Sojojin Somaliya Sun halaka Mayakan Kungiyar Al-Shabab Fiye Da Hamsin A Kudu Maso Yammacin Mogadishu
Published: 4th, August 2025 GMT
Sama da mayakan kungiyar ta’addanci ta Al-Shabaab 50 ne suka halaka a yankin kudu maso yammacin birnin Mogadishu fadar mulkin kasar somaliya
Tawagar wanzar da zaman lafiya ta Tarayyar Afirka a Somaliya ta sanar a ranar Lahadin da ta gabata cewa; Sama da mayakan kungiyar ta’addanci ta Al-Shabaab 50 ne suka halaka a wani samame da dakarun sojin Somaliya suka kai a garin Bireire da ke kudu maso yammacin Mogadishu fadar mulkin kasar.
Tawagar ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta fitar cewa: “A samamen hadin gwiwa da sojojin kasar Somaliya domin kwato garin Bireire a ranar 1 ga watan Agusta, ya haifar da hasara mai yawa ga ‘yan ta’addar, tare da kashe mayakan Al-Shabaab fiye da 50, wasu kuma sun samu munanan raunuka.”
Tawagar ta ambato wakilin musamman na shugaban hukumar Tarayyar Afirka a Somaliya, Alhaji Ibrahima Deini yana cewa: “Dakarun tawagar da sojojin kasar Somaliya sun kuduri aniyar kwato garin Bireire da sauran yankunan da har yanzu ke karkashin ikon kungiyar Al-Shabaab, domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali ga al’ummar Somaliya.”
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label Name* Email* Website Label Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Pakisatan: Iran Ce Madogara Ga Al-ummar Musulmi August 4, 2025 Wakilin Hukumar FAO A Iran Yace Sauyin Yanayi Ya shafi Dukkan Yankin August 4, 2025 Malamai A Najeriya Suna Goyon Bayan Iran A Yadda Take Fuskantar HKI August 4, 2025 Shugaban Kasar Lebanon Ya Yi Alkawalin Adalci Ga Wadanda Feshewar Beirut Ta Shafa August 4, 2025 Iran Ta Ce Ba Wani Ma’aikacin Hukumar IAEA A Kasar A Halin Yanzu August 4, 2025 Pezeshkian ya yaba da irin goyon bayan da Pakistan ta baiwa Iran a lokacin yaki August 4, 2025 Bloomberg: FBI ta cire sunan Trump daga Fayilolin badakalar Epstein August 4, 2025 Jerin gwanon nuna goyon baya ga al’ummar Gaza a Sydney Australia August 4, 2025 MDD ta yi gargadi game da mummunar matsalar da yunwa ka iya haifarwa ga al’ummar Gaza August 4, 2025 Rasha da China sun fara wani gagarumin atisayen soji na hadin gwiwa a tekun Japan August 4, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
An Tube Yarima Mai Jiran Gado Na Birtaniya Bayan Da Aka Tabbatar Da Laifinsa
Bayan kwashe shekaru ana taƙaddama kan abubuwan kunya da ake zargin shi da aikatawa, a yanzu an tube shi, kacokan, duk wata alfarma ko sarauta ko mukami daga tsohon yariman Birtaniya Andrew, wanda da ne ga marigayiya Sarauniya Elizabeth II.
Fadar masarautar Birtaniya ta Buckingham Palace ce da kanta ta fitar da sanarwa game da hakan. A yanzu “za a rika kiransa da tsuran sunansa, wato Andrew Mountbatten Windsor,” in ji sanarwar.
Masarautar na fatan wannan mataki nata zai kawo karshen muhawara kan jerin abin kunyar da ake zargin yariman ya aikata wadanda ake alakantawa da masarautar.
Yanzu an tube shi karfi da yaji, duk wasu sarautu da ke kansa, kamar yariman York da sauran su.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kasashen Pakistan Da Afghanistan Sun Tsawaita Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta October 31, 2025 M D Duniya Tayi Gargadi Game Da Gwajin Nukiliya Da Amurka Ta Sanar Za ta yi October 31, 2025 Sudan Ta Yi Kira Ga Kwamitin Tsaro Da Ya Ayyana RSF A Matsayin Kungiyar ‘Yan Ta’adda October 31, 2025 Araqchi: Gwajin Makaman Nukiliya Na Amurka Babbar Barazana Ce Ga Duniya October 31, 2025 Masar da Eritrea Sun Tattauna Bukatar Tallafawa Kasar Sudan October 31, 2025 Shugaban Lebanon Ya Umarci Sojoji Da Su Fuskanci Kutsen Na Isra’ila A Kudancin Kasar October 31, 2025 Madagascar Ta Sanar da Kafa Sabuwar Gwamnati Tare da Manyan ‘Yan Adawa October 31, 2025 Iran ta yi fatali da kalamman IAEA Kan Shirin Nukiliyarta October 30, 2025 Trump Ya Umarci Ma’aikatar Yakin Amurka Ta koma gwajin makaman nukiliya October 30, 2025 Isra’ila ta amince da fadada matsugunai a Yammacin Kogin Jordan October 30, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci