Leadership News Hausa:
2025-08-04@17:37:18 GMT

Yaran Gaza Suna Da Hakkin Rungumar Gobe

Published: 4th, August 2025 GMT

Yaran Gaza Suna Da Hakkin Rungumar Gobe

“Jerin sunayen yaran Gaza da ke mutuwa “, dole ne a tabbatar da ba a kara yawansu ba. Shin wadannan sunayen yara kanana da hotunan su ba za su iya tada hankalin bangarori masu rikici ba?

 

Akasarin kasashen duniya sun yarda cewa “shawarar samar da kasashe biyu” ita ce mafitar warware matsalar Falasdinu, kuma amincewa da kasar Falasdinu wani muhimmin mataki ne na aiwatar da wannan shawara.

Kwanan nan, an gudanar da babban taron kasa da kasa kan warware matsalar Falasdinu da aiwatar da shawarar “samar da kasashe biyu” a hedkwatar MDD da ke birnin New York, inda ministocin harkokin wajen kasashe 15 suka sanya hannu kan sanarwar hadin gwiwa, suna nuna niyyar amincewa da kasar Falasdinu. A yanzu, fiye da kashi biyu bisa uku na kasashe membobin MDD sun amince da kasar Falasdinu. Muna fatan ganin an tabbatar da shawarar “kafa kasashe biyu” da wuri, domin hasken zaman lafiya ya zo Gaza. Yaran Gaza ma yara ne, kamar kowane yaro na kowane iyali a duniya, suna da hakkin rungumar gobe. (Mai zane da rubutu:MINA)

 

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Sauya Sheƙa: Sanatoci Biyu APC Ke Buƙata Wajen Samun Kashi Biyu Cikin Uku A Majalisar Dattawa

Saboda haka, ƙarfin APC a zauren majalisar dattawa mai mambobi 109 ya kai 70, kujeru biyu kadai take buƙata ta cika 72 don samun rinjaye na kashi biyu cikin uku.

PɗP yanzu haka tana da kujeru 28, yayin da jam’iyyar LP ke da biyar. Jam’iyyar SɗP na da kujeru biyu, yayin da jam’iyyar NNPP da APGA ke da kujeru guda daya kowannansu.

A yanzu haka, akwai kujeru biyu na majalisar dattawa da babu kowa. Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), har yanzu ba ta gudanar da zaɓen cire gurbin Sanata Ifeanyi Ubah, mai wakiltar Anambra ta kudu, wanda ya rasu a farkon wannan shekara, da Sanata Monday Okpebholo, mai wakiltar Edo ta tsakiyar, wanda ya bar kujerarsa bayan lashe zaɓen gwamna na Jihar Edo a 2024.

Kazalika, a majalisar wakilai ma an samu sauya sheƙar mambobi guda uku daga PɗP zuwa APC a ranar Laraba, wanda ya kuma ƙara ƙarfafa ƙarfin jam’iya mai mulki zuwa samun kujeru 224 a cikin kujeru 360 na majalisar. ƴan majalisar wakilan da suka saura sheƙa sun hada da Taofeek Ajilesoro da Omirin Emmanuel Olusanya daga Jihar Osun, tare da Marcus Onobun daga Jihar Edo da kuma Mark Esset daga Akwa Ibom.

Bisa wannan lamari, PɗP yanzu tana da kujeru 86, yayin da jam’iyyar LP take da kujeru 26, NNPP ta da 16, APGA ta da shida, SɗP ta da biyu, sannan ADC tana da daya.

A halin yanzu, akwai kujeru biyar a majalisar wakilai da babu kowa sakamakon mutuwar ƴan majalisar guda huɗu da kuma daya da ya yi murabus.

da yake tsokaci kan samun rinjayen APC a zauren a majalisun tarayya a gaban zabɓen 2027, masana kimiyyar siyasa, Farfesa Gbade Ojo, ya yi gargaɗi game da mummunan sakamako ga makomar dimokuraɗiyyar Nijeriya.

Ya ce, “Abin da muke shaida shi ne, APC na ƙara samun gagarumin rinjaye. ɗuk da cewa hakan na iya bayyana matsayin siyasa mai ƙarfi a zahiri, tasirin wannan ga dimokuraɗiyya yana da matukar damuwa. 

“Lokacin da wata jam’iyyar mai mulki a cikin dimokuraɗiyya ta mamaye majalisa har ta samu kashi biyu cikin uku na yawan mambobi, hakan yana zama wani siffofi na mulkin kama-kurya, domin ba za a samu ingantaccen kulawa da daidaito ba,” in ji shi.

Ya ba da shawara cewa a irin wannan yanayi, majalisun tarayya na iya rasa ƴancin kai da zama ƴan amshin shata ga ɓangaren zantarwa.

Ya gargaɗin cewa in har ƴan adwa ba su sake tsarawa ba ta hanyar dawo da tsaftataccen tsarin cikin gida da kafa wani takamaiman aƙidar tunani, dimokuraɗiyyar Nijeriya za ta ci gaba da kasancewa cikin hatsari da rashin daidaito.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • MDD ta yi gargadi  game da mummunar matsalar da yunwa ka iya haifarwa ga al’ummar Gaza
  • Dakarun Kare Juyin Juya Halin Musulunci  Sun Bayyana Cewa: Masu Shirin Halaka Gaza Suna Son Mamaye Duniyar Musulmi Ne
  • IRGC Tace Bata Amince Da Kasashen Biyu A Kan Kasar Falasdinu Ba
  • Iran Da Japan Suna Iya Jagorantar Duniya Don Rabata Da Makamai Kare Dangi
  • Kungiyar Hamas Ta Bayyana Cewa Ba za ta Ajiye Makamanta ba Sai Bayan samar Da Kasar falasdinu
  • Jamus ta soma jefa kayan agaji a Zirin Gaza
  • Babban Jami’in MDD: Kokarin Sin A Fannin Samun Ci Gaba Mai Dorewa Na Da Matukar Alfanu Ga Yanayin Duniya
  • Sauya Sheƙa: Sanatoci Biyu APC Ke Buƙata Wajen Samun Kashi Biyu Cikin Uku A Majalisar Dattawa
  • Sin Ta Kadu Da Takunkumin Da Amurka Ta Kakaba Wa Hukumomi Da Jami’an Falasdinu