NAJERIYA A YAU: Alfanu Da Kalubalen Sabon Jadawalin Karatun Makarantu Da Gwamnati Ta Bijiro Dashi
Published: 11th, December 2025 GMT
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
A kwanakin baya, Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da sabon tsarin jadawalin karatu ga makarantun firamare da sakandare. Sabon tsarin, wanda Ma’aikatar Ilimi ta ƙasa ta tsara, yana da nufin inganta koyarwa da koyo, da rage nauyin lodi ga dalibai, da kuma tabbatar da cewa malamai suna da isasshen lokaci don isar da darussa tare da kwarewa.
Tsarin ya mayar da hankali kan daidaita ranakun makaranta, da tsara lokutan darussa bisa bukatun shekaru da matakin karatu, da kuma kara aiki a kan basira, da kirkire-kirkire, da koyon sana’o’i, domin shirya dalibai su zama masu amfani a harkokin tattalin arziki tun daga matakin makaranta.
NAJERIYA A YAU: Yadda Abincin Da Mutane Ke Ci Ke Zamewa Guba DAGA LARABA: Ko Ziyarar Tawagar Amurka Za Ta Kawo Karshen Matsalar Tsaro A Najeriya?Shin ko wadanne alfanu ko akasin haka wannan canji zai haifar a fannin ilimi a kasar nan?
Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kai.
Domin sauke shirin, latsa nan
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Majalisar Dattawa ta amince Tinubu ya tura sojojin Najeriya zuwa Jamhuriyar Benin
Majalisar Dattawa a ranar Talata ta amince da bukatar Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta tura sojojin Najeriya zuwa Jamhuriyar Benin domin tabbatar da dimokuradiyya a kasar.
Majalisar ta kuma ce tana goyon bayan matakin da shugaban ya ɗauka kwanaki kafin haka domin hana yunƙurin kifar da tsarin dimokuraɗiyya a makwabciyar kasar.
Gwamnan Jihar Ribas ya sauya sheka zuwa APC Juyin Mulki: ECOWAS ta ayyana dokar ta-baci a kasashentaBukatar dai na kunshe ne a cikin wata wasiƙa da Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio, ya karanta a zauren majalisa yayin zamanta.
Tinubu ya umarci tura sojojin makon da ya gabata domin dakile yunƙurin karɓar mulki ba bisa ka’ida ba a Jamhuriyar Benin da kuma kaucewa rikicewar tsaro a yankin yammacin Afirka.
Sai dai Tinubu bai nemi amincewar majalisa ba kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.
Bayan karanta wasiƙar, majalisar ta koma zaman kwamiti domin tantance bukatar. A yayin zaman, ’yan majalisa sun tattauna kan tasirin tsaro, jin‑ƙai da diflomasiyya da ke tattare da wannan mataki.
Babbar damuwar a cewarsu ta haɗa da yiwuwar kwararar ’yan gudun hijira zuwa Najeriya, tsaron iyaka da kuma tasirin matakin ga zaman lafiya da tsaro a yankin.
Bayan doguwar muhawara, majalisar ta koma zama a zaurenta, inda ta kada kuri’ar amincewa da matakin shugaban ƙasa cikin rinjaye.
Shugaban Majalisar, Akpabio, ya gabatar da rahoton kwamitin domin tabbatarwa, inda ’yan majalisa suka amince ba tare da wata adawa ba kafin su amince da tura sojojin ta hanyar kada kuri’ar murya karo na biyu.
A jawabin sa, Akpabio ya yabawa Shugaba Tinubu bisa ɗaukar matakan da suka tabbatar da zaman lafiya a yankin da kuma bin ka’idojin kundin tsarin mulki ta hanyar neman amincewar majalisa, ko da bayan tura sojojin cikin gaggawa.
“Wannan mataki ne da ya zama dole. Shugaban Ƙasa ya yi aiki ne domin kare tsaron ƙasa da kuma kare dimokuraɗiyya a yammacin Afirka. Barazana ga kasa ɗaya barazana ce ga kowa,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa za a isar da kudurin majalisar ga Shugaban Ƙasa nan take.