2025-12-07@18:21:15 GMT
إجمالي نتائج البحث: 12262
«kasar Labanon»:
An gano gawar wani malamin makarantar Islamiyya kuma mahaifin ’ya’ya bakwai, Malam Awwal Yakubu, a cikin wani kango da ke rukunin gidaje na Talba a birnin Minna, na Jihar Neja. Malam Awwal, yana da makarantar Islamiyya a unguwar Barikin-Saleh, an neme shi sama ko ƙasa tun ranar Alhamis ɗin da ta gabata. ’Yan bindiga sun hallaka mutum 4, sun sace mata 4 a Sakkwato Sojoji sun yi yunkurin juyin mulki a Jamhuriyar Benin An gano gawarsa ne da safiyar ranar Lahadi. Rahotanni sun nuna cewa an ƙone al’aurarsa, sannan an samu kwalin ashana a gefen gawarsa. Shugaban al’ummar yankin, Malam Mahmud Dalhatu Iya, ya shaida wa Aminiya cewa iyalan mamacin sun riga sun gano gawar kuma an riga an binne...
Rahotanni daga Jamhuriyar Benin na cewa am kama wasu 12 bayan yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba da jijjibin safiyar Lahadin nan. Tun da farko dama fadar shugaban kasar ta ce har yanzu Shugaba Patrice Talon ne a kan mulkin. Ministan harkokin cikin gida na Jamhuriyar Benin ya bayyana a gidan talabijin din kasar cewa yunkurin juyin mulkin da wasu tsirarun sojoji suka yi bai yi nasara ba. Wani rukunin sojojin kasar ne karkashin Laftanar Kanar Pascal Tigri ya sanar da hambare Shugaba Patrice Talon tare da dakatar da tsarin mulki a kafar talabijin din. Mr Talon, mai shekaru 67, ana sa ran zai mika mulki a watan Afrilu na shekara mai zuwa bayan shekaru 10 a kan...
Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araghchi ya tabbatar da cewa har yanzu Amurka ba ta nuna sha’awarta ta shiga “tattaunawa mai ma’ana ba,” yana mai sake nanata cewa dole ne Washington ta fara amincewa da ‘yancin Iran na samar da makamashin nukiliya na zaman lafiya a karkashin Yarjejeniyar hana yaduwar Makaman Nukiliya ta (NPT). A wata hira ta musamman da aka yi da kamfanin dillancin labarai na Japan Kyodo a ranar Asabar, ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa an kaiwa cibiyoyin nukiliya na Jamhuriyar Musuluncihari da bama-bamai, wanda ya lalata su sosai” a lokacin harin Isra’ila da Amurka a watan Yuni. Araghchi ya jaddada cewa wadannan hare-haren sun kasance “wataƙila mafi girman keta dokokin kasa da kasa” da aka...
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa Hamas ta bayyana cewa za ta mika makamanta ne kawai ” idan Isra’ila ta kawo karshen mamaya, tana mai jaddada cewa ba za a iya kwance damarar makamai ba a cikin yanayin da ake ciki na zaluncin soja da siyasa. Babban jami’i a ofishin siyasa na Hamas kuma babban mai shiga tsakani na kungiyar, Khalil al-Hayya, ne ya bayyana hakan inda yake cewa idan mamayar ta kare, za a sanya wadannan makaman a karkashin ikon gwamnatin kasar Falasdinu.” Ofishinsa ya fayyace cewa kalmar “ƙasa” tana nufin “ƙasar Falasɗinawa mai zaman kanta” mai cikaken iko. “Har yanzu ana ci gaba da tattaunawa game da kwance makamai tsakanin kungiyoyi daban-daban da masu shiga tsakani, kuma yarjejeniyar tana cikin farkon...
Jamhuriya Musulinci ta Iran, ta bayyana sabbin dabarun tsaron Amurka na cimma maradun gwamnatin Isra’ila ne. Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ya ce sabbin dabarun tsaron Kasa na Amurka (NSS) da ke bayyana ka’idojin Washington da muhimman manufofin harkokin waje a zahiri cimma maradun tsaro ne ga gwamnatin Isra’ila ne. Esmaeil Baghaei ya yi wannan furucin ne a lokacin wani taron manema labarai, kwana biyu bayan gwamnatin Shugaban Amurka Donald Trump ta bayyana sabbin dabarun tsaron na NSS na 2025. A kwanan ne gwamnatin Amurka ta sanar da sabbin dabarun tsaron na ta wanda ya tanadi har da soke bada mafaka ga ‘yan kasashen duniya 19. Kasashe sun suka hada da Chadi, Congo, Equatorial Guinea, Eritrea, Libya, Somalia, Sudan, Burundi,...
Kasar Masar ta sake jaddada cewa ba za ta bari a yi amfani da hanyar shiga iyakar Rafah don korar Falasdinawa daga gidajensu ba, tana mai jaddada bukatar sa ido kan yarjejeniyar tsagaita wuta ta Gaza. Ministan harkokin wajen Masar Badr Abdelatty ya yi wannan furucin ne a wata hira da ya yi da Al Jazeera yau Lahadi, inda ya nuna cewa Alkahira tana tattaunawa da Isra’ila game da yadda hanyar shiga tsakanin Rafah ke aiki, yayin da ya jaddada cewa matsayin Masar kan wannan batu “a bayyane yake kuma tabbatacce.” M. Abdelatty ya kuma fayyace cewa hanyar shiga ta Rafah za ta takaita ne kawai ga saukake isar da kayan agaji da kuma kwashe marasa lafiya masu tsanani. Ya...
’Yan bindiga sun kai sabon hari wasu yankuna na Jihar Sakkwato, inda suka kashe mutane huɗu tare da yin awon gaba da mata huɗu. Wani mazaunin Gatawa, ya shaida wa Aminiya ce harin ya faru ne a daren ranar Asabar, lokacin da ’yan bindiga sama da goma suka shiga garin a kan babura. Mutum 5 sun rasu sanadin gobara da faɗa wa rijiya a Kano Sojoji sun yi yunkurin juyin mulki a Jamhuriyar Benin A cewarsa, “Sun ratsa gefen gari suka dinga shiga gida-gida. Sun harbe mutane huɗu; uku sun mutu nan take, na huɗu kuma ya rasu a asibiti.” Ya ƙara da cewa bayan harin, sojoji sun isa garin wanda hakan ya sa maharan suka tsere, amma duk da...
’Yan bindiga sun kai sabon hari wasu yankuna na Jihar Sakkwato, inda suka kashe mutane huɗu tare da yin awon gaba da mata huɗu. Wani mazaunin Gatawa, ya shaida wa Aminiya ce harin ya faru ne a daren ranar Asabar, lokacin da ’yan bindiga sama da goma suka shiga garin a kan babura. Mutum 5 sun rasu sanadin gobara da faɗa wa rijiya a Kano Sojoji sun yi yunkurin juyin mulki a Jamhuriyar Benin A cewarsa, “Sun ratsa gefen gari suka dinga shiga gida-gida. Sun harbe mutane huɗu; uku sun mutu nan take, na huɗu kuma ya rasu a asibiti.” Ya ƙara da cewa bayan harin, sojoji sun isa garin wanda hakan ya sa maharan suka tsere, amma duk da...
Majalisar Dokokin Amurka ya iso Abuja yayin da ƙasashen biyu ke ƙara matsa ƙaimi wajen tattaunawar diflomasiyya kan haɗin gwiwar tsaro da kuma zargin tauye haƙƙin addini. Mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan tsaro Nuhu Ribadu, ya ce ya gana da wakilan kuma zuwan tawagar na cikin abubuwan da suka amince da shi a tasu ziyarar da suka kai birnin Washington a watan Nuwamba. “Tawagar ta ƙunshi ‘yanmajalisar wakilai Mario Díaz-Balart, Norma Torres, Scott Franklin, Juan Ciscomani, da Riley M. Moore,” in ji Ribadu cikin wata sanarwa a shafinsa na sada zumunta. Kazalika, Jakadan Amurka a Najeriya Richard Mills na cikin tawagar. A cewar Ribadu, tattaunawar ta mayar da hankali kan yaƙi da ta’addanci, tabbatar da zaman lafiyar yanki...
Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, ta tabbatar da rasuwar wasu mutum biyar sakamakon haɗura uku da suka auku a jihar. Kakakin hukumar, Saminu Yusif Abdullahi, ya ce hatsrin farko ya faru ne da safiyar ranar Alhamis a unguwar Badawa Layin Day by Day ca Ƙaramar Hukumar Nassarawa. Sojoji sun yi yunkurin juyin mulki a Jamhuriyar Benin Jirgin sojin sama ya yi hatsari a Neja Lamarin ya faru ne a wani gida mai faɗin kafa 25 da 20 wanda ya kama da wuta. Ma’aikatan kashe gobara sun ceto wata yarinya mai shekara 10 daga a cikin gidan, amma daga baya ta rasu a asibiti. An bai wa iyayenta gawarta. Hatsari na biyu ya faru ne a Ƙauyen Badume Kanawa da...
Gwamnatin Jamhuriyar Benin ta bayyana cewa ta dakile wani yunkurin juyin mulki, bayan da wasu sojojin ƙasar suka sanar da cewa sun hambarar da shugaba Patrice Talon a gidan talabijin na kasar. Talon, mai shekaru 67, tsohon dan kasuwa ne wanda aka yiwa lakabi da “Sarkin Auduga na Cotonou”, zai mika mulki a watan Afrilun shekara ta 2025 dake ƙaratowa, bayan shafe shekaru 10 a kan karagar mulki wanda ke nuna samun ci gaban tattalin arziki mai inganci. Da sanyin safiyar Lahadi ne sojojin da ke kiran kansu da suna “Kwamitin Soji na sake farfado da ƙasa” (CMR), suka gabatar da wata sanarwa a gidan talabijin na kasar cewa sun gana kuma sun yanke shawarar cewa “An tsige shugaba Patrice...
Wani jirgin Sojin saman Najeriya ya yi haɗari jim kaɗan bayan tashi daga sansanin Sojin ƙasar da ke Kainji a jihar Neja, sakamakon tangarɗar inji. Kakakin rundunar sojin saman na Najeriya Ehimen Ejodame lokacin da yake tabbatar da faruwar haɗarin ya ce babu ko mutum guda da ya rasa ransa sanadiyyar wannan haɗari, sai dai fasinjan da ke cikin jirgin yanzu haka suna karɓar kulawar gaggawa a asibiti. Tuni dai aka jiyo hafson sojin saman Najeriyar Air Marshal Sunday Aneke, na yabawa matuƙan jirgin wanda ya bayyana da jajirtattu, da ya ce ƙwarewa da jarumtarsu ce ta tseretar da asarar rayuka a haɗarin. Jiragen sojin Najeriya a lokuta da dama na gamuwa da haɗari wanda ke kaiwa ga asarar ɗimbin...
Gwamnatin kasar Rwanda ta rattaba hannu a kan yarjeniya na dalar Amurka miliyon $228 a karkashin sabon tsarin taimako na gwamnatin kasar Amurka. Shafin yanar gizo na labarai Africa News ya bayyana cewa tallafin zai taimakawa kasar Rwanda ta kyautata harkokin kiwon lafiya a kasar ta Rwanda a yayinda tallafin kudaden zai ci gaba a sabon tsarin da gwamnatin Amurka ta fitar don tallafawa kasashen kawayenta. Tun ran Jumma’a ne aka bada labarin kulla wannan yarjeniyar, bayanda shugaba Paul Kagame na kasar Rwanda ya rattaba hannu kan wata yarjeniya ta zaman lafiya tsakaninsa da shugaban kasar Kongo Felix tsetsekedi don kawo karshen yaki a gabacin kasar Kongo wanda kasar ta Amurka ta jagoranta. Karkashin wannan yarjeniyar dai Amurka zata kashe...
Tom Barrack jakadan Amurka na musamman a kasar Siriya ya bayyana cewa gwamnatin kasar Amurka ta yi kokarinkifar da gwamnatin JMI a baya har sau biyu amma ta kasa yin haka. Tashar talabijin ta Presstva a nan Tehran ta nakalto Barrack yana fadawa wani kamfanin dillancin labaran UAE a ranar jumma’an da ta gabata, ya kuma kara da cewa daga shekara ta 1946 ya zuwa yau gwamnatin Amurka ta yi kokarin kifar da gwamnatoci 93 biyu daga cikinsu a kasar Iran ba tare da samun nasarara ba. Amma akwai da dama wadanda suka sami nasara. Ya ce kafin Trump ya hawo kan kujerar shugabancin Amurka mun yi kokar kifar da gwamnatin kasar har sau biyu ba tare da samun nasara...
Kakakin majalisar dokokin kasar Iran Mohammad Bakir Qalibaf ya yi tir da kungiyar kasashen larabawa na yankin tekun Farisa, wadanda suka fidda bayanin bayan taronsu a baya bayan nan suka allawadai da kuma nuna goyon bayansu ga kasar UAE kan mallakar tsibiran Tumb babba da tumb karami da Abu Musa. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Qalibaf yana cewa bayan duk wani taron da suka gudanar sai kaji cewa wadan nan kasashen Larabawa suna allawadai da Iran kan mallakar wadanan tsibiran, tare da wannan kuma suna kokarin bata dangantaka mai kyau dake tsakanin kasashen yankin da Iran. Yace yana da tabbaci wasu kasashen duniya ne suke ingiza wadan nan kasashen larabawa su rika tada hankali don a...
Kungiyar Hamas wace take iko da yankin gaza ta bada sanarwan cewa, zata mika makamanta ne kawai ga gwamnatin Falasdinawa wacce take da cikekken iko a kan kasar Falasdinu da aka mamaye, idan yahudawan sun kawo karshen mamayar da sukewa kasar. Shafin labarai na yanar Gizo ArabNews ya nakalto shugaban kungiyar Khalilul Hauua yana fadar haka ya kuma kara da cewa ; idan HKI ta kawo karshen mamayar da takewa kasar Falasdinu gaba dayanta, Hamas zata mika makamanta ga gwamnatin Falasdinawa wacce al-ummar Falasdinu ta zaba. Ya ce ; Samuwar Makamammu na da dangantaka da mamaye, don haka a duk lokacinda HKI ta kawo karshen mamayar kasar Falasdinu (daga teku zuwa ) a lokacin kungiyar Hamas zata mika makamanta ga...
Sojoji a kasar Jamhuriyar Benin sun kifar da gwamnati a wani juyin mulki da suka sanar a ranar Lahadi. Sojojin sun bayyana ne a gidan talabijin na kasar inda suka sanar da tsige Shugaban Kasa Patrice Talon da kuma rushe duk hukumomin kasar. Dakarun, karkashin jagorancin Laftanar Kanar Pascal Tigiri, sun rufe iyakokin kasar da rushe jam’iyyun siyasa. Zuwa lokacin kammala wannan labarin babu labarin halin da Shugaba Talon wanda ke kan karagar mulkin tun a 2016 yake ciki. Amma ministan harkokin kasar, Olusegun Ajadi Bakari, ya ce an samu yunkurin kifar da gwamnati, amma ana neman shawo kan lamarin.
Ministan harkokin cikin gidan kasar Venezuela ya bayyana cewa al’ummar Venezuela ba ta tsoron barazanar da Amurka take yi ma ta, domin juyin juya halin kasar zai ci gaba, kuma azamar al’umma ce za ta yi nasara a gaban masu wuce gona da iri. Ministan harkokin cikin gidan kasar ta Venezuela Diosdado Cabello Rondón wanda kuma shi ne sakataren jam’iyyar gurguzu ta kasar, ya ce a halin yanzu juyin juya halin kasar yana fuskatar gwagwarmaya ce wacce ba ta makami domin fuskantar matsin lamba na kowace rana daga Amurka. Ministan harkokin cikin gidan kasar ta Venezuela wanda ya halarci bikin rantsar da sabbin shugabannin al’umma a jihar Monagas ya yi Ishara da yadda Amurka ta girke jiragen yaki a ruwa...
Kungiyar ‘yan wasan ” Taekwondo” Iran dake kasa a shekaru 21 sun zama gwarazan duniya da aka yi a birnin Nairobi, bayan da su ka sami zinariya 3 da azurfa 1 sai kuma tagulla biyu. Kamfanin dillancin labarun “Irna” ya nakalto cewa; a jiya Asabar ne aka kawo karshe gasar wasan na ” Taekwondo” wanda ya sami halartar ‘yan wasa 452 daga kasashe 75. A ranar ta karshe ta wasan, dan wasan Iran Muhammad Aizadeh, ya sami azurfa, sai kuma wani dan wasan “Matin Rizayi wanda ya sami tagulla. Wadanda su ka sami zinariya kuwa su ne Abul Fadl Zandi, da Radin Zinalu sai kuma Amir Riza Gulami. Kasar Turkiya ta zo ta biyu da ta sami zinariya biyu da...
Rahotanni da suke fitowa daga birnin Pretoria sun ce, adadin mutanen da su ka kwanta dama sanadiyyar bude wuta ta kan mai uwa da wabi, sun kai 11 daga cikinsu har da karamin yaro dan shekaru uku. Jami’an ‘yan sandan kasar ta Afirka Ta Kudu ne su ka sanar da cewa an bude wutar ne a cikin wani gidan shan barasa dake birnin Pretoria a jiya Asabar. Haka nan kuma sun sanar da kama wasu mutane uku da ake zargin suna da hannu a abinda ya faru. Kananan yara uku ne dai kisan ya hada da su, biyu daga cikinsu shekarunsu uku-uku ne, sai daya mai shekaru 12. Kuma da akwai wata buduruwa ‘yar shekaru 16 da ita ma lamarin...
Rahotannin da suke fitowa daga DRC sun ce fadan ya barke ne dai bayan kwanaki kadan da gwamatin DRC da ta Rwanda su ka amince da tabbatar da zaman lafiya. A can gabashin kasar an ga dubban mutane maza, mata, da kananan yara suka dauke da kayayyakinsu a lokacin da suke ficewa daga kauyukna da suke gundunar Kivu ta kudu,saboda kaucewa sabon fadan da ya barke a tsakanin sojojin kasar da na ‘yan tawayen kungiyar M23. A jiya Asabar ne sabon fadan ya barke saboda bama-baman da ake amfani da su wajen kai hare-haren a tsakanin bangarorin biyu da suke fada da juna. Wani mutum da yake gudu daga garin Luvungi ya fada wa cibiyar watsa labaru ta “Afirka Today”...
Daga Usman Muhammad Zaria Ma’aikatar Ayyuka da Sufuri ta Jihar Jigawa ta yi kiyasin kashe kudade miliyan dubu 161 da milyan 336 domin gudanar da ayyukan hanyoyin mota da harkokin yau da kullum a sabuwar shekara ta 2026. Babban sakataren ma’aikatar, Malam Ahmad Isah, ya bayyana haka lokacin da ya ke kare kiyasin kasafin kudin ma’aikatar a gaban kwamatin ayyuka da sufuri na majalisar dokokin jihar Jigawa. Babban Sakataren ya yi bayanin cewar, za a yi amfani da mafi yawan kudaden ne wajen gudanar da ayyukan hanyoyin mota tsakanin gariruwa da hanyoyin burji da kuma titunan cikin gari. Yana mai cewar, haka kuma za a gudanar da ayyukan hanyoyi a manyan makarantun jihar ciki har Jami’ar Sule Lamido da ke...
Rahotanni sun bayyana cewa dakarun tsaron kasashen pakistan da Afghanistan sun yi musayar wuta mai tsananin a iyakokin kasashensu, kuma yayi sanadiyar mutuwar mutane 5, hakan na nuna irin rikicin dake tsakanin kasashen masu makwabtataka da juna, bayan sun cimma yarjejeniyar sulhu a kasar saudiya amma da alama babu ci gaban da aka samu. A wani sakon da kakakin gwamnatin Taliban ya wallaka a shafinsa na x zabihullah majahid yace sojojin kasar Pakistan sun kaddamar da hari a wani yanki dake lardin kandahar na kasar Afghanistan da hakan yasa sojojin su mayar da martani. Sai dai ana sa bangaren firaministan kasar Pakistan Shebaz sharif ya ce sojojin kasar afgahnistan ne suka fara harbe harbe a iyakar chaman, Dangantaka tsakanin Afghanistan...
Rahotanni na nuna cewar wani jirgin yaƙi na rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF), ya yi hatsari a Jihar Neja. Jirgin ya faɗi a sansanin NAF da ke Kainji jim kaɗan bayan tashinsa. Nakiya ta hallaka yara 4 a Borno Kwastam ta kama jirgin ruwan Brazil ɗauke da hodar iblis a Legas Majiyoyi sun ce jirgin ya samu matsala ne, lamarin da ya sa matuƙan jirgin suka ɗauki matakin gaggawa. Mai magana da yawun NAF, Ehimen Ejodame, ya tabbatar da faruwar lamarin. Ƙarin bayani na tafe…
A wata tattaunawa ta wayar tarho da ta gudana tsakanin ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi da takwaransa na kasar masar Badr Abdelatty sun bayyana cewa isra’ila na ci gaba da kai hare-hare da keta yarjejeniyar dakatar da bude wuta a Gaza da kuma kasar labanon, Ci gaba da keta yarjejeniyar dakatar da bude wuta mai mataki 20 kan gaza,wanda shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar hujja ce da ta tabbata tun daga farko kamar yadda rahotanni da suka fito daga yankin gaza suka bayyana cewa akalla mutane 366 ne abin ya shafa daga lokacin da aka cimma yarjejeniyar zuwa yanzu. A watan nuwamba shekara ta 2024 ne aka cimma yarjejeniyar dakatar da bude wuta tsakanin kungiyar hizbulla da...
Rahotanni na nuna cewar wani jirgin yaƙi na rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF), ya yi hatsari a Jihar Neja. Jirgin ya faɗi a sansanin NAF da ke Kainji jim kaɗan bayan tashinsa. Nakiya ta hallaka yara 4 a Borno Kwastam ta kama jirgin ruwan Brazil ɗauke da hodar iblis a Legas Majiyoyi sun ce jirgin ya samu matsala ne, lamarin da ya sa matuƙan jirgin suka ɗauki matakin gaggawa. Mai magana da yawun NAF, Ehimen Ejodame, ya tabbatar da faruwar lamarin. Ƙarin bayani na tafe…
Fira ministan kasar Qatar shaikh mohammad bin Abdurrahaman al thani yayi gargadi game da ci gaba da kai hare-hare da kame falasdinawa da HKi ke yi a yankin gaza, ya jaddada cewa shirin da shugaban Amurka ya bullo da shi na zaman lafiya zai zama gaskiya ne idan isra’ila ta janye dukkan sojojinta a yankunan da ta mamaye a gaza. Da yake bayani a wajen taron da aka gudanar da birnin Doha al thani yace yarjejeniyar tsagaita wuta da aka kwashe watanni biyu da cimmawa tsakanin Hamas da Isra’ila ta kai wani muhimmin matsayi adaidai lokacin da matakin farko na shirin da trump ya bullo da shi mai matakai 20 yake gaba da karewa. Ya kara da cewa masu shiga...
Sabon bashin, ya nuna yadda Bankin ya bai wa kasar bashin da ya kai jimlar dala biliyan 5.1 tun daga ranar 31 na watan Okutobar 2025. Kazalika, wannan sabon bashin, zai taimaka wa kashi na biyu na shirin habaka tattalin arziki a bangaren samar da makamashi da sauye-sauye, a fannin makamashin da cimma burin da ake da shi, na rage dumamar yanayi. A zagaye na farko na shiri, za a kara karfafa sauye-sauye wajen tafiyar da kudade da tabbatar da ana aiki da Ka’ida da kuma sanya ido, kan yadda ake kashe kudaden Gwamnati. Bugu da kari a zagaye na biyu kuma, manufar shi ne, a kara habaka samar da makamashi da fadada samar da wutar lantarki wanda hakan zai...
Rahotanni sun bayyana cewa kungiyoyin kare hakkin bil adama na yankin falasdinu sun yi gargadi game da makircin da isra’ila ke kullawa na kashe Marwan bargusu daya daga cikin shuwagabanin falasdinawa a inda take tsare da shi a gidan yari, samakamon gana masa azaba da aka yi . Babban darektan kungiyar pps Amad Najjar yayi kira ga majalisar dinkin duniya da sauran kasashen duniya da su dauki matakin gaggawa tun kafin lokaci ya kure game da abin da israila ke kokarin yi kan marwan barghusi da hakan ya sabama dokokin kasa da kasa. Haka zalika yayi kira ga majalisar dinkin duniya da ta ziyarci inda ake tsare da barghusi domin ganin irin halin da yake ciki, kuma su matsa lamba...
Wata nakiya da ta fashe a garin Banki, da ke Ƙaramar Hukumar Bama, a Jihar Borno, ta yi sanadin mutuwar yara huɗu tare da jikkata wani yaro guda ɗaya. Rundunar ’yan sandan jihar, ta tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Juma’a. Kwastam ta kama jirgin ruwan Brazil ɗauke da hodar iblis a Legas Ranar Sabuwar Shekara za mu rufe duk na’urar POS mara rajista —Gwamnati Lamarin ya faru da misalin ƙarfe 12:40 na rana a bayan tashar motar Banki da ke yankin Wajari. Wani mazaunin garin, Babagana Mohammed, ya kai rahoton fashewar nakiyar da misalin ƙarfe 1 na rana, wanda hakan ya sa aka tura jami’an tsaro zuwa yankin. DPO na Banki tare da ƙwararrun sashen cire bam, sun killace...
Hukumar Kwastam, ta kama kilo 25.5 na hodar iblis a wani jirgin ruwa na ƙasar Brazil mai suna MV San Anthonio a tashar jirgin ruwa ta Legas. An ɓoye hodar cikin ƙananan jakunkuna biyar. ’Yan bindiga sun harbe ɗan sanda har lahira a Edo Ranar Sabuwar Shekara za mu rufe duk na’urar POS mara rajista —Gwamnati Kwanturola Emmanuel Oshoba, ya ce an gudanar da aikin ne bayan samun bayanan sirri tare da haɗin gwiwar hukumar NDLEA. Ya ƙara da cewa jirgin ya tsaya a ƙasashen da suka yi ƙaurin suna wajen harkar safarar miyagun ƙwayoyi kafin isowarsa Najeriya. An tsare jirgin, sannan an miƙa hodar da aka kama ga NDLEA domin ci gaba da bincike. Oshoba, ya ce wannan nasara...
Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Jigawa ta ce za ta gudanar da aikin shigar da sabbin dokokin jihar cikin kundin bayanan dokoki da aka yi a jihar. Babban Sakataren ma’aikatar, Barrister Lawan D. Baba, ya bayyana haka lokacin da ya ke kare kiyasin kasafin kudin sabuwar shekara ta 2026 a gaban kwamatin harkokin shari’a na majalisar dokokin jihar Jigawa. Barrister Lawan D. Baba ya bayyana cewa ma’aikatar ta yi kiyasin kashe naira milyan 311 da dubu 847 a kasafin kudin sabuwar shekara. Babban sakataren yace za su mayar da hankali ga batun kawar da jinkiri wajen gudanar da shari’o’i domin karfafa matakan samun shari’a cikin sauri ga al’ummar jihar. A nasa jawabin, Shugaban kwamatin harkokin shari’a na majalisar dokokin jihar Jigawa...
An harbe wani jami’in ɗan sanda har lahira, yayin da yake tsaka da binciken ababen hawa a Benin a Jihar Edo. Kakakin rundunar, CSP Moses Yamu, ya ce lamarin ya faru da misalin ƙarfe 12 na ranar Juma’a, lokacin da jami’an rundunar suka tsayar da wata baƙar mota ƙirar Lexus, amma ta ƙi tsayawa. ’Yan sanda sun ceto yara 2 da aka yi garkuwa da su a Borno Ƙasashen waje na taimaka wa ’yan ta’adda a Najeriya —Sheikh Gumi Ɗaya daga cikin mutanen da ke cikin motar ya buɗe wa jami’an da ke shingen wuta, sannan suka tsere. A dalilin haka ne suka harbe wani ɗan sanda wanda ba a bayyana sunansa ba har lahira. Kwamishinan ’yan sandan jihar, Monday...
Hukumar Kula da Rajistar Kamfanoni (CAC) ta ba wa dukkan masu gudanar da harkar kuɗi ta PoS a fadin Najeriya, wa’adin ranar 1 ga Janairu, 2026, su yi cikakken rajista ko ta rufe su. A ranar Asabar, Hukumar ta sanar cewa yawaitar masu PoS marasa rajista a sassan ƙasar nan ya yawaita. Don haka ta jaddada cewa gudanar da PoS ba tare da rajista ba ya saɓa wa Dokar Kamfanoni ta 2020 da kuma ka’idojin Babban Bankin Najeriya (CBN). Hukumar ta kuma zargi wasu kamfanonin fasahar kudi (fintech) da daukar wakilai ba tare da rajista ba, tana bayyana wannan dabi’a a matsayin da sakaci kulawa da kuma barazana ga daidaiton tsarin kuɗi na ƙasar. Ta ce hakan na jefa miliyoyin ’yan...
’Yan sanda sun ceto yara 2 da aka yi garkuwa da su, masu shekaru hudu da biyar, a Jihar Borno. An ceto yaran ne a yayin wani samame da ’yan sanda suka kai a Ƙaramar Hukumar Jere, inda masu garkuwar suka je karbar kuɗin fansa. Sanarwa da ASP Nahum Kenneth Daso, kakakin rundunar ya fitar ta ce, bayan sun sami rahoto a ranar 4 ga Disamba cewa yara uku sun bace, washegari masu garkuwar suka sako ɗaya daga cikin yaran da takardar neman naira miliyan 10 domin sakin sauran biyun. A ranar ce jami’an rundunar suka kai samame a wurin da aka ware don karɓar kuɗin fansar. Ganin hakan masu garkuwa da mutanen, suka farga da wannan tarko da aka...
Wasu mutane uku sun rasu yayin da suke tsaka da aikin yasar rijiya a garin Badume da ke Ƙaramar Hukumar Bichi a Jihar Kano. A yayin da suke aikin haƙar rijiya, ɗaya daga cikinsu ya shiga domin yasowa biyu kuma na janyo ƙasar da aka haƙo. Ana cikin haka igiyar ta tsinke, inda nan take ƙasa ta koma kan dattijon mai shekara 65 da ke haƙar rijiyar. Hakan ya sa ɗansa mai shekara 20 shiga rijiyar domin fito da shi amma abu ya tura. A nan ne na ukunsu mai 60 Yakubu Abdullahi shi ma ya shiga domin ceto su, amma duka dai abu ya gagara. A ƙarshe jami’an Hukumar Kashe Gobara sun yi nasarar ceto su ukun a sume,...
Kungiyar kwallon kafa ta Iran “Time Milli” Ta Fada ‘Group H’ a rabon da aka yi na gasar kwallon kafa ta FIFA 2026 wanda za’a gudanar a kasashen Amurka Canada da kuma Mexico a shekara mai zuwa. Group H dai ta kunshi Iran,Masat Belgium da New Zealand. Kamfanin dillancin labaran Ip na kasar Iran ya ce wannan shi ne gasan FIFA wacce ta tara kasashe mafi yawa a gasar kwallon kafa ta duniya a tarihin FIFA, inda kasashe 48 suna cancanci shiga gasar. Kuma an rarrabasu zuwa ‘group 12’ ko wace group tana da kungiyoyinkwallon kafa guda 4. A zagaye na farko za’a dauki kasashen guda biyu a ko wani Group , wato kasashe 16 ke nan, sannan da kungiyoyi...
Yanzu ƴan Najeriya za su iya cire naira 100,000 ta na’urar cire kuɗi ta ATM a rana, haka ma abin yake a ɓangaren cire kuɗi ta na’urar POS. A ɓangaren ma’aikatu kuma, za su iya cire kuɗi har naira miliyan biyar ne a duk mako. Wannan na ƙunshe ne a cikin sabbin tsare-tsaren da Babban Bankin Najeriya CBN ya fitar bayan garambawul da ya yi kan dokokin cire kuɗi ta na’urar ATM da POS a Najeriya. Bankin ya ce wannan sabuwar dokar za ta fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Janairun shekarar 2026. A cikin wata sanarwa da daraktan tsare-tsare na bankin, Dr Rita Sike ta fitar a ranar Talata 2 ga watan Disamba, ta ce babban bankin...
Kasashen Larabawa da musulmi 8 ne suka gamu suka ki amincewa da shirin HKI na korar Falasdinawa da karfi daga Gaza. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran tanakalto ministocin harkokin kasashen waje na kasashen Saudia, Masar, Jordan, da UAE Pakisatan Turkey da kuma Qatar sun bada bayanin hadin giwa daga kasashen Saudiya kan cewa shirin HKI na bude Kofar Rafah ta fcewar Falasdinawa Kawai ba tare da shigowa ba, baa bin amincewa bane. Bayanin ya kara da cewa, wannan shirin yana da hatsari, kuma shiri ne wanda zai hana kafuwar kasar Falasdinu idan har duk wanda ya fit aba zai sake shigowa ba. Jami’an diblomasiyyar sun bayyana cewa, shirin ya sabawadokokin kasa da kasa, kuma barazana ce ga...
Sojojin kasashen Afghan da Pakistan sun yi musayar wuta a safiyar yau Asabar, a kan iyakokin kasashen biyu. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa wannan budewa juna wuta ya nuna cewa yarjeniyar tsagaita budewa juna wuta na kasar saudiya a kwanakin baya ya kasa aiki. Hukumomin kasashen biyu sun tabbatar da cewa sojojin kasashen nasu sun yi musayar wuta a daren Jumma’a wayewar garin asabar. Tare da amfani da makamai masu linzami . Ko wani bangare yana zargin dayan da fara bude wuta. Zabihullahi Mujahid kakakin gwamnatin kasar Afganistan ya rubuta a shafinsa na X kan cewa, sojojin kasar Pakisatan ne suka fara bude wuta a kan iyakar kasar da ke Spin Boldak a cikin...
Majiyar ma’aikatar tsaron kasar Rahsa ta bada sanarwan cewa garkuwan sararin samaniyar kasar ta kakkabo jiragen Drones na yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa na kasar Ukrai har guda 116 a daren jiya kadai. Tashar talabijan ta Almayadeen ta kasar Lebanon tanakalto majiyar ma’aikatar tsaron na cewa, rasha ta kakkabo jiragen 116 ne a yankuna har 10 a cikin kasar. Bayanin ya kara da cewa an kakkabo 29 daga cikinsu a yankin Riyazan, 26 a yankin Furunaj, 23 a yankin Biryonsk sai kuma 21 a yankin Bilgurun. Har’ila yau an kakkabo wasu 6 a Tafrin, 3 a kkursek sai biyu Tambuf. Sannan daya A Tula. Na karshe kuma a Uryol. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of...
Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Godswill Akpabio ya shigar da Sanata Natasha Akpoti ƙara a kotu kan zargin ɓata masa suna yana mai neman ta biya shi diyyar naira biliyan 200. Sanata Natasha mai wakiltar jihar Kogi ta tabbatar da karɓar sammacin a shafukanta na sada zumunta, inda ta nuna jin daɗinta tana mai cewa ta samu damar bayyana hujjojinta kan zargin yunƙurin lalata da ta zarge shi da yi a baya. “Yau 5 ga watan Disamban 2025, na karɓi sabon sammacin kotu kan ƙarar diyya ta naira biliyan 200 da Sanata Godswill Akpabio ya kai ni game da ɓata masa suna da zargin lalata,” a cewar Natasha. “Na yi farin ciki da Sanata Akpabio ya taso da wannan batu saboda...
Kotu ta yanke wa wani wanda ya yi wa wata yarinya ’yar shekara 12 fyaɗe hukuncin ɗaurin rai-da-rai a Ƙaramar Hukumar Guba ta Jihar Yobe. Babbar Kotun Jihar Yobe da ke zaune a ƙaramar hukumar Gujba ta yanke wa mutumin mai shekaru 31 mai suna Ali Kwano. An gurfanar da shi ne a kan zargin ya kai yarinyar cikin aji a ƙaramar makarantar sakandare ta je-ka-ka-dawo da ke garin Bumsa, inda ya yi lalata da ita da ƙarfi. Ya yaudari yarinyar ce bayan ya gaya mata cewa ta jira shi a cikin aji bisa cewar zai sayi ƙosai. Bayan da ta shiga ajin sai ya kama hannunta, ya rufe bakinta ya danne ta a ƙasa sannan ya yi lalata da...
Gwamnatin Kano ta tabbatar da kama Muhuyi Magaji Rimingado, tsohon shugaban hukumar yaƙi da cin hanci ta jihar ranar Juma’a, inda ta yi zargi wasu ‘yansiyasa da hannu a kamen nasa. Wata sanarwa daga ofishin Kwamashinan Shari’a Abdulkarim Maude ta ce jami’an ‘yansanda ne suka kama lauyan a ofishinsa da ke kan titin Zariya da misalin ƙarfe 5:30 na yamma, kuma suka tafi da shi hedikwatarsu da ke Bompai. Kwamashinan ya siffanta kamen da “abin damuwa sosai” wanda “ya yi kama da yanayin aikin soja”. Ya yi iƙirarin cewa dakaru kusan 40 ne ɗauke da makamai suka je kama Muhuyi. “Kwamashinan ya nuna cewa akwai yiwuwar lamarin yana da alaƙa da binciken da ake yi wa wasu manyan ‘yansiyasa,” in...
Amurka ta faɗaɗa yawan ƙasashen da ta sanyawa haramcin samun bizar shiga ƙasar zuwa 32 ƙarƙashin jagorancin Donald Trump da ke tsaurara matakan shiga wannan ƙasa ta yammacin duniya saboda abin da ya kira barazanar ƙasashen ga tsaron Washington da kuma kange kwararar ƴan cirani. Sakatariyar tsaron cikin gida ta Amurka Kristi Noem yayin wasu kalamanta a shirin kai tsaye ta gidan talabijin, ta ce dole ne Amurka ta dakatar da bizar ga duk wata ƙasa da ke turo mata baragurbi waɗanda ke wargaza tsaro da zaman lafiyarta. Duk da cewa Noem bata bayyana sunayen ƙasashen ba, amma wasu bayanai da suka fita daga ma’aikatar sirrin ƙasar sun ce galibinsu ƙasashe ne na Afrika ciki kuwa har da Kenya da...
Pars Today – Hanieh Rostamian, jarumar harbin bindiga ta Iran, za ta fafata a wasan karshe na gasar cin kofin duniya. Za a fara gasar cin kofin duniya ta 2025 gobe, Asabar, a Qatar. A cewar Pars Today, tunda manyan ‘yan wasan harbi na duniya suna shiga wannan gasar, Hanieh Rostamian—wanda a halin yanzu yana cikin manyan ‘yan wasa 10 a duniya—zai fafata a gasar bindiga mai tsawon mita 25 a ranar Lahadi. Wannan ya nuna cewa Rostamian ya bayyana a karo na hudu a gasar cin kofin duniya. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0...
Iran da Rasha sun rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna guda 20, kwangilolin haɗin gwiwa na fasaha guda biyar
Pars Today – Ziyarar da tawagar Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kai Rasha a fannin sadarwa da fasahar sadarwa ta zamani ta haifar da sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin gwamnatoci guda 20, da kuma kwangiloli biyar tsakanin kamfanoni daga kasashen biyu. Meysam Abedi, Mataimakin Ministan Sadarwa da Fasahar Sadarwa ta Duniya kan Fasaha da Kirkire-kirkire na Iran, ya ce: “A lokacin tafiyar zuwa Moscow ranar Juma’a, an sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna guda 20 da kwangilolin haɗin gwiwa na fasaha guda biyar tsakanin Iran da Rasha, kuma muna fatan ganin hadin gwiwa mai zurfi da kuma karuwar darajar kwangilolin hadin gwiwa na bangarorin biyu a kowace shekara.” A cewar Pars Today, Abedi ya kuma yi magana kan...
Kakakin Majalisar Dokokin jihar Ribas, Martin Amaewhule tare da mambobin majalisar su 15 sun sanar da sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC. Amaewhule ya bayyana shawarar ’yan majalisar ne a zaman majalisa na ranar Juma’a, inda ya ce akwai abin da ya kira “rarrabuwar kai a fili” a cikin PDP wanda ya sa suka yanke wannan shawara. Yayin da yake bayyana dalilin sauya sheƙar, Amaewhule ya ce sun bar PDP ne saboda rikice-rikicen cikin jam’iyyar. Bugu da ƙari, a wani mataki da ake ganin na ƙoƙarin kaucewa gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2026 daga Gwamna Siminalayi Fubara ne, Kakakin ya sanar da dage zaman majalisa har zuwa watan Janairu 2026. Ayyukan majalisar a kwanakin baya-bayan nan sun nuna cewa...
Mutanen garin Dadin-Kowa da ke Ƙaramar Hukumar Yamaltu Deba a Jihar Gombe, sun shiga damuwa kan yadda wata Dorinar ruwa ta addabi yankin, ta hanyar kashe mutane da kuma lalata gonaki. Cikin watanni biyu, Dorinar ta kashe mutum biyu, ta karya wasu biyu, sannan ta jikkata wasu huɗu, waɗanda yawanci manoma da masunta ne a Dam ɗin Dadin-Kowa. Matsalar ta sa ɗan Majalisar Tarayya na Yamaltu Deba, Inuwa Garba, ya kai koke gaban Majalisar Wakilai, inda ya nemi gwamnati ta hanzarta kawo wa mazauna yankin ɗauki. Ya ce, “Ta’addancin Dorinar ya yi yawa. Idan ba a taimaka mana ba, za ta ci gaba da kashe mutane da lalata amfanin gona.” A makon da ya gabata, Dorinar ta farmaki wani matashi...
Fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Ahmad Mahmud Abubakar Gumi, ya yi zargin cewa ƙasashen waje na taimaka wa ƙungiyoyin ’yan ta’adda Najeriya. Sheikh Ahmad Gumi ya danganta ƙaruwar matsalar tsaro a Najeriya a baya-bayan nan da irin maganganun da ƙasashen waje suka riƙa yi a kai. A yayin wata hira da BBC Hausa, malamin ya bayyana cewa yanayin taɓarɓarewar tsaro a baya-bayan nan ya nuna akwai alamun hannun ƙasashen waje a ciki. Tsohon hafsan sojin, ya ce matsalar tsaro ta ragu a sassan ƙasar nan sai baya-bayan nan da ƙasashen waje suka fara magana a kai. Ya bayyana cewa an samu aminci a hanyar Abuja zuwa Kaduna, wadda baya ta kasance tarkon mutuwa, amma sai kwanan nan matsalar ta fara dawowa...
Makwanni biyu bayan da masu garkuwa su ka sace kananan yara ‘yan mamaranta an bayyana cewa;har yanzu da akwai 250 a hannun barayin mutanen. A ranar 21 ga watan Nuwamba ne dai masu dauke da makamai su ka kutsa cikin wata makaranta ta majami’ar Roman Katolika, su ka yi awon gaba da dalibai 300 da kuma malamai. Mahukuntan makarantar sun ce dalibai 50 sun iya tserewa daga hannun wadanda su ka yi garkuwar da su, don haka har yanzu da akwai wasu 250 da suke a hannun barayin. Sace daliban da aka yi na bayan nan, shi ne mafi muni,tun wanda aka yi wa daliban makarantar Chibok a 2014 da adadinsu ya kai 276 a hannun Bokoharam. Jami’an tsaron kasar...
Shugaban kasar Rasha Vladmir Putin wanda ya kai ziyarar aiki kasar India ya bayyana cewa kasar tasa da kuma abokiyar kawancenta India za su bunkasa kasuwancinsu. Ziyarar ta shugaban kasar Rasha a Indiya, tana a karkashin taron da kasashen biyu suke yi ne daga lokaci zuwa lokaci wanda wannan shi ne karo na 23 da ya kunshi ayyukan tattalin arziki, siyasa da al’adu. A yayin taron, kasashen biyu sun cimma matsayar bunkasa girman kasuwancinsu da zai kai dalar Amurka biliyan 100 daga nan zuwa 2030. A nashi gefen Fira ministan kasar India, Modi ya ce, duk da fadi tashin daake samu,amma alakar kasashen biyu India da Rasha tana nan daram. Taron na kasashen biyu dai ya damu Amurka tana mai...
Babban magatakardar kungiyar Hizbullah Sheikh Na’im Kassim wanda ya gabatar da jawabi a jiya Juma’a da marece ya yi suka akan yadda aka shigar da farar hula dan kasar Lebanon a cikin kwamitin dake sa ido akan tsagaita wutar yaki da Haramtacciyar kasar Isra’ila, yana mai bayyana hakan da cewa; ya sabawa dukkanin bayanan da su ka rika fitowa a hukumance na fada ganin an daina kawo wa Lebanon hari sannan ayi hakan. Jawabin na Sheikh Na’im ya yi shi ne adaidai lokacin da ake tunawa da kuma girmama malaman addini da su ka yi shahada, yana mai cewa abinda aka yi na tura wakilin Lebanon farar hula a cikin wannan kwamitin tsagaita wutar, tamkar bai wa Isra’ila kyauta ne...
Gwamnatin Iraki Ta Kore Saninta Da Shigar Da Sunayen Hizbullah Da “Ansarullah” A Cikin Na ‘Yan Ta’adda
Fadar gwamnatin kasar Iraki ta sanar da cewa ba ta masaniya akan yadda aka shigar da sunayen Ansarullah na Yemen da kuma Hizbullah ta kasar Lebanon a cikin jerin sunayen kungiyoyin ‘Yan ta’adda da aka rike kudadensu dake bankunan kasar. Bayanin fadar gwamnatin kasar ta Iraki ya kuma kara da cewa; Matakai irin wadannan da ake dauka a kasar ba a aike wa da su zuwa fadar shugaban kasa,abinda ake aikewa fadar shi ne dokokin da majalisar dokokin kasar ta yi, domin a sake tantancewa da kuma amincewa.” Haka nan kuma sanarwar ta ce; wasu daga cikin abubuwan da ake aikewa fadar mulkin kasar sun hada da tsare-tsaren fadar shugaban kasa,amma abinda ya shafi matakan majalisar ministoci, da na kwamitin...
Daga Usman Muhammad Zaria Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ya yaba da gagarumin cigaba a harkar noma da Gwamna Umar Namadi ya samar cikin shekaru biyu kacal na mulkinsa. Ya bayyana haka ne a masarautar Gumel cikin Jihar Jigawa, yayin kaddamar da sabon masallacin Juma’a da Gidauniyar Kashim Shettima ta gina a matsayin wani ɓangare na bikin zagayowar cikar Sarkin Gumel shekaru 45 a kan karaga. A cewarsa, abin sha’awa ne yadda Gwamna Umar Namadi ya mayar da harkar noma a jihar Jigawa zuwa ta zamani cikin shekaru biyu kacal. Ya jinjina wa Gwamnan da al’ummar Jihar Jigawa bisa wannan ci gaba mai armashi. Kashim Shettima ya kara taya Sarkin Gumel, Alhaji Muhammadu Sani, murnar cika shekaru 45...
Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya (FIFA), ta kammala fitar da jadawalin Rukunin Gasar Kofin Duniya ta 2026. Za a gudanar da gasar ne a Amurka, Kanada da Mexico daga ranar 11 ga watan Yuni zuwa 19 ga watan Yulin 2026. Ina nan a PDP duk da sauya sheƙar ’yan majalisar Ribas — Wike DSS ta kama likitan da ke duba ’yan bindiga a dazukan Kwara Rabon jadawalin ya gudana ne a birnin Washington na ƙasar Amurka a ranar Juma’a, inda Ingila ta samu kanta a rukuni ɗaya Croatia. Brazil za ta kara da Maroko, yayin da Amurka za ta kara da Australia. Faransa za ta ɓarje gumi da Senegal, sannan Argentina za ta fafata da Austria. Ga jerin yadda kowane...
Mutanen garin Dadin-Kowa da ke Ƙaramar Hukumar Yamaltu Deba a Jihar Gombe, sun shiga damuwa kan yadda wata Dorinar ruwa ta addabi yankin, ta hanyar kashe mutane da kuma lalata gonaki. Cikin watanni biyu, Dorinar ta kashe mutum biyu, ta karya wasu biyu, sannan ta jikkata wasu huɗu, waɗanda yawanci manoma da masunta ne a Dam ɗin Dadin-Kowa. Na kashe N100bn a kan harkar tsaro a 2025 — Zulum Gwamnatin Gombe da UNICEF sun tallafa wa yara masu fama ƙarancin abinci mai gina jiki Matsalar ta sa ɗan Majalisar Tarayya na Yamaltu Deba, Inuwa Garba, ya kai koke gaban Majalisar Wakilai, inda ya nemi gwamnati ta hanzarta kawo wa mazauna yankin ɗauki. Ya ce, “Ta’addancin Dorinar ya yi yawa. Idan...
Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya bayyana cewa har yanzu yana nan daram a jam’iyyar PDP. Ya yi wannan bayani ne a Abuja a ranar Juma’a yayin da yake mayar da martani kan ficewar wasu ’yan majalisar dokoki na Jihar Rivers daga PDP zuwa jam’iyyar APC. Na kashe N100bn a kan harkar tsaro a 2025 — Zulum Najeriya ta shigo da tataccen man fetur na tiriliyan 12.8 cikin watanni 15 A ranar Juma’a, ‘yan majalisar Ribas guda 16, ciki har da Kakakin Majalisar, Martins Amaewhule, da suka sauya sheƙa zuwa APC. Amaewhule, ya ce ya yanke shawarar komawa APC ne saboda rarrabuwar kai da aka samu a PDP. Hakazalika, kakakin ya ce yana son ya yi aiki tare da...
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya ce gwamnatinsa ta kashe kusan Naira biliyan 100 a wannan shekara domin inganta tsaro a faɗin jihar. Ya bayyana haka ne lokacin da ya ziyarci Sarkin Uba, inda ya yi masa jaje kan hare-haren da suka yi sanadin mutuwar mutane da dama. Jami’an tsaro sun kama masu garkuwa da mutane 7 a Gombe Najeriya ta shigo da tataccen man fetur na tiriliyan 12.8 cikin watanni 15 Zulum ya yaba wa jami’an tsaro da al’umma kan ceto manoman mata 12 da aka yi garkuwa da su. Gwamnan, ya ce matsalar tsaro na hana samar da manyan ayyukan ci gaba a yankin. Ya kuma sake alƙawarin gina makarantu, asibiti, hanyoyi, cibiyar kwamfuta, cibiyar JAMB da...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe, tare da haɗin gwiwar maharba, sun samu nasarar tarwatsa gungun masu garkuwa da mutane, tare da kama mutum bakwai da ake zargi da aikata laifuka a Jihohin Gombe, Bauchi, Yobe da Adamawa. Rundunar ta samu nasarar ne bayan kama Abdullahi Ibrahim, mai shekaru 40 daga ƙauyen Tilde a Funakaye, a ranar 23 ga watan Nuwamba 2025. An harbe manomi saboda rikici kan filin kiwo a Borno DSS ta kama likitan da ke duba ’yan bindiga a dazukan Kwara An kama shi ne bayan samun bayanan sirri kan hulɗa da masu satar shanu. Abdullahi, ya amsa cewa yana da hannu a garkuwa da mutane tare da bayyana sunayen waɗanda suke aikata laifin tare. A cewar kakakin...
It might be a daunting experience because making professional voiceovers may seem like a challenging process, particularly when you either do not want to use your own voice or you lack access to audio equipment with higher quality. Fortunately, CapCut PC makes this whole process easier with its strong text to speech AI services. YouTube recordings, educational tutorials, brand explanation, social media, don’t matter: CapCut provides the flexibility to cut a clean, professional, natural-sounding narration within a matter of minutes. You will also get to know in this article how to incorporate an AI avatar into your content to achieve even more compelling outcomes. Why Use CapCut PC for Voiceovers? Voiceovers have traditionally involved the use of microphones, silence, and...
Rikici kan filin kiwo tsakanin wani makiyayi da wani manomi ya yi sanadin mutuwar wani manomi mai shekaru 32 a kauyen Muva da ke cikin karamar hukumar Askira/Uba a jihar Borno. Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa, a ranar 2 ga watan Disamba, 2025, da misalin karfe 4:00 na yamma, Alhaji Usman, wanda ke kiwon shanu, ya samu rashin jituwa da Jauro Ishaya mai shekaru 43, kan rikicin filin kiwo. A cewar majiyar, yayin takaddamar ne aka zargi Jauro Ishaya da harba bindigar gida wadda ta sami Alhaji Usman a ciki, lamarin da ya yi sanadin mutuwarsa. An garzaya da wanda abin ya shafa zuwa babban asibitin Askira, amma likitoci suka tabbatar da mutuwarsa nan take. Rundunar ’yan sandan...
Hukumar Tsaro ta DSS ta kama wani likita da ake zargin yana ba da magunguna tare da kula da ’yan bindiga masu garkuwa da mutane da ke wasu sassan jihar Kwara. An kama wanda ake zargin, wanda ba a iya gano sunansa ba a lokacin rahoton, a yankin Jebba bayan rahotannin sirri sun nuna cewa wasu masu safarar kaya suna kai magunguna daga Sakkwato domin kula da ’yan fashin daji da suka samu raunuka a dazukan jihar. Kakakin majalisar dokokin Ribas da takwarorinsa 16 sun fice daga PDP zuwa APC An kashe matashi yayin rikici a wajen raɗin suna a Bauchi Majiyoyin tsaro sun ce da dama daga cikin waɗannan ƙungiyoyin masu laifi sun samu raunukan harbin bindiga a fafatawar...
Kakakin Majalisar Dokokin jihar Ribas, Martin Amaewhule tare da mambobin majalisar su 15 sun sanar da sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC. Amaewhule ya bayyana shawarar ’yan majalisar ne a zaman majalisa na ranar Juma’a, inda ya ce akwai abin da ya kira “rarrabuwar kai a fili” a cikin PDP wanda ya sa suka yanke wannan shawara. Muna tafe da karin bayanai…
Kasashen Iran da Pakisatan sun amince sun dawo da zirga-zirgan jiragen kasa tsakanin birnin Istambul na kasar Turkiyya zuwa birnin Tehran na kasar Iran da kuma birnin Islamabda na kasar Pakistan a cikin wannan shekarar. Kamfanin dillancin labaran Ip na kasar Iran yanakalto jakadan kasar Iran a Islamabad Dr RezaAmiri Moghaddam yana fadar haka a lokacin ganawarsa da ministan zirga-zirgan jiragen kasa na kasar Pakisatan Mohammad Hanid Abbasi a birnin Isla,abad. Ya kuma kara da cewa zasu farfado da layin dogon a cikin wannan shekara ta 2025 sannan karkashin tsarin nan na ITI masu jigilar kaya da kuma na fasinja. Labarin ya kara da cewa idan hakan ya tabbata, wannan zai farfado da daya daga cikin layukan dogo masu muhimmanci...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baghaei ya yi tir da takunkuman tattalin arzikin da kasar Amurka take ci gaba da dorawa JMI na shekaru masu yawa. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bada nakalto Baghaei yana fadar haka a dai dai ranar tunawa da ranar haramcin takunkuman tattalin arziki na bangare guda ta kasa da kasa wacce ba’a dade da samar da ita a farkon wannan shekarar. Isma’el Baghaei ya bayyana haka ne a shafinsa na X a jiya Alhamis, inda yayi tir da Amurka wace ta fara fara dorawa JMI takunkuman tattalin arziki tun fiye da shekaru fiye da 40 da suka gabata. Kuma hakan take hakkin bil’adama. Yace a farkon wannan shekarar ne dai...
Shugaban kasar Amurka Donal Trump wanda ya jagoranci taron rattaba hannu kan yarjeniyar sulhuntawa da kuma kawo karshen yakin gabacin Kongo tsakanin shugaban kasar Rwanda Paul Kagame da tokwaransa na kasar Kongo Felix Tsetsekedi a birnin Washington a jiya Alhamis. Shafinyanar gizo na labarai ‘AfricaNews” ya bayyana cewa, shuwagabannin biyu sun rattaba hannun kan wannan yarjeniyar ne a gaban kafafen yada labarai da dama a duniya. Kuma a ganin masana shugaba Trump yana neman suna ne kawai da wannan yarjeniyar. Saboda babu tabbas kan cewa zaman lafiya zai dawo yankin Kivu na gabacin kasar Kongo. Banda haka, sun bayyana cewa hatta a dai dai lokacinda ake bikin rattaba hannu a kan yarjeniyar akwai labaran da suke tabbatar da cewa ana...
Shugaba Bola Ahmad tinubu na tarayyar Najeriya ya nada wasu karin jakadu 65 wadanda suka hada da sanatoci masu ci da kuma tsoffin gwamnoni har’ila yau da kwararrun jakadu. Jaridar Premium times ta Najeriya ta bayyana cewa shugaban ya aikawa majalisar dokokin kasar wasika dangane da hakan, wasika wacce shugaba majalisar dattawa Godswill Akpabio ya karanta a gaban sanatoci a jiya Alhamis. Kafin haka shugaban ya gabatar da sunayen wasu yan siyasa 3 don nadasu jakadu. A cikin wasikar shugaban yace mutane 34 daga cikinsu kwararrun jakadune, sannan sauran 31 yan siyasa ne. Daga cikin wadanda shugaba yanada har da tsohon shugaban hukumar zabena kasar (INEC) Farfesa Mahmood Yakubu) sauran sun hada tsoffin gwamnonin jihohin. Enugu, Abia, tsohon mataimakin gwamnan...
Pars Today – Vladimir Putin ya yi tafiya zuwa Indiya don ƙarfafa dangantakar ƙasashen biyu. Vladimir Putin, shugaban Rasha, ya isa New Delhi a ranar Alhamis, 4 ga Disamba, a ziyararsa ta farko zuwa Indiya tun bayan fara yakin Ukraine a 2022. Ziyarar ta kwanaki biyu na da nufin zurfafa haɗin gwiwa tsakanin tsaro da kasuwanci tsakanin ƙasashen biyu. Putin yana tare da wata babbar tawaga wacce ta haɗa da ministan tsaron Rasha. Ana sa ran zai halarci wani cin abincin dare na sirri tare da Firayim Ministan Indiya Narendra Modi, sannan tattaunawa ta hukuma da zaman tattalin arziki, gami da taron kolin shekara-shekara na 23. A lokacin ziyarar, ana sa ran ɓangarorin biyu za su sanya hannu kan yarjejeniyoyi...
Wani matashi mai shekaru 20, Haruna Haruna, ya rasa ransa bayan fada ya barke a lokacin bikin radin suna a ƙauyen Kwata da ke Karamar Hukumar Warji ta Jihar Bauchi. Bayanai sun ce lamarin ya faru ne a ranar Talata lokacin da sa’insa ta barke tsakanin wasu matasa ta rikide ta zama fada, wanda ya bar Haruna cikin rashin hayyacinsa. Tinubu ya naɗa tsohon kantoman Ribas da Dambazau a matsayin Jakadun Najeriya ’Yan sandan Borno sun kama matashin da ake zargi da kashe makwabciyarsa da wuƙa “Wani matashi mai shekaru 20, Haruna Haruna na ƙauyen Kwata, Karamar Hukumar Warji, Jihar Bauchi, ya riga mu gidan gaskiya bayan rikici mai tsanani da ya barke a bikin radin suna a ranar 2...
Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Esmail Baghaei ya yi Allah wadai da kakkausar murya da sanarwar bayan taron shugabannin Kasashen Yankin Tekun Farisa (GCC) wanda suka fitar game da tsibiran Iran guda uku. Baghhaei ya nuna takaici kan dagewar da kungiyar GCC ta yi kan maimaita ikirari maras tushe na Hadaddiyar Daular Larabawa game da tsibiran Abu Musa, Greater Tunb, da Lesser Tunb na Iran. Ya yi Allah wadai da ikirarin da ke cikin sanarwar karshe ta taron kolin GCC karo na 46 game da wadannan tsibirai na kasar Iran, yana mai jaddada cewa Abu Musa, Greater Tunb, da Lesser Tunb muhimmin bangare ne na yankin Iran kuma duk wani ikirari sabanin hakan ba shi da inganci, kuma a bayyane...
Wani matashi mai shekaru 20, Haruna Haruna, ya rasa ransa bayan fada ya barke a lokacin bikin radin suna a ƙauyen Kwata da ke Karamar Hukumar Warji ta Jihar Bauchi. Bayanai sun ce lamarin ya faru ne a ranar Talata lokacin da sa’insa ta barke tsakanin wasu matasa ta rikide ta zama fada, wanda ya bar Haruna cikin rashin hayyacinsa. Tinubu ya naɗa tsohon kantoman Ribas da Dambazau a matsayin Jakadun Najeriya ’Yan sandan Borno sun kama matashin da ake zargi da kashe makwabciyarsa da wuƙa “Wani matashi mai shekaru 20, Haruna Haruna na ƙauyen Kwata, Karamar Hukumar Warji, Jihar Bauchi, ya riga mu gidan gaskiya bayan rikici mai tsanani da ya barke a bikin radin suna a ranar 2...
A ranar Alhamis ne fadar shugaban kasar Afirka ta Kudu ta sanar da cewa kasar za ta dauki hutu daga halartar tarukan G20 yayin da shugaban Amurka Donald Trump ke jagorantar kungiyar a karkashin tsarin karba-karba, bayan da gwamnatinsa ta tabbatar da cewa ba za ta gayyaci Afirka ta Kudu a taro mai zuwa ba. Amurka ta karbi shugabancin G20 na karba-karba a makon da ya gabata, bayan kauracewa taron da Shugaba Cyril Ramaphosa ya shirya a Johannesburg. “A wannan lokacin a shekara mai zuwa, Birtaniya za ta karbi shugabancin G20. Za mu iya shiga cikin batutuwan da suka shafi duniya,” in ji mai magana da yawun Ramaphosa, Vincent Magwenya. “A yanzu haka, za mu dakatar da shirye-shiryen kasuwanci har...
Microsoft Za Ta Fuskanci Hukunci Kan Waimaka Wa Isra’ila A Laifukan Da Take Aikatawa Kan Falasdinawa
Microsoft na fuskantar matsin lamba da kuma matakin shari’a saboda samar wa Isra’ila fasahar da ake amfani da ita wajen take hakkin Falasdinawa a Gaza da Yammacin Kogin Jordan. A cikin wata budaddiyar wasika da aka aike wa kamfanin a ranar 2 ga wannan watan, wata kungiyar lauyoyi ta kasa da kasa ta yi gargadin cewa Microsoft da shugabanninta za su iya fuskantar hukunci na shari’a kan taimakawa da kuma tallafawa laifukan da aka aikata wa fararen hula Falasdinawa. Eric Saib, mai kula da harkokin ci gaban kafofin watsa labarun kasa da kasa na Cibiyar Larabawa don Ci gaban Kafafen Yada Labarai, ya jaddada cewa watannin baya-bayan nan sun nuna karara cewa ana amfani da ayyukan kamfanin wajen take hakkin...
Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta sanar da cewa tana sake duba dangantakarta da Tanzania a daidai lokacin da ake samun abin da Amurka ta kira damuwa game da ‘yancin addini, ‘yancin fadin albarkacin baki, cikas ga ayyukan zuba hannayen jarin Amurka, da kuma cin zarafin fararen hula. Amurka ta bayar da gargadin tsaro ga Amurkawa a kasar da ke Gabashin Afirka bayan babban zaben watan Oktoba, wanda zanga-zangar ta mamaye shi. Kungiyoyin kare hakkin dan adam, jam’iyyun adawa, da Majalisar Dinkin Duniya sun bayar da rahoton cewa an samu matsaloli bayan zaben, duk da cewa dai gwamnatin kasar ta musanta alkaluma na asarorin da aka samu, tana mai kiransu da alkalumman karin gishiri. Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ce kasar...
Fadlallah Na Hizbullah Ya Yi Kiran Hadin Kai A Tsakanin Musulmi Da Larabawa Domin Fuskantar Kalubale
Hassan Fadlallah wanda dan majalisar kasar Lebanon ne daga kungiyar Hizbullahy a bayyana cewa; gwargwadon yadda ake ja da baya a gaban makiya, suke kara samun karfin gwiwa,don haka da akwai bukatar hadin kai a tsakanin kasashen larabawa da na musulmi domin fuskantar kalubalen dake gaba. Shi dai Hassan Fadlalalah yana halartar taron majalisun kasashe nahiyar Asiya da ake yi a birnin Mashhad na Iran, ya bayyana cewa: Laifukan da ‘yan sahayoniya suke yi, yana nuni ne da yadda su ka kai koli wajen nuna keta a kan kasashen da suke da cin gashin kai da ‘yanci, da hakan yake a matsayin karya zaman lafiya da sulhu na duniya. Fadlallah ya kuma yi jinjina ga jamhuriyar musulunci ta Iran akan...
Rahotanni daga kasar Lebanon sun ambaci cewa da marecen yau jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra’ila sun kai hare-hare a garuruwan Mahruna,jibaa, Bar-ishit da Majadil dake kudancin Lebanon. Hare-haren sun rusa gidaje da dama na garuruwan da su ka kai wa harin. Wannan harin dai yana faruwa ne kwana daya bayan da Lebanon ta aike da wakili a cikin kwamitin ttataunawa da ‘yan sahayoniyar da tsohon jakadan kasar Simon Karam yake wakiltarta. Tashar talabijin din almanar ta ambato ofishin karamar hukumar garin Mahrunah tana yin tir da wannan harin wanda ya rusa wani gida na fararen hula a tsakiyar unguwa. Bayanin ya ci gaba da cewa; Kai hari a tsakiyar unguwar fararen hula keta dokokin ‘yan adamtaka na duniya. Kuma abinda...
Kungiyoyin kare hakkin bil’adama na kasar Canada sun shigar da kara ga jami’an ‘yan sandan kasar, da kuma ma’aikatar shari’a da su kama tsohon Fira ministan haramtacciyar kasar Isra’ila Ehud Olmert da kuma ministan harkokin waje Tzipi Livni bisa rawar da su ka taba a baya a laifukan yaki a Gaza a tsakanin 200-2009. Kungiyoyin sun bukacin ganin an fitar da sammacin kamo ‘yan sahayoniyar biyu a bisa dogaro da dokokin kare hakkin dan’adama da laifukan yaki na kasar Canada, saboda kasar tana karkashin yarjejeniyar Geneva ta 4 da ta bukaci kasashe su hukunta masu irin wadannan laifukan. Bugu da kari, kungiyoyin sun ce Olmert wanda ya yi fira minista daga 2006 zuwa 2009, shi ne mai rike da mukami...
Kafafen watsa labarun “Isra’ila” sun ce an kashe shugaban kungiyar ‘yan daba na Gaza Yasi Abu Shaba,ba tare da an tantance wanda ya yi hakan ba. Kafafen watsa labarun “Isra’ilan”sun ce; Kashe Abu Shabab wani mummunan labari ne ga Isra’ila.” Tashar talabijin 12 ta ambato wani jami’in tsaro yana cewa; Abu Shabab ya cika ne a asibiti saboda raunin da ya samu daga harbin da aka yi masa a wani sabani na cikin gidan.” Sai dai wata majiyar ta ce, da akwai yiyuwar kungiyar Hamas ce ta kashe shi, bayan da ta tattara bayanai akansa daga makusantansa. An fara jin duriyar Abu Shabab ne a ranar 30 ga watan Mayu 2025 bayan da kungiyar Hamas ta watsa wani faifen bidiyo...
Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnatin Jihar Jigawa ta gudanar da bikin bude tayin bada kwangilar samar da wutar lantarki a wasu garuruwa dake kananan hukumomin Jihar. A lokacin da yake jawabi a yayin gudanar da bikin daya gudana a sakatariyar Jihar dake Dutse, Shugaban hukumar, Injiniya Zubairu Musa ya bayyana cewar tayin bada kwangilar samar da wutar da gyara da fadadawa gami da kammala wasu ayyukan za a yi sune a garuruwa 17. Kazalika, Injiniya Zubairu Musa, yace wannan na daga cikin kudirori 12 na Gwamna Umar Namadi na hada wutar lantarki a kanana da matsakaitan garuruwan jihar da basu da wuta. A cewar sa, garuruwan da za’a samar da wutar lantarkin a Dutse sun hada da Sabuwar Takur...
Rundunar ’yan sandan jihar Borno ta kama matashin nan da ake zargi da kashe makwabciyarsa a unguwar Shuwari II, a garin Maiduguri babban birnin jihar, ta hanyar daba mata wuka. Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, ASP Nahum Kenneth Daso, ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:00 na dare a ranar Talata. Amurka za ta hana ’yan Najeriyar da ake zargi da yi wa Kiristoci kisan kiyashi biza Jirgin fadar shugaban ƙasa ya ƙi sayuwa wata 5 bayan saka shi a kasuwa Ya ce ana zargin matashin ne mai shekaru 17 da aka fi sani da Amir, wanda makanike ne da kashe matar ta hanyar daba mata wuka. Wani makwabcin wajen ya shaida cewa ana zargin matashin ne...
Ƙasar Amurka ta yi barazanar sanya takunkumin izinin shiga kasarta ga ’yan Najeriyar da aka gano suna ɗaukar nauyi ko goyon bayan ayyukan da ke take ’yancin yin addini da yi wa Kiristoci kisan kiyashi. Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio, ya bayyana haka a cikin wani saƙo da ya wallafa a shafin X, inda ya ce Amurka na ɗaukar mataki mai ƙarfi kan munanan ayyuka da tashin hankali da ake yi wa Kiristoci a Najeriya da sauran sassan duniya. NAPTIP ta daƙile yunƙurin safarar mutum 7 daga Kano zuwa Saudiyya Na gana da Tinubu kan Kanu ba batun sauya sheƙa ba — Gwamnan Abia “Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka (@StateDept) za ta takaita bizar Amurka ga waɗanda suka san da...
Jagoran Juyin Juya Halin Musuluncina Iran, Ayatollah Seyyed Ali Khamenei, ya bayyana cewa Musulunci yana bai wa mata matsayi mai girma da daidaito tsakanin maza a rayuwar zamantakewa da siyasa, yayin da yake Allah wadai da “al’adun kasashen Yammacin duniya ” game da mata. “Maganar Alkur’ani game da asali da halayen mata ita ce mafi girma,” in ji Ayatollah Khamenei a ranar Laraba, a wata ganawa da dubban mata daga yankuna daban-daban na kasar. A cikin jawabinsa, Jagoran ya yi nuni da halayen Fatemeh Zahra (amincin Allah ya tabbata a gare ta), ‘yar Annabi Muhammad (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da zuriyarsa), yana yabon matan Iran saboda “suna samun wahayi daga irin wannan haske mai...
Iran ta yi watsi da zarge-zargen da wakilan gwamnatin Isra’ila da gwamnatin Yemen mai murabus suka yi a zaman taron hukumar kula da harkokin teku ta duniya (IMO) karo na 34. A wata wasika da ta aike wa Sakatare Janar na IMO Arsenio Dominguez, Ofishin Jakadancin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a kungiyar da ke Landan a ranar Laraba, ya bayyana damuwarsa game da yadd Isra’ila kesarrafa hukumar IMO don manufofinta. Wasikar ta jaddada cewa wannan dabi’a tana wargaza kwarewar hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya a harkokin teku. Tawagar Iran ta kara da cewa wadannan zarge-zargen marasa tushe wani bangare ne na wani tsari da Isra’ila ke kokarin lalata dokokin kasa da kasa, raunana hanyoyin da suka shafi bangarori daban-daban, da...
MDD ta bukaci a kawo karshen mamayar Isra’ila a Falasdinu da kuma janyewa daga Tuddan Golan na Siriya
Babban taron Majalisar Dinkin Duniya ya amince da wasu kudurori guda biyu da ke kira da a kawo karshen mamayar Isra’ila a Falasdinu da kuma Tuddan Golan na Siriya. Djibouti, Jordan, Mauritania, Qatar, Senegal, da Falasdinu ne suka gabatar da daftarin kuduri game da Falasdinu. Kasashe 151 ne suka kada kuri’a a kan hakan, yayin da kasashe 11, ciki har da Amurka, suka ki amincewa da hakan, sai kuma wasu 11 da suka ce ba ruwansu. Kudirin da aka amince da shi ya sake tabbatar da alhakin Majalisar Dinkin Duniya game da batun Falasdinu tare da yin kira da a kawo ƙarshen mamayar Isra’ila a yankunan da aka mamaye tun 1967, yayin da yake goyon bayan samar da kasashe guda...
Rundunar Sojan Ruwa ta IRGC ta fara wani atisayen soji a yankin kudancin Iran a Tekun Fasha, wanda ya kunshi rundunonin sojoji da dama. An yi wa atisayen lakabi da “Eightedar” (Ikon Kasa), domin girmama kwamandan da ya yi shahada Mohammad Nazeri, wani babban jami’in sojin ruwa na IRGC. Ana gudanar da atisayen a cikin ruwan Tekun Fasha, yankin tekun Nazeat (Abu Musa, Greater Tunb, Lesser Tunb, da Tsibiran Siri), Mashigar Hormuz. Abin lura ne cewa Mohammad Nazeri shi ne kwamandan rundunonin kwamando na rundunar sojin ruwa ta IRGC. An san shi sosai a Iran saboda rawar da ya taka wajen kama ma’aikatan jirgin ruwan Amurka goma—maza tara da mace daya—wadanda suka shiga ruwan Iran a ranar 12 ga Janairu,...
Aƙalla mutum shida ne suka rasu, yayin da wasu 13 suka jikkata, bayan wata bas ɗauke da nakasassu ta yi hatsari a kan hanyar Lokoja zuwa Okene. Waɗanda abin ya shafa suna komawa Okene ne bayan halartar bikin Ranar Nakasassu ta Duniya ta 2025 a Gidan Gwamnatin Jihar da ke Lokoja. Jirgin fadar shugaban ƙasa ya ƙi sayuwa wata 5 bayan saka shi a kasuwa ’Yan sanda sun kama mutum 28 kan zargin lalata mata da yara a Yobe An garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa asibitoci daban-daban a jihar, inda suke ci gaba da samun kulawa. Kwamishinan Harkokin Sadarwa na Jihar Kogi, Kingsley Femi Fanwo, ya ce wannan hatsari abun baƙin ciki ne ga gwamnati da jama’a. Ya ce...
Dan wasan taekwando na kasar iran Abolfazl zandi ya samu lambar yazo ta zinariya a ranar farko ta gasar takwando ta duniya da ake gudanarwa a birnin Nairobi na kasar kenya , kuma ita ce lambar yabonsa na biyu a cikin kwanaki 35, Gasar tana gudana ne a filin wasa na moi international sport center dake kasar kenya kimanin yan wasa 452 da suka fito daga kasashen duniya 75 ne ke halartar gasar, kuma iran ta shiga gasar da yan wasa guda 16 da suka hada da mata 6 da kuma maza 8 da za su yi tasu karawar acikin kwanaki 4. Zandi da ya samu lambar yabo ta zinairiya a baya –bayan nan ya nuna gwaninta da ya cancanci...
Rahotanni sun bayyana cwa kungiyar Hamas tace za ta mikawa isra’ila sabon samfurin jikin dan Adama da ta samu a arewacin gaza, bayan da isra’ila ta yi ikirarin cewa gawarwakin da kungiyar gwagwarmaya ta basu ba su daga cikin gawarwaki guda biyu da su ke rike da su da har yanzu ba’a dawo da su ba, Kungiyar ta hamas ta bayyana cewa dakarunta da hadin guiwa dakarun kungiyar jihadil Islami suna aiki tare kuma sun gano wani burbushin jikin dan adam da suke ganin yana da alaka da bayahuden da suka kama ne beneath a karkashin burabutsai a yankin beit lahia, Kuma za ta mika samfurin zuwa isra’la ta hannun babban kwamitin kungiyar bada agaji ta red cross ta ksa...
Iran Ta ce Tsaron Yankin Tekun Fasha Jan Layi Ne Da Za’a Fuskanci Mayar Da Martani Adan Aka Taba Shi
Mataimakin kwamandan dakarun kare juyin juya halin musulunci na kasar Iran ya gargadi Amurka da kawayenta game da tsaron tekun fasha da mashigar Hurmuz, yace tsaron wadannan muhimman wurare jan layi ne ga kasar iran da zata mayar da martani mai tsanin ga duk wanda ya taba su Brigadier Janal Ali Fadavi da yake bayani game da muhimmancin mashigar Hurmuz ya fadi cewa babu wata yarjejeniya da za’a yi game da samun tabbaci ga makamashi na duniya, inda sama da ganga miliya 20 take wucewa ta wannan mashigar kullum , kuma duniya ta dogara ne da makamashin na tekun fasha Janar fadavi ya bayyana cewa dakarun kare juyin musulunci na kasar iran sun shirya tsaf wajen kare wannan yankin mai...
Gamayyar Kungiyoyin kare hakkin bil adama har da palastinian center for human right sun aike da takaradar korafi ga bangaren shari’a na kasar Kanada inda suka bukaci a kamam tsohon pira ministan Isara’ila Egud Olmaert da kuma tsohowar ministan harkokin wajen isra’ila tzipi Livnin idan suka kawo ziyara birnin Toranto. Zargin yayi dadai da dokar yaki da kare hakkin bil adama da kuma laifukan yaki mai lamba 146 na yarjejeniyar janeva da ta tilasta gwamnati ta kama wadanda ake zargi da keta dokokin , Olmert da Livnin suna da zarge-zarge akan su, da tafka laifukan yaki da kuma cin zarafin dan adama a shekara ta 2008 zuwa 2009 a yankin Gaza. Olmert da Livni suna fuskantar zargi iri daya ne...
Majalisar Dattawa a najeriya ta amince da tsohon hafsan sojin kasa, Janar Christopher Musa (mai ritaya), a matsayin sabon Ministan Tsaro bayan tantance shi da aka dauki kusan awanni biyar. A lokacin tantancewar, Musa ya ce zai inganta tsaro ta hanyar hada kai tsakanin sojoji, ’yan sanda, sauran hukumomin tsaro da al’ummomi. Ya yi gargaɗin cewa ’yan ta’adda na kai hare-hare a Nijeriya ne saboda suna ganin kasar tana da arziki, Ya kuma yi alkawarin magance gibin tsaro da aka samu da kuma kara hadin gwiwa da kasashen makwabta. Ya yi nuni da cewa sojoji kadai ba za su iya magance matsalar tsaro ba, ya jaddada bukatar kyakkyawar gwamnati da goyon bayan al’umma. Sanatoci sun yaba da kwarewarsa kuma suka...
Jirgin Fadar Shugaban Kasa da Gwamnatin Najeriya ta saka a kasuwa da nufin sayarwa ya kasa samun mai saye kusan watanni biyar bayan ɗora shi a dandalin sayar da jiragen sama na duniya. A sakamakon haka, tuni ma kamfanin dillancin da ke kula da sayar da jirgin samfurin Boeing 737-700 Business Jet ya janye jerin sayar da shi daga shafinsa. ’Yan Najeriya suna da ƙwarin guiwa a kaina, ba zan ba su kunya ba — Ministan Tsaro ’Yan sanda sun kama mutum 28 kan zargin lalata mata da yara a Yobe Jaridar Punch ta rawaito cewa jirgin da a baya aka saka a shafin kamfanin, yanzu an cire shi daga kai. A cikin wata amsa ga sakon imel, Laurie Barringer...
Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya), ya ce ba zai bai wa ’yan Najeriya kunya ba, saboda ƙwarin guiwar da suke da shi a kansa. Musa, wanda Shugaba Bola Tinubu ya naɗa ministan tsaro, ya bayyana haka ne a ranar Laraba lokacin da aka tantance shi a Majalisar Dattawa. Tsaro: Gwamnonin Arewa na shirin dakatar da haƙar ma’adinai Ƙudirin dokar hukuncin kisa ga masu satar mutane ya tsallake karatu na biyu Ya gode wa Shugaban Ƙasa saboda zaɓarsa da ya yi a matsayin minista, sannan ya gode wa ’yan Najeriya saboda amincewa da suka yi da shi. Ya yi alƙawarin yin iya bakin ƙoƙarinsa domin tabbatar da zaman lafiya a ƙasar nan. Ya ce: “Da na ga irin martanin...
Gwamnonin Arewaci, na shirin dakatar da haƙar ma’adinai a wasu yankuna da ake fama da matsalar tsaro, domin daƙile ayyukan ’yan bindiga da sauran ƙungiyoyin ta’addanci. Wannan batu ya fito ne daga taron haɗin gwiwa na Gwamnonin Arewa da Majalisar Sarakunan Gargajiya da aka yi a Kaduna daga 1 zuwa 2 ga watan Disamba, 2025. ’Yan sanda sun kama mutum 28 kan zargin lalata mata da yara a Yobe Tsaro: Gwamnatin Kano za ta fara amfani da jirage marasa matuƙa a iyakokinta Shugaban ƙungiyar gwamnonin, Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na Jihar Gombe, ya ce lamarin tsaro ya kai wani mataki da ke buƙatar ɗaukar matakin gaggawa. Ya bayyana cewa wuraren haƙar ma’adinai sun zama mafakar ’yan bindiga, masu garkuwa da...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Yobe, ta ce ta samu rahoton laifuka 25 na cin zarafin mata da ƙananan yara a Ƙananan Hukumomin Jakusko, Fika, Potiskum da Tarmuwa, inda aka kama mutum 28 da ake zargi da aikata laifukan. Kakakin rundunar, SP Abdulkarim Dungus, ya ce an kama masu laifin ne cikin watanni uku da suka wuce, a wani yunƙuri na daƙile cin zarafin mata da yara a faɗin jihar. Tinubu ya san dalilin da ya sa na yi murabus daga muƙamin ministan — Badaru Ƙudirin dokar hukuncin kisa ga masu satar mutane ya tsallake karatu na biyu Daga cikin waɗanda aka kama akwai wani matashi mai shekara 23, Yusuf Garba, da ake zargi yi wa wata yarinya mai shekaru biyar...
Tsohon Ministan Tsaro, Abubakar Badaru, ya ce Shugaba Bola Tinubu ya san dalilin da ya sa ya yi murabus. Badaru, ya ajiye aiki ne a ranar Litinin, inda ya ce matsar rashin lafiya ce ta sa ya yi murabus. Ƙudirin dokar hukuncin kisa ga masu satar mutane ya tsallake karatu na biyu Tsaro: Gwamnatin Kano za ta fara amfani da jirage marasa matuƙa a iyakokinta Shugaban ƙasa ya amince da murabus ɗinsa kuma ya naɗa Janar Chris Musa a matsayin sabon Ministan Tsaro. Badaru, ya ƙaryata rahotannin da ke cewa ya yi murabus ne saboda barazanar da Amurka ta yi na ɗaukar matakin soji kan Najeriya game da zargin kisan Kiristoci. “Ina so na bayyana a fili cewa wannan labari...
Majalisar Dattawa ta amince da wani sabon ƙudiri da ke neman a gyara dokar yaƙi da ta’addanci, domin a ɗauki garkuwa da mutane a matsayin babban laifi na ta’addanci. Ƙudirin, wanda Sanata Opeyemi Bamidele ya gabatar, ya tanadi hukuncin kisa ga duk wanda aka kama da laifin satar mutane, ba tare da wata zaɓin tara ba. Tsaro: Gwamnatin Kano za ta fara amfani da jirage marasa matuƙa a iyakokinta Gobara ta ƙone kasuwar katako a Abuja Sanata Bamidele, ya ce ƙudirin ya yi daidai da yunƙurin gwamnati da majalisa na kawo ƙarshen matsalar tsaro a ƙasar nan. Yayin gabatar da ƙudirin, ya ce garkuwa da mutane na ƙara yawaita, kuma ƙungiyoyin miyagu na amfani da shi wajen tara k6udi, abin...
Jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khaminae ya bayyana cewa addinin musulunci ya daukaka matsayin macce ya kuma bada matsayin guda da maza a fagagen zamantakewa da siyasa, ya kuma yi watsi ya akidar kasashen yamma wadanda suka kaskasntata suka maida ita kayan aika don cimma bukatatun wasu. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Jagoran yana fadar haka a wani jawabin da ya gabatar a taron dubban mata daga yankunan daban daban na kasar a yau laraba a nan Tehran. Imam Khaminae ya ce, mata a Iran suna koikoyon Fatimah Azzahra (s) diyar manzon Allah (s) don haka suka kama hanyar daukaka wanda alah ya bawa mata. Fatima (s) makaranta ce ga mata kuma daukaka...