HausaTv:
2025-12-14@21:19:36 GMT

Iran Tayi Tir Da Hare-Haren Sydney Na Kasar Austaralia

Published: 14th, December 2025 GMT

Gwamnatin kasar Iran ta yi allawadai da hare-haren ta’addancin da aka kai a birnin Sydney na kasar Australia. Ta kuma kara da cewa, ayyukan ta’addanci abin ki ne a ko ina ya auku a duniya.

Tashar talabijan ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta nakalto kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Esma’ila Baghaei yana fadar haka a yau Lahadi ya kuma kara da cewa ayyukan ta’addanci da kuma tashe-tashen hankali ba abin amincewa ne ba a duk inda suka auku a duniya.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen ya bayyana haka ne a shafinsa na X a yau Lahadi ya kuma kammala da cewa yana isar da sakon ta’aziyya da iyalan wadanda suka rasa rayukansu a wannan aikin ta’addancin da kuma fatan saurin warkewa ga wadanda suka ji raunin.

Jami’an tsaro a kasar Australia sun bada sanarwan kashe mutane 11 da kuma raunata wasu 16 a wani taron yawon shakatawa a bakin ruwa a birnin Sydney a yau Lahadi.

Labarin ya kara da cewa jami’an tsaro a kasar ta Australia sun bada sanarwan fara wani aikin bincike mai fadi don gano wadanda suka kai hare-hare a wurin shakatawa na Buwandi dake bakin ruwa a birnin Sydney. Sannan wani bangare daga cikinsu na kokarin kwance wata nakiya da aka dana a cikin wata mota na daya daga cikin yan ta’addan da suka bu wuta a kan masu yakin shakatawa a safiyar yau Lahadi.

Sannan kafafen yada labarai na HKI sun bada sanarwan cewa yan ta’addan sun kai hari ne kan wata jama’ar Yahudawa wadanda suke bukukuwan Khonuka na yahudawa. Kuma Babban malamin yahuduwa a kasar Australia Khakham Ili Shalingar yana daga cikin wadanda aka kashe.

Labarin ya ce mutane biyune suka kai hare-haren kuma kashe akalla mutane 11 ya zuwa yanzu.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Sudan: Makaman ‘Drones’ Sun Kashe Ma’aikatan MDD 6 A Kadugli Na Kurdufan Ta Kudu December 14, 2025 Eritrea Ta Fice Daga Kungiyar Raya Kasahsen Gabacin Afrika (IGAD) December 14, 2025 َA Yau Ne Za’a Gudanar Da Taron Koli Na Kungiyar ECOWAS A Birnin Abuja December 14, 2025 Iran Ta karbi Bakunci Taron Kasashen Dake Makwabtaka Da Afghanistan Da Rasha December 14, 2025 Isra’ilaTa Kashe Wani Bafalasdine Matashi A Wani Hari Da Takai A Arewacin Kogin Jodan. December 14, 2025 Shuwagabannin Majalisar Kasar Iran Da Na Ethiopia Sun Gudanar Da Taron Manema Labarai December 14, 2025 Ghana Ta Kori Wasu Yahudawa Guda 3 Don Mayar Da Martani December 14, 2025 Araghchi ya bukaci Amurka ta girmama al’ummar Iran da gwamnatinta December 14, 2025 Dan bindiga ya kashe sojojin Amurka biyu da wani farar hula a Siriya December 14, 2025 Mutum biyu sun mutu a harbin bindiga a Jami’ar Brown ta Amurka December 14, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Kalibaf:  Iran Da Habasha Suna Bunkasa Alakokin Siyasa Da Tattalin Arziki

Shugaban Majalisar Shawarar musulunci ta Iran Muhammad Bakir Kalibaf wanda ya gana da takwaransa na kasar Habasha Tagseh Chapo ya bayyana cewa: Kasashen biyu da suke da alakar diplomasiyya ta tsawon shekaru 70, sun Shata hanyoyin bunkasa alakokin tattalin arziki, siyasa da al’adu.

Haka nan kuma ya ce; kasantuwar kasashen biyu mambobi a cikin kungiyar Bricks yana kara dankon alakar da take tsakaninsu.

Shugaban Majalisar shawarar musuluncin ta Iran Muhammad Bakir Kalibaf, ya kuma ce; A shekarar da ta gabata na kai ziyarar aiki zuwa Addib Ababa,mun gana da Mr. Tagseh Chapo, inda na gayyace shi ya kawo Ziyara Iran, kuma an yi wannan ziyarar ce dai a lokacin da kasashen biyu suke mambobi na kungiyar Bricks.

Haka nan kuma shugaban Majalisar Shawarar musuluncin ta Iran ya ce; Habasha Babbar kasa ce a cikin nahiyar Afirka, musamman ta fuskar yawan jama’a, kuma ta yi tarayya da kasashen musulmi akan al’adu masu, musamman ma Iran.

Bugu da kari Kalibaf ya ce, alakar kasashen biyu ta fuskokin siyasa da tattalin arziki ta kai tsawon shekaru 70, kuma an Shata manufafofin da ake son cimmawa a wadannan fagagen.

A nashi gefen, shugaban majalisar dokokin kasar Habasha ya ce; Alakar kasashen biyu ta kai shekaru 70, kuma shekaru 60 da su ka gabata, sarkin kasarmu ya kawo Ziyara Iran,a wannan lokacin kuma tawaga mai girma daga Habashan ta sake zuwa Ziyara Iran.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan(a) 171 December 13, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan(a) 170 December 13, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan(a) 169 December 13, 2025 Isra’ila Ta Kai Hari A Kudancin Labanon  A Ci Gaba Da Keta Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta December 13, 2025 Ziyarar Da Shugaban Rasha Ya Kai Indiya Ta Kara Karfafa Dangantakar Mosko Da Delhi December 13, 2025 Amurka Ta Sanya Sabbin Takunkumi A Bangaren Manfetur Na  Venuzuela December 13, 2025 Hamas Ta Ce Ci Gaba Da Kai Hare-Haren Isra’ila Ya Nuna Gazawar Tsarin Duniya Na Dakatar Da Ita. December 13, 2025 Matatar Mai ta Dangote Ta Rage Farashin Man Fetur Zuwa Naira 699 December 13, 2025 Iran da Rasha sun jaddada aiwatar da yarjejeniyar hadin gwiwa a tsakaninsu December 13, 2025 Ali Nuhu, ya yaba wa Iran kan haskaka Musulinci ta hanyar fina-finai December 13, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Iran Ta Bukaci Mutanen Yemen Su Daina Kashe Juna
  • Shuwagabannin Majalisar Kasar Iran Da Na Ethiopia Sun Gudanar Da Taron Manema Labarai
  • Kalibaf:  Iran Da Habasha Suna Bunkasa Alakokin Siyasa Da Tattalin Arziki
  • Hamas Ta Ce Ci Gaba Da Kai Hare-Haren Isra’ila Ya Nuna Gazawar Tsarin Duniya Na Dakatar Da Ita.
  • Iran Ta soki Kasashe Masu Karfi Na Bawa Isra’ila Dama Ta Musamman Wajen Kai Hare-hare
  • Shuwagabannin Kasashen Iran Da Iraqi Sun Tattauna A Wajen Taron Zaman Lafiya A Kasar Turkmanistan
  • Iran Zata Dauki Bakoncin Taro Dangane Da Kasar Afganistan Da Tsaron Yankin
  • Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Amince Ya Ziyarci Beirut
  • Za A Yi Manyan Zabuka A Kasar Habasha A Watan Yuni Na 2026