Majalisar Dattawa Ta Bawa Tunubu Damar Kai Sojoji Zuwa Kasar Benin
Published: 10th, December 2025 GMT
Majalisar dattawan Najeriya ta amince da bukatar shugaba Bola Ahmed Tinubu na aika sojoji zuwa kasar Benin saboda tabbatar da zaman lafiya a kasar bayan yunkurin juyin mulki wanda wasu sojoji suka yi a cikin yan kwanakin da suka gabata.
Jaridar Premium times ta Najeriya ta bayyana cewa shugaban majalisar dattawan Sanata Godwill Alpabio ne ya karanta bukatar shugaban a gaban majalisar ya kuma sami amincewarsu da baka ba tare da an kada kuri’a ba.
Kafin haka dai shugaban Tinubu ya rika ya aika sojojin sama zuwa kasar ta Benin wacce take makobtaka da Najeriya daga yamma cin kasar, sai dai saboda cika bukatar kundin tsarin mulkin kasar na bukatar samun amincewar Majalisar shugaban ya rubuta mata yana neman amincewarta.
Kafin haka dai shugaban kasar Benin ya bukaci taimakon gwamnatin Najeriya a dai-dai lokacinda sojojin suka kwace wata gidan talabijin suna bada sanarwan cewa sun kwace mulki.
Bayan an murkushe juyin mulkin an kuba shelanta neman shugaban juyin mulkin Tigri Pascal a matsayin mutum wanda ake nema a duk inda yake.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label Name* Email* Website Label Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Ministan Makamashi: Iran Tana Da Sanayya Ta Ilimi Na Samar Da Hadari Domin Yin Ruwan Sama December 10, 2025 Kasar China Ta Zartar Da Hukuncin Kisa Akan Wani Babban Jami’in Banki December 10, 2025 Ganawa A Tsakanin Mataimakan Ministocin Waje Na Kasashen Saudiyya, China Da Minista Arakci Na Iran December 10, 2025 Antoni Gutress Ya Yi Allawadai Da Kutsen Da “Isra’ila” Ta Yi A Cibiyar Unrwa December 10, 2025 Iran da Saudiyya sun sake jaddada fadada dangantakarsu December 9, 2025 Faransa ta ce da hannunta aka dakile juyin mulki a Benin December 9, 2025 RSF : Rabin ‘Yan jarida 67 da aka kashe a bana, a Zirin Gaza ne December 9, 2025 An cire Tony Blair daga jerin wadanda zasu jagoranci Gaza December 9, 2025 Isra’ila ta sake kai hare-haren a kudancin Lebanon December 9, 2025 Trump Ya Yi Gefe Da Kasashen Turai Dangane Da Tattaunawa Kan Rikicin Ukraine December 9, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Juyin mulki: An kama sojojin da suka yi yunƙurin kwace mulki a Benin
Aƙalla sojoji 13 aka cafke a ƙasar Benin bayan yunƙurin da juyin mulki da suka yi bai yi nasara ba.
Majiyoyin tsaro da na soja sun bayyana cewa dukkan waɗanda aka kama sojoji ne masu aiki a halin yanzu, sai mutum ɗaya da ya taɓa yin aiki a rundunar amma ya yi ritaya.
Kama su ta biyo bayan sanarwar da aka yi a talabijin na ƙasar da safiyar Lahadi, inda sojojin suka bayyana cewa sun kifar da gwamnatin Shugaba Patrice Talon tare da rushe dukkan cibiyoyin gwamnati.
Jami’an da suka kira kansu Kwamitin Soja na Sake Tsarawa, sun ce sun karɓe mulki, sun rufe iyakokin ƙasar tare da dakatar da jam’iyyun siyasa.
Sai dai fadar shugaban ƙasa ta tabbatar da cewa Shugaba Talon yana cikin ƙoshin lafiya, kuma dakarun da suka tsaya kan gaskiya na dawo da doka da oda.
Gwamnati ta bayyana lamarin a matsayin aikin “tsiraru mutane” da ba su da tasiri.
“Wasu ’yan tsiraru ne kawai da ya mamaye talabijin. Rundunar sojan ƙasa na sake karɓar iko. Birnin da ƙasar gaba ɗaya suna cikin tsaro,” in ji sanarwar fadar shugaban ƙasa.