Juyin mulki, wani lamari ne da ya zama abun mamaki a shekarun baya amma a ‘yan shekarun nan, a iya cewa, ba abun mamaki ba ne domin ya zama tamkar ruwan dare musamman a Nahiyar Afirka. Masoynmu masu bibiyarmu, me zai hana, mu tambayi kanmu, shin me ake nufi da juyin mulki kuma me ke kawo shi? Juyin mulki, shi ne ƙwace gwamnatin ƙasa ba zato ba tsammani kuma ba bisa ƙa’ida ba, wanda yawanci sojoji ko ƙungiya mai ƙarfi ke yi, ta hanyar amfani da ƙarfi ko barazana domin cire zaɓaɓɓun shugabanni.
A wannan makon, alƙalaminmu zai karkata ne kan sharhi ga wannan muhimmin abu da ke barazana ga wanzuwar dimokuraɗiyya a yankin Afirka, duk da cewa, akwai dalilai masu ƙarfi da ke janyo a yi juyin mulki a ƙasa. Ga bayani a sarari kuma a taƙaice game da manyan dalilan da ake kyautata zaton su suke haifar da juyin mulkin da ake yi kwanan nan a Afirka, musamman daga ƙarshen shekarun 2020 zuwa 2025. Duk da cewa, kowacce ƙasa da na ta irin sanadin, kamar a ƙasashe irin Mali, Burkina Faso, Guinea, Nijar, Gabon, Chad, da Sudan da suka fada hannun mulkin sojoji a ‘yan shekarun da suka gabata. Babban dalilin juyin mulki, bai gaza rashin Shugabanci na gari da cin hanci da rashawa. Gwamnatoci da yawa a ƙasashen da abin ya shafa suna fama da cin hanci da rashawa, rashin kula da ababen more rayuwar jama’a, rashin samar da wutar lantarki, ayyukan yi, ilimi, da kiwon lafiya na gari. Wannan yana raunana amincewar mutane ga gwamnatocin farar hula kuma yana haifar da gurɓacewar mulkin dimokuraɗiyya wanda hakan ke bai wa sojoji uzurin karɓar mulki cikin sauƙi. Wasu daga cikin dalilan sun haɗa da rashin tsaro da yawaitar tashe-tashen hankula. Ƙasashen Sahel, kamar Mali, Burkina Faso, Nijar – sun fuskanci hare-haren ta’addanci daga ƙungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi (IS, Al-Qaeda, JANIM), wanda hakan ya haifar da zargin cewa, jami’an tsaron ƙasa sun gaza. A duk lokacin da gwamnatoci suka gaza kare ‘yan ƙasa, sojoji sukan amfani da wannan dama wajen ƙwace mulki da nufin “dawo da tsaro.” Wasu shugabanni, sukan yi yunƙurin yin kwaskwarima ga kundin tsarin mulki don sauya kujerar dimokuraɗiyya ta zama ta dindindin, kuma su yi riƙa tafka maguɗi a yayin zaɓe, kamar Guinea (2021) da Gabon (2023). Wannan sau da yawa ya kan fusata jama’a sai hakan ya zama wani uzuri ga sojoji wajen hamɓarar da gwamnatin. Har ila yau, wasu jama’a saboda fusata da salon mulkin dimokuraɗiyya a ƙasarsu, suna ganin sojoji a matsayin masu ceto, sun yi imanin cewa, sojoji za su kawo musu kwanciyar hankali. Wannan amincewar ta jama’a, yana sa juyin mulki ya yi nasara cikin sauƙi.
Jerin juyin mulki da aka yi cikin nasara a Afirka. 1 – Sojojin Mali a 2020 sun tsige Shugaba Ibrahim Boubacar Keïta saboda rashin tsaro da zanga-zanga. 2 – Sojojin Chad a 2021 sun karɓi mulki a ƙarƙashin ɗan Shugaba Idriss Déby, bayan mutuwar sa. 3 – Sojojin Guinea a 2021 sun tsige Alpha Condé a 2021 bayan yunƙurin tsawaita mulkinsa. 4 – Sojojin Sudan sun rushe gwamnatin raba iko a 2021 5 – Sojojin Burkina Faso a 2022 sun tsige Shugaba Kaboré saboda gazawar dakatar da rashin tsaro. A juyin mulki na biyu kuma, wata tawagar sojoji ta hambarar da Laftanar Kanar Damiba duk a wannan shekara. 6 – Sojojin Nijar a 2023 sun hamɓarar da gwamnatin Bazoum. 7 – Sojojin Gabon a 2023 sun hamɓarar da gwamnatin Ali Bongo. 8 – Sojojin Guinea-Bissau a watan Nuwamban 2025, sun hamɓarar da gwamnatin Umar Sissoco Embalò. Akwai jerin juyin mulki da aka yi yunƙurin aiwatarwa amma bai yi nasara ba da dama duk a nahiyar ta Afirka. ADVERTISEMENT ShareTweetSendShare MASU ALAKA

Manyan Labarai Abubuwan Da Ba Ku Ji Ba Kan Rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi December 13, 2025

Manyan Labarai Shugaba Tinubu Ya Karrama Shugaban NPA Da Lambar Yabo Ta Musamman December 13, 2025

Manyan Labarai Dantsoho Ya Yaba Wa Ƙoƙarin Oyetola Na Dawo Da Nijeriya Tsarin Sufurin Jiragen Ruwa Na Duniya December 13, 2025
উৎস: Leadership News Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
NLC Ta Shirya Zanga-Zangar Rashin Tsaro A Faɗin Ƙasa Ranar 17 Ga Disamba
Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC) ta bayyana cewa za ta gudanar da zanga-zangar ƙasa baki ɗaya a ranar 17 ga Disamba, 2025, domin nuna damuwarta kan taɓarɓarewar tsaro a Nijeriya. Wannan sanarwa ta fito ne daga saƙon da NLC ta aikawa dukkanin majalisun jihohi a ranar 10 ga Disamba, bayan taron NEC da ta gudanar a ranar 4 ga watan. Kungiyar ta nuna baƙin ciki kan ƙaruwar hare-haren ƴan daba da satar mutane da ke ci gaba da addabar al’umma.
NLC ta mayar da hankali musamman kan sace ɗalibai mata a wata makarantar kwana da ke Jihar Kebbi a ranar 17 ga Nuwamba, inda ta bayyana mamaki cewa an janye jami’an tsaro daga makarantar kafin harin. Ta ce wannan lamari ne mummunan kuma abin takaici da ya kamata a bincike shi sosai tare da gurfanar da duk masu hannu a ciki. Ƙungiyar ta zargi gwamnati da gaza ɗaukar matakan da suka dace wajen kare rayukan ɗalibai a makarantu.
Gwamnonin Arewa Sun Yi Rawar Gani A Kafa Gidauniyar Fuskantar Matsalar Tsaro Tinubu Na Ɗaukar Ƙwararan Matakai Don Magance Matsalar Tsaro A Nijeriya – Shettima
Sanarwar ta ƙara da cewa an umarci dukkan rassan NLC da ƙungiyoyin ƙwadago da su “shirya cikakke” domin zanga-zangar. Ƙungiyar ta bayyana cewa yawaitar sace yara a makarantu ya kai wani mawuyacin matsayi da ba za a amince da shi ba. Ta jaddada cewa gwamnati na da nauyin kare makarantu, musamman waɗanda suke a karkara ko yankunan da ke fama da hare-hare.
ADVERTISEMENT
NLC ta ce dole ne gwamnati ta ɗauki mataki cikin gaggawa ta kammala bincike game da janye jami’an tsaro daga makarantar da aka kai harin, tare da ladabtar da masu laifi. A cewarta, rashin tsaron da ake fuskanta ya zama barazana ga rayuwa, da ilimi da ci gaban ƙasa. Saboda haka NEC ta umarci dukkan ƙungiyoyi da majalisun jihohi su fita ƙwansu da ƙwarƙwatarsu wajen zanga-zangar ranar 17 ga Disamba domin nuna rashin gamsuwarsu da yadda gwamnati ke tafiyar da batun tsaro.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Yadda APC Da ADC Ke Amfana Da Rikicin Jam’iyyar PDP December 12,
2025 
Manyan Labarai Farashin Kayan Abinci Na Sauka Yayin Da Bikin Kirsimeti Da Sabuwar Shekara Ke Matsowa December 12, 2025

Manyan Labarai Ƴan Bindigar Daji: Jihohin Arewa 7 Sun Kaddamar Da Rundunar Fatattakar Su December 12, 2025