2025-12-15@03:41:14 GMT
إجمالي نتائج البحث: 3202
«Yan uwa»:
Haddadiyar Kungiyoyin Makiyaya na kasashen Africa (CORET) ta bayyana cewa an samu karin yawan ɗalibai a makarantun makiyaya cikin watanni goma da aka fara shirin ciyar da ɗalibai. Babban Sakataren CORET, Muhammed Bello Tukur, ya bayyana haka a taron kwana ɗaya da aka gudanar a Kaduna domin ƙara wa ma’aikata da abokan hulɗarsu...
A halin yanzu, shugaba Bola Tinubu yana ganawa da gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara a fadar shugaban kasa dake Abuja a yammacin yau Litinin. Ganawar na zuwa ne kwanaki kadan bayan Fubara ya koma ofis a ranar 19 ga watan Satumba bayan da Shugaba Tinubu ya janye dokar ta-ɓaci da aka kafa a jihar Ribas...
Yayin da “bikin girbi na manoman kasar Sin” na takwas ke karatowa, babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin wato JKS, shugaban kasar, kuma shugaban kwamitin kolin soja Xi Jinping, a madadin kwamitin kolin JKS, ya mika gaisuwar bikin, da fatan alheri ga manoma da ma’aikatan dake gudanar da ayyukan da suka shafi...
Mataimakin shugaban jami’ar ya ja hankalin gwamnati da cewa, yawan al’ummar Nijeriya kusan miliyan 230, kusan kashi 30 cikin 100 na matasa ne a halin yanzu ke makaranta ko kuma suke koyon sana’o’i. Don haka, ya yi gargadin cewa, hakan ya bar wani kaso mai tsoka na matasa da ba su zuwa makaranta ko...
Na hudu, an yi ta samu ci gaban sayayya sakamakon masu yawon bude ido daga ketare. Bisa ga manufar rage haraji lokacin barin kasa da kasar Sin ke gudanarwa, an shirya shirin “Sayayya a Sin” yadda ya kamata, wanda hakan ya canza fa’idar yawan baki daga ketare da suke yawon shakatawa a kasar zuwa habaka...
Ana ci gaba da takaddama a duniyar kwallon kafa kan wa ya fi cancanta da lashe kyautar Ballon d’Or a matsayin gwarzon dan wasan duniya na bana. A ranar Litinin din na za a bayar da Kyautar Ballon d’Or ta shekarar 2025 a birnin Paris na kasar Fasansa, ga wanda alakalai suka zaba a matsayin...
A jiya Lahadi ne dai jirgin ruwan agaji da aka bai wa sunan; ” Umar Mukhtar” ya bar ruwan kasar Libya domin nufar Gaza da zummar karya killace yankin da aka yi na tsawon shekaru 18. Masu kula da jirgin ruwan na “Umar Mukhtar” sun bayyana cewa; Sun yi tanadin kayan aikin liktanci da aka...
Jam’iyyar APC reshen jihar Taraba ta yi yi kakkausar suka ga mulkin Gwamna Agbu Kefas, inda ta ce bayan shekaru biyu a ofis ya gaza cika alkawuran da ya ɗauka a lokacin yaƙin neman zaɓe. Jam’iyyar ta ce rashin tasirin gwamnatin PDP zai sauƙaƙa wa APC kwace mulki a shekarar 2027 a jihar. Da yake...
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya isa birnin New York, Amurka, domin halartar taron babban zauren Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 80 wanda zai gudana daga ranar Litinin 22 ga Satumba zuwa Lahadi 28, 2025. Shettima, wanda ya wakilci Shugaba Bola Tinubu, zai gabatar da jawabin Nijeriya a gaban zauren, tare da shiga wasu tattaunawa...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Wata cuta mai cin naman jikin dan’Adam ta yi sandin mutuwar mutum takwas yayin da wasu fiye da 60 suke kwance a asibiti a garin Malabu dake Karamar Hukumar Fufure ta Jihar Adamawa. Wannan lamari dai ya jefa fargaba a zukatan mazauna yankin. NAJERIYA A YAU: Ayyukan...
Ya gargadi cewa, tarihi ba zai gafarta wa shugabannin Arewa ba idan suka kasa daukar matakin gaggawa wajen dakile kashe-kashe, garkuwa da mutane da rikice-rikicen da ke addabar yankin. Ya ce shiru da fifita wasu akan wasu daga cikin shugabanni suna kara ta’azzara matsalar tsaro a jihohin Zamfara, Kaduna, Katsina, Filato da Benuwe. Ya...
Wannan yana faruwa sosai gaskiya, kuma ƙarshe ba a wayewa da lafiya gaskiya. Masu yi gaskiya tun wuri su daina wallahi, dan aure ya sha mutuwa ta sanadin haka ƙarshe azo ana nadama mara amfani. Sosai ana samun gagarumar matsala tsakanin ma’aurata zargi ya shiga tsakani, daga nan ma dai wani aure ka ji ya...
A daren ranar 19 ga wannan wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na kasar Amurka Donald Trump sun tattauna ta wayar tarho, inda shugaba Xi ya jaddada cewa, alakar Sin da Amurka na da matukar muhimmanci, Sin da Amurka na iya cimma nasarar bai daya da wadata tare, ta yadda za su amfani...
Abdulahi, wanda ke jigilar kaya daga Agbara a Jihar Ogun zuwa Ibadan, ya ce yana kashe har Naira 25,000 a kowace tafiya da yake yi, inda mafi yawan kuɗin ke shiga hannun ƴ an Agbero a Legas, waɗanda ke gudanar da ayyukansu sa’o’i 24 a rana, kwana 7 a mako. Ya ce daga Berger, gefen...
Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta SERAP tare da Amnesty International sun nemi Shugaba Bola Tinubu ya janye ƙarar da aka shigar a kotu kan ɗan gwagwarmaya Omoyele Sowore, da kuma kamfanonin sada zumunta X da Facebook. Ƙungiyoyin sun bayyana damuwa cewa hukumomin tsaro na ƙara amfani da kotu wajen tsoratar da ƴan Nijeriya da...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Borno, ta kama mutum biyar da ake zargi da satar fakiti 7,871 na abincin yara, wanda aka fi sani da Tamuwa, wanda aka tanada don yara masu fama da cutar yunwa. Kakakin rundunar, ASP Nahum Kenneth Daso ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar 19 ga Satumba,...
A yayin da ake gudanar da shagulgulan ranar zaman lafiya ta Duniya ta Bana, Kungiyar rajin tabbatar da zaman lafiya da hadin Kai da kuma cigaban Arewacin Nigeria ta yi Kira ga Gwamnati a dukkan matakai da kuma Hukumomin tsaro su karfafa amfani da bayanan tsaro na sirri wajen kare rayukan al’ummar Kasa. Shugaban Kungiyar...
Wanda zan iya tunawa za su kai goma haka. Ko akwai wani fim wanda bayan fitar sa ka samu ƙalubale daga dangi ko wajen masu kallo? Gaskiya a fim dai har yanzu ban samu wani ƙalubale ba, saboda duk abin da nake fitowa a rol na malunta ne. Kawai dai akwai wata waƙa da na...
Ministan harkokin wajen Iran ya kore abinda wasu kafafen watsa labaru su ka watsa na zantawa a tsakaninsa da manzon Amurka a gabas ta tsakiya Steven Witkoff. Ministan harkokin wajen na Iran, Abbas Arakci ya fada wa kamfanin dillancin labarun “Tasnim” na Iran cewa; Babu gaskiya a cikin labarun da wasu kafafen watsa labaru su...
Sanarwar ta ƙara da cewa, an bayar da ƙarin kayayyakin da za a raba a matsayin tallafin ne daga Hukumar Kula da Ilimi ta Duniya (UBEC) da UNICEF. A jawabinsa a wajen taron, Gwamna Lawal ya sake nanata cewa gwamnatinsa ta zo ne da aikin ceto da sake gina jihar. Ya ce: “Tun...
Kin Amincewar Japan Game Da Muggan Laifukan Yakin Da Ta Aikata Ya Dakatar Da Bukatar Sin Ga Hukumar UNESCO
A ranar Alhamis 18 ga watan nan, aka kaddamar da fara nuna fim din nan mai taken “Evil Unbound” a dukkanin sassan duniya, fim din da ya ba da labarin yadda a yayin yakin kin mamayar dakarun Japan, wata rundunar dakarun sojin kasar Japan ta aiwatar da wani shirin sirri, na gwaje-gwajen kimiyya ta makamai...
‘Yan Ta’addan Lakurawa Sun Sake Zama Sanadin Mutuwar Mutane Da Dama A Turmutsitsin Shiga Kwale-kwale
Al’ummar Jihar Sakkwato na cike da fargaba da alhini bayan da wasu mazauna kauyuka da dama suka rasu a hatsarin kwale-kwale a Karamar Hukumar Sabon Birni ta Jihar Sakkwato. Lamarin ya faru ne lokacin da jama’a ke tserewa daga wani sabon harin da ‘yan ta’addan Lakurawa suka kai, inda kwale-kwalen da ke dauke da mutane...
Kamfanin dillancin labaran Nijeriya ya bayar da rahoton cewa, lamarin wanda ya faru ne a lokacin da ake gudanar da aikin a ƙarshen mako a masana’antar, ya yi sanadin mutuwar ma’aikata biyu ciki har da wani jami’in soji da ke aiki tare da jikkata wasu huɗu. “Na ji wani babban ƙara har sai...
A kwanan nan ne aka rufe taron kolin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai ko SCO a takaice, a birnin Tianjin dake arewacin kasar Sin, inda shugaban kasar, Xi Jinping ya gabatar da shawarar tsarin inganta jagorancin duniya. Wakiliyar babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG, ta zanta da shugaban kasar Iran,...
Wasu ’yan bindiga da ake zargin Lakurawa ne, sun kai hari ƙauyen Sayinna, da ke Ƙaramar Hukumar Tangaza a Jihar Sakkwato. Sun kashe Hakimin ƙauyen, Malam Murtala Sa’adu, tare da wani mutum mai suna Ibrahim Mai-Kuɗi. Yadda za ka dawo da kuɗinka da ka yi kuskuren turawa wa wani An tsinci gawar kwamandan hukumar NDLEA...
Daga nan ya wuce gidan tsohon shugaban ƙasa Marigayi Muhammadu Buhari domin yi wa matar sa Aisha da sauran ‘yan uwa ta’aziyya. Tinubu a gidan marigayi tsohon shugaban kasa, Buhari Ya bayyana Buhari a matsayin “shugaba mai kishin ƙasa da sadaukarwa, wanda gudunmawarsa ga haɗin kan Najeriya da ci gabanta ba za a manta da...
Sheikh Na’im Kassima wanda ya gabatar da jawabi a jiya juma’a ya kuma kara da cewa; A halin yanzu kungiyar gwagwarmaya tana fuskantar matsanancin yanayi mai hatsari,tare da jaddada cewa; Wanzuwar HKI, manufarsa ita ce a samar da wani yanki na turai da Amurka a cikin wannan yankin domin hana al’ummar yankin ci gaba da...
Kimiyyar sadarwa ta kawo sauƙin rayuwa a harkokin kasuwanci da mu’amalar kuɗi ta banki. Yawaitar amfani da wayar hannu wajen yin hada-hadar banki a Nijeriya ya sa mutane da dama ke tura kuɗi cikin sauƙi. A shekarar 2024 kaɗai, rahoton Hukumar Biyan Hada-hadar Banki ta Ƙasa (NIBSS) ya nuna cewa darajar kudin da aka tura...
Miyetti Allah ta roki Gwamntin Kwara da ta sa baki kan rufe Kasuwar Kara da Shugaban Karamar Hukuma Ya Yi
An bukaci gwamnatin jihar Kwara da ta gaggauta shiga tsakani kan rufe kasuwar Kara da ke yankin Kwara ta Kudu da shugaban karamar hukumar ya yi domin ceto harkokin kasuwanci daga durkushewa. Shugaban kungiyar Miyetti Allah reshen jihar Kwara, Alhaji Shehu Garba ne ya yi wannan roko a wata sanarwa da ya rabawa manema...
Shugaban kungiyar goyon bayan Sanata Marafa, Alhaji Surajo Garba Maikatako, ya ce ficewar Sanata Kabir Garba Marafa daga jam’iyyar APC ya kara karfafa masa siyasa tare da jaddada goyon bayansa ga magoya bayansa. A wata sanarwa mai dauke da sa hannun sa da kan sa, Alhaji Maikatako ya bayyana cewa Sanata Marafa ya yanke...
Jakadan Iran A Majalisar Dinkin Duniya Ya Ce: Kwamitin Sulhu Ya Rasa Damar Tattaunawa Da Fahimtar Juna
Jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa: Kwamitin sulhun Majalisar ya rasa damar tattaunawa da fahimtar juna a yau Jakadan kasar Iran kuma wakilin din-din-din a Majalisar Dinkin Duniya Amir Sa’ed Irawani, ya yi tsokaci kan rashin amincewa da daftarin kudiri na ci gaba da dage takunkumin da aka kakabawa Iran a taron...
Daga baya an ƙara nata wani nauyin kula da Tashoshin Warri, Koko, Burutu da kuma ta Sapele, waɗanda kamfanonin ƴ an kasuwa masu zaman kansu ne, ke tafiyar da su, amma har zuwa yau, mahukunta a NPA ne, ke tafiyar da duk wata ragamar hukumar baki ɗaya. A shekaru da dama da suka gabata, matsaloli...
Kamfanin Kasar Sin Ya Bayar Da Gudunmuwar Kayayyaki Ga Wadanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Sudan Ta Kudu
Kamfanin man fetur na kasar Sin (CNPC), ya mika wasu kayayyakin agaji ga dubban mutanen da ambaliya ta raba da matsugunansu a jihar Unity mai arzikin man fetur dake arewacin kasar Sudan ta Kudu. Daraktan sashen hulda da jama’a na reshen kamfanin CNPC a Afrika Ren Yongsheng, ya ce gudunmuwar ta kunshi tantuna, da barguna,...
1- Musayar yawu ta hanyar sumbatar juna- Ma’ana, ta hanyar sumbatar juna a tsakanin ma’aurata, idan guda daga cikinsu na ɗauke da cutar, nan da nan ɗayan shi ma zai kamu da cutar. 2- Gaurayewar jini ko haɗuwar jini- Haɗuwar jini, misali; idan wani ya yi amfani da reza ya yanke, ɗayan ya yi amfani...
Rundunar ’yan sandan Jihar Yobe, ta ƙaryata rahotannin da ke nuna cewar an kai hari sakatariyar ƙungiyar ’yan jarida ta Najeriya (NUJ) da ke Damaturu. Wannan na cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar a ranar Juma’a. An cafke mutum 6 kan tono gawa a kabari don yin asiri a Gombe Wata mata ta ƙona...
Albarkacin bikin murnar cika shekaru 100 na kafuwar Jam’iyyar Zhigong ta Sin, shugaban kwamitin kolin Jam’iyyar Kwaminis ta Sin, JKS, kana shugaban kasar Xi Jinping ya aika wasikar taya murna, kuma a madadin kwamitin tsakiyar JKS, ya taya dukkan ’yan Jam’iyyar Zhigong murna tare da nuna musu gaisuwa. Xi Jinping ya jaddada cewa, a kan...
Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ta ce akalla mutane 1,666 mazauna jihar Legas sun rasa ransu ta hanyoyin da ba su dace ba, ciki har da kashe kansu, tsakanin farkon 2020 zuwa karshen 2024. Wannan bayani ya fito ne daga bakin likitan binciken gawarwaki na rundunar, ACP Samuel Keshinro, yayin gabatar da rahoton bincike kan kisan...
A cewar ma’aikatar, dakatarwar ta na nufin samar da damar ci gaba da tattaunawa da duk masu ruwa da tsaki da kuma yin cikakkiyar bitar tsarin harajin da tasirinsa na dogon lokaci ga tattalin arziki. A watan Afrilu 2025, Kwaturola Janar na Kwastom, Adeniyi, ya bayyana shirin sake gabatar da harajin kashi 4 bayan tattaunawa...
A cewarsa, jihar ta ba da fifiko wajen samar da kudade, kayayyakin more rayuwa, da kuma samun damar koyo tun bayan hawansa kujerar mulki. Gwamnan ya kara da cewa, yadda gwamnatinsa ta mayar da hankali kan ilimin ’ya’ya mata, bayar da tallafin karatu, da rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta, ya taimaka...
Rahotannin cibiyoyin kididdiga a HKI sun ambaci cewa, ana ci gaba da samun yin hijirar yahudwa zuwa waje wanda shi ne mafi girma a cikin shekaru da dama. Jaridar “Ma’ariv” ta amabto wani makwararre a fagen kididdiga yana cewa; Shekarar 2024 ta fuskanci ficewar mutane masu yawan gaske daga “Isra’ila” saboda yakin da ake yi...
Rundunar ’yan sandan Jihar Neja ta kama wasu mutane tara da ake zargi da shirin yin garkuwa da kansu tare da neman kuɗin fansa Naira miliyan 7. Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, Wasiu Abiodun ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, inda ya ce waɗanda ake zargin na da hannu...
Tun a ranar 7 ga watan Satumba, 2025, wani mutum mai suna Hussaini Manager ya kai rahoto ofishin ’yansanda na Kafin Hausa cewa an sace masa mota ƙirar Golf mai launin shuɗi mai lambar MGA 108 JG a Agura Motor Park, Kafin Hausa. Bincike ya gano cewa ɗaya daga cikin mutanen na yin sojan gona...
Wani jariri ya rasu a bayan mahaifiyarsa lokacin da take kokarin tserewa daga harin ’yan bindiga a ƙauyen Allawa da ke ƙaramar hukumar Shiroro ta Jihar Neja. Hakkin ya fito ne daga bakin Hakimin Bassa, Bagudu Amos, yayin wani taron tattaunawa da mata kan rikici da zaman lafiya mai taken: “Ƙarfafa Matakan Kare Fyade da...
A lokacin dokar ta-ɓaci, Tinubu ya naɗa tsohon Hafsan sojin ruwa, Vice Admiral Ibok-Ete Ibas (mai ritaya), a matsayin wanda zai yi mulki na rikon ƙwarya. A jawabin bankwana da ya yi da safiyar ranar Alhamis, Ibas ya roƙi ’yan siyasa a jihar su ci gaba da kiyaye zaman lafiya da haɗin kai da gwamnatinsa...
Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Zamanin kebe kai ya ƙare, Haɗin gwiwar Iran da Rasha ya cimma abin koyi mai nasara A yayin ganawarsa da ministan makamashin kasar Rasha Sergei Tyswell da tawagarsa, shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa: Nasarar da aka samu na hadin gwiwa tsakanin kasashe masu cin gashin kai...
Wani makami mai linzami na Yemen ya tilastawa jirgin saman fira ministan gwamnatin Isra’ila saukar gaggawa Kafofin yada labaran yahudawan swahayoniyya sun watsa rahoton cewa, an tilastawa jirgin saman Fira ministan gwamnatin mamayar Isra’ila Benjamin Netanyahu yin saukar gaggawa a lokacin da ake atisayen soja bayan harba makami mai linzami daga kasar Yemen zuwa yankunan...
A lokacin dokar ta-ɓaci, Tinubu ya naɗa tsohon Hafsan sojin ruwa, Vice Admiral Ibok-Ete Ibas (mai ritaya), a matsayin wanda zai yi mulki na rikon ƙwarya. A jawabin bankwana da ya yi da safiyar ranar Alhamis, Ibas ya roƙi ’yan siyasa a jihar su ci gaba da kiyaye zaman lafiya da haɗin kai da gwamnatinsa...
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana matukar alhininsa kan asarar rayuka da aka yi a gobarar da ta tashi a ranar Talata a Afriland Towers da ke Broad Street, a Legas. A cikin wata sanarwa da mai baiwa shugaban kasa shawara kan yada labarai, Bayo Onanuga ya fitar, ya ce shugaba Tinubu ya...
Ya jaddada cewa dakarun tsaron Nijeriya suna da ƙarfin da za su iya fatattakar ’yan ta’adda, amma abin da ya rage shi ne samun ingantaccen shugabanci da ƙwarin gwiwa daga fadar shugaban ƙasa. Atiku ya yi kira ga ’yan Nijeriya da su haɗa kai domin ceto ƙasar nan, inda ya bayyana cewa dawo da zaman...
Gwamnatin Jihar Zamfara ta roki Hukumar Raya Kasashen Waje ta Kasa (FCDO), Premier Urgence Internationale (PUI), da sauran masu ruwa da tsaki da su kara tallafa wa ‘yan gudun hijirar da ke jihar. Kwamishinan Bada Agaji na Jiha Alhaji Salisu Musa Tsafe ne ya yi wannan kiran a lokacin da yake jawabi ga mahalarta...