Taɓarɓarewar rashin tsaro ya nuna rashin shugabanci na gari — Obi
Published: 14th, December 2025 GMT
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP, Peter Obi, ya ce taɓarɓarewar rashin tsaro a Najeriya na nuna gazawar shugabanci.
Ya yi kira da a gudanar da bincike mai zurfi cikin gaggawa kan zargin wasu jami’an gwamnati da taimaka wa ’yan ta’adda.
Buɗe cibiyar horas da sabbin sojoji a Kudu zai taimaka — Janar Shaibu Shirin kafa ‘Hisbar Ganduje’ ya tayar da ƙura a KanoObi, ya bayyana hakan ne bayan wani bidiyo da aka yaɗa a kafafen sada zumunta, inda wasu da ake zargin ’yan ta’adda ne suka ce jami’an gwamnati ne ke taimaka musu da makamai.
Ya ce wannan zargi abu ne mai matuƙar muhimmanci da bai kamata a yi watsi da shi ba.
“An ga wani bidiyo mai tayar da hankali a Jihar Kwara inda waɗanda aka kama suka ce jami’an gwamnati ne suka ba su harsasai da kayan aiki.
“Wannan zargi na buƙatar bincike cikin gaggawa kuma a bayyane.”
Obi ya ce duk da maƙudan kuɗaɗen da aka kashe a fannin tsaro tsawon shekaru, rashin tsaro na ƙara taɓarɓarewa a ƙasar.
“An kashe tiriliyoyin juɗi da biliyoyin daloli a fannin tsaro, amma duk da haka rashin tsaro na ƙara taɓarɓarewa a faɗin ƙasar nan.”
Ya kuma tambayi dalilin da ya sa ba a amfani da na’urorin zamani da fasahar tsaro wajen gano da kama ’yan ta’adda, duk da cewa ƙasar na da irin waɗannan damarmaki.
“Gwamnati na da iko da hanyoyin sadarwa, bayanan sirri da bin sahun kuɗaɗe, amma duk da haka satar mutane da ta’addanci na ci gaba da ƙaruwa.”
Obi ya kuma soki yadda ake murnar sakin waɗanda aka sace ba tare da kama waɗanda suka aikata laifin ba, inda ya ce hakan na nuna rashin ɗaukar al’amarin da muhimmanci.
A ƙarshe, ya yi gargaɗin cewa ƙaruwar rashin tsaro na nuni da gazawar gwamnati da kuma yin sakaci, inda ya jaddada cewa babban aikin kowace gwamnati ne kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Gazawa Rashin Tsaro Tsaro rashin tsaro
এছাড়াও পড়ুন:
DRC: Kungiyar M23 Ta Kwace Iko Da Wani Gari Mai Muhimmanci
Kungiyar ‘yan tawayen kasar DRC ta M23 ta kwace iko da wani gari mai muhimmanci bayan rushewar batun zaman lafiya
A jiya Juma’a ne dai kasar Amurka ta zargi kasar Rwanda da cewa ta keta yarjejeniyar sulhu da zaman lafita da ta kulla da DRC, tare da cewa, abinda Kigalin take yi shi ne jefa yankin zuwa yaki.
Mako daya da ya gabata ne dai aka kulla yarjejeniyar sulhu a tsakanin kasashen biyu wacce shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bayyana cewa; Ta tarihi ce.” Tare da nuna fatan ganin an sami zaman lafiya a cikin wannan yankin wanda ya dade cikin fadace-fadace.
Sai dai a ranar Larabar da ta gabata da yamma mayakan kungiyar M23 wacce Rwanda take goyawa baya sun sanar da kama garin Uvira wanda daya daga cikin muhimman wuraren da suke a hannun sojojin gwamnatin kasar a gabashin kasar.
Dama dai tun a baya wasu kwararru na MDD sun zargi Kigali da cewa, ita ce mai iko da akan dukkanin hare-haren da ‘yan tawayen suke kai wa a gabashin DRC.
Jakadan Amurka a MDD Mike Waltz ya ce; Amurka ba ta ji dadin abinda ya faru ba ko kadan, domin ya rusa yarjejeniyar zaman lafiyar da aka kulla.
Su dai ‘yan tawayen ba su cikin yarjejeniyar zaman lafiyar da aka kulla da Amurka kai tsaye, amma da suna cikin tattaunawar da ake yi da kasar Qatar.
Amurka dai ta shiga cikin Shirin zaman lafiya a cikin DRC, domin ta sami damar dibar ma’adanai da Allah ya huwacewa wannan kasar.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Syria: Sojojin “Isra’ila” Sun Kutsa Cikin Yankin Qunaidhara December 13, 2025 Kalibaf: Iran Da Habasha Suna Bunkasa Alakokin Siyasa Da Tattalin Arziki December 13, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan(a) 171 December 13, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan(a) 170 December 13, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan(a) 169 December 13, 2025 Isra’ila Ta Kai Hari A Kudancin Labanon A Ci Gaba Da Keta Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta December 13, 2025 Ziyarar Da Shugaban Rasha Ya Kai Indiya Ta Kara Karfafa Dangantakar Mosko Da Delhi December 13, 2025 Amurka Ta Sanya Sabbin Takunkumi A Bangaren Manfetur Na Venuzuela December 13, 2025 Hamas Ta Ce Ci Gaba Da Kai Hare-Haren Isra’ila Ya Nuna Gazawar Tsarin Duniya Na Dakatar Da Ita. December 13, 2025 Matatar Mai ta Dangote Ta Rage Farashin Man Fetur Zuwa Naira 699 December 13, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci