Gwamnatin Jigawa Ta Amince da Sama da Naira Biliyan 2.6 Domin Aikin Hajjin 2026
Published: 13th, December 2025 GMT
Daga Usman Muhammad Zaria
Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira biliyan 2.6 domin gudanar da ayyukan Hajjin shekarar 2026.
Kwamishinan Yada Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed ne ya bayyana hakan jim kadan bayan kammala taron Majalisar Zartarwa ta Jiha da aka gudanar a gidan gwamnati da ke Dutse, babban birnin jihar.
A cewarsa, majalisar ta amince da kashe sama da naira biliyan 2 da miliyan 651 domin ayyukan Hajjin 2026, biyo bayan gabatar da bukatar da Sakataren Gwamnatin Jihar (SSG) ya yi.
Alhaji Sagir Musa Ahmed ya ce za a yi amfani da kudaden ne a bangarorin sufuri da jijigilaAlhazai, jin dadinsu, ayyukan lafiya da kuma shirye-shiryen gudanarwa.
Sauran bangarorin sun hada da duk wasu muhimman abubuwa da za su tabbatar da ingantaccen tsari da nasarar aikin Hajji ga Alhazan jihar Jigawa.
Kwamishinan ya kara da cewa, majalisar ta kuma amince da kashe sama da Naira Biliyan 1 da Miliyan 300 domin tallafin karatu (bursary) ga dalibai 19,716 da aka tantance kwanan nan.
Ya bayyana cewa daga cikin adadin, akwai dalibai maza 12,638, da mata 7,088 da ke karatu a manyan makarantu 77.
Ya ce wannan tallafi zai taimaka wajen bunkasa harkar ilimi, rage nauyin kudi a kan iyaye da iyalai, tare da karfafa gwiwar dalibai su yi fice a karatunsu.
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jigawa
এছাড়াও পড়ুন:
Mahajjata 2,235 Ne Suka Yi Rijistar Aikin Hajjin 2026 A Sokoto
A cewar Musa, shirye-shiryen sun hada da jigilar kayayyakin tafiya, masaukai da kammala yarjejeniyar ciyarwa da hukumomin da suka dace a Kasar ta Saudiyya.
A cewarsa, adadin mahajjatan da suka yi rajistar ya hada har da jami’an gwamnati.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA