Aminiya:
2025-09-19@15:54:56 GMT

’Yar shekara 17 daga Yobe ta lashe Gasar Turanci ta Duniya

Published: 5th, August 2025 GMT

Wata yarinya ’yar shekara 17, Nafisa Abdullah, daga Jihar Yobe, ta lashe Babbar Gasar Harshen Turanci ta Duniya ta ‘TeenEagle’ ta shekarar 2025 da aka gudanar a birnin Landan, fadar gwamnatin  ƙasar Birtaniya.

Nafisa ta zama Gwarzuwar Shekarar 2025 ce baya da ta fafata ne da sama da mahalarta gasar 20,000 daga ƙasashe kusan 69 na duniya, inda ta zama ta ɗaya a Gasar ‘UK Global Finals’, sakamakon fintinkau da ta yi wa takwarorinta na ƙasashe daban-daban da ke jin harshen Ingilishi a duniya.

Wannan nasara ta lashe wannan babbar gasa da Nafisa ta samu ya haifar da alfahari a faɗin Najeriya, musamman a mahaifarta, Jihar Yobe. Nafisa ta wakilci Najeriya ne daga Kwalejin Tulip International College (NTIC), Jihar Yobe.

A wani jawabi da ya gabatar jim kaɗan da sanarwar lashe gasar, wani ɗan uwan Nafisa, Malam Hassan Salihu, ya yaba wa Gwamnatin Jihar Yobe da Makarantar NTIC bisa irin gudunmawar da suna bayar har ya kai ga samun nasarar ’yar uwarsa a wannan babbar gasa ta duniya. Ya ƙara da yaba wa shugabannin kwalejin bisa ga yadda suke gudanar da karatuttukansu da hakan ne ta kai ga nasarar.

Tinubu ya bai wa ’yan wasan ƙwallon kwandon mata kyautar Dala dubu 100 da gidaje Sanata Buba ya ƙaddamar da allurar rigakafin dabbobi kyauta

“Tabbas wannan nasara da Nafisa ta samu da taimakon Allah (SWT) ne,” in ji shi, kuma nasarar wata babbar shaida ce ga abin da matasan Najeriya za su iya cimma idan aka ba su dama da goyon baya.

“Alal haƙiƙa wannan nasara da Nafisa ta samu ya zama abin farin ciki da alfahari ga duk al’ummar jiharmu ta Yobe da ma ƙasa baki daya,” in ji Malam Hassan.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Gasar Harshen Turanci Gasar Turanci Najeriya

এছাড়াও পড়ুন:

Tinubu Ya Janye Dokar Ta-baci A Jihar Rivers

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanar da janye dokar ta-baci a Jihar Rivers daga ƙarfe 12 na daren 17 ga watan Satumban 2025.

Shugaban Ƙasar, a wata sanarwa da ya sanya wa hannu, ya ce dokar ta-bacin da ta dakatar da Gwamna, Mataimakiyarsa, da ‘yan majalisar dokokin jihar na tsawon watanni shida ta cimma manufarta na dawo da zaman lafiya a jihar.

Tinubu ya bayyana cewa ya yi amfani da Sashe na 305 na Kundin Tsarin Mulkin 1999 ne a watan Maris na 2025 sakamakon durƙushewar mulki a Jihar Rivers.

A cewarsa, rashin jituwa tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara da Majalisar Dokokin Jihar, da kuma lalata muhimman kadarorin gwamnati sun jefa jihar cikin rikici.

“Lamarin ya kai ga Babbar Kotun Ƙoli ta bayyana a ɗaya daga cikin hukuncinta cewa babu gwamnati a Jihar Rivers.” In ji Shugaban Ƙasa.

Ya gode wa Majalisar Ƙasa bisa amincewa da wannan sanarwa, tare da yabawa Sarakuna da jama’ar jihar bisa haɗin kan da suka bayar.

Tinubu ya kuma yaba wa  masu adawa da suka kalubalanci wannan mataki a kotu, yana cewa wannan shi ma wani ɓangare ne na dimokuraɗiyya.

Da yake magana kan sabuwar fahimta tsakanin manyan ‘yan siyasa a jihar, Shugaban Ƙasa ya ce babu dalilin ƙara tsawaita dokar ta-bacin.

Ya bayyana cewa Gwamna Siminalayi Fubara, da Mataimakiyarsa Ngozi Nma Odu, da Shugaban Majalisar Dokoki Martins Amaewhule da dukkan mambobin majalisar jihar za su koma bakin aiki daga 18 ga Satumban 2025.

Tinubu ya yi kira ga shugabannin siyasa a faɗin Najeriya da su ƙarfafa zaman lafiya da haɗin kai domin isar da fa’idodin dimokuraɗiyya ga al’umma.

 

Daga Bello Wakili

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ’Yan bindiga sun kai hari sakatariyar ’yan jarida ta jihar Yobe
  • Nan Ba Da Jimawa Ba Hauhawar Farashin Kayayyaki Za Ta Zama Tarihi —Fadar Shugaban
  • Shugaban Guinea-Bissau Ya Goyi Bayan Shawarar Tsarin Shugabancin Duniya Da Sin Ta Gabatar
  • Uwargidan Shugaban Kasa, Oluremi Tinubu Ta Yi Kira Ga Zaman Lafiya A Duniya
  • Pezeshkian: Iran da Masar suna da tsohon tarihi a duniya
  • Zinariya, Azurfa, da Tagulla na Iran a Gasar Kokawa ta Duniya
  • Tinubu Ya Janye Dokar Ta-baci A Jihar Rivers
  • Guterres: Jerin Shawarwarin Da Sin Ta Gabatar Sun Cika Ka’idar Kundin Tsarin Majalisar Dinkin Duniya
  • Duniya na tir da sabon farmakin Isra’ila kan Gaza
  • ALGON ta karrama Gwamna Buni da lambar yabo kan kawo ci gaba a Yobe