaira ba dalili, to ita kanta ƙasar nan za ta lalace balle wata jiha. Duk lokacin da abubuwa suka rikice, wurinsu muke komawa domin neman addu’o’i,” in ji Gwamnan.

Malam Uba Sani ya bayyana damuwarsa kan yadda wasu ’yan siyasa ke haɗa kai da wasu da ya bayyana da “marasa sanin abin da ya dace” wajen ɓata suna da yi wa malamai ƙage a kafafen sada zumunta.

Ya buƙaci shugabanni da mabiyansu da su guji yin amfani da malaman addini wajen biyan buƙatun siyasa ko na ƙashin kai, yana mai jaddada cewa hakan yana barazana ga zaman lafiya da jituwa da ake morewa a Kaduna da ma ƙasar baki ɗaya.

Gwamnan ya kuma yaba da rawar da malaman addini suka taka tun daga lokacin da ya hau mulki har kawo yanzu, yana cewa sun kasance ginshiƙi wajen samar da zaman lafiya a jihar.

“Da ba don su ba, da babu damar da muke da ita yau ta cin moriyar zaman lafiya a Jihar Kaduna,” in ji shi.

Ya nuna rashin jin daɗinsa kan yadda ’yan siyasa ke watsi da malamai bayan samun nasarar zaɓe, sannan su sake waiwayarsu idan zaɓe ya gabato.

“Muna tunawa da su ne wata ɗaya ko biyu kafin zaɓe. Muna zuwa wajen su da maganganu na yaudara da daɗin baki dangane da addini, domin su mara mana baya.”

Uba Sani ya kuma buƙaci a samar da alaƙa ta dindindin da shugabannin addini, ba sai kawai lokacin da zaɓe ya kusanto ba.

“Malamai da shugabannin addini muhimman jiga-jigai ne a tsarin ƙasa, shi ya sa muke ganin lallai muna buƙatar su a koyaushe wajen shiriya, ba sai lokacin zaɓe ba,” in ji shi.

Ya ce tun farkon mulkinsa, ya samu shawarwari masu amfani daga shugabannin addini kan batutuwan zaman lafiya, haɗin kai da kwanciyar hankali a jihar.

A ƙarshe, ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da bai wa shugabannin al’umma muhimmanci a duk wani sha’ani da ya shafi tsaro, yana mai cewa zaman lafiya mai ɗorewa ba zai samu ba sai da amincewar jama’a da haɗin gwiwa.

“Mun bayyana cewa ba za mu tura jami’an tsaro zuwa kowace unguwa ba tare da tuntubar shugabannin yankin ba. Su za su ɗauki nauyi, su tsara, sannan gwamnati ta tallafa musu,” in ji gwamnan.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: zaman lafiya

এছাড়াও পড়ুন:

Gumi Ya Nemi Nijeriya Ta Katse Hulɗa Da Amurka Idan Trump Bai Janye Barazanar Sa Ba

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Ƙasashen Da Ba Su Yanke Hukuncin Kisa A Duniya Ba November 2, 2025 Manyan Labarai 2027: Yadda Gwamnoni Suka Yi Fatali Da Mataimakansu Wajen Zaɓo Waɗanda Za Su Gaje Su November 2, 2025 Manyan Labarai Wadi Al-Salam: Maƙabartar Musulmai Mafi Girma A Duniya November 2, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gumi Ya Nemi Nijeriya Ta Katse Hulɗa Da Amurka Idan Trump Bai Janye Barazanar Sa Ba
  • Gidauniyar IRM Da KADCHMA, Ta Ƙaddamar Da Inshorar Lafiya Kyauta Ga Mutane 200 A Kaduna
  • Muna shirin kai farmaki a Nijeriya — Ma’aikatar Yaƙin Amurka
  • Kiristoci: Najeriya ba ta yadda da cin zarafin addini ba — Tinubu
  • Zargin Kisan Kiristoci: Najeriya ba ta yadda da cin zarafin addini — Tinubu
  • Zargin Kisan Kiristoci: Maganar Trump a kan Najeriya tsagwaron ƙarya ce — Shehu Sani
  • Gwamna Uba Sani Ya Bayyana Tsare-tsaren Ci Gaban Kaduna a Taron Duniya a Dubai.
  • Shugabar Tanzania Samia Suluhu Ta Lashe Zaɓe, Duk Da Rikicin Da Ya Mamaye Ƙasar
  • CMG Ta Kammala Gabatar Da Rahoto Kan Ganawar Shugabannin Sin Da Amurka
  • Gwamnatin Jigawa Za Ta Gina Gidaje 52 A Babban Birnin Jihar