Daga Aliyu Muraki 

Gwamna Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa ya ce gwamnonin Arewa sun amince su sayi na’urorin zamani na tsaro da kuma daukar matasa aiki don tallafawa ayyukan tsaro domin magance matsalolin rashin tsaro a yankin.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a zaman Majalisar Zartarwa ta Jihar da aka gudanar a Lafia, babban birnin jihar.

Gwamna Abdullahi Sule, wanda shi ne shugaban kungiyar gwamnonin Arewa ta Tsakiya, ya ce an cimma wannan matsaya ce a taron gwamnonin Arewa da aka yi a Kaduna kwanan nan.

 

A cewarsa, gwamnonin Arewa sun amince cewa kowace jiha za ta rika bada gudummawar Naira Biliyan Daya a kowane wata na tsawon shekara guda domin samar da kudin da zai taimaka wajen magance matsalolin tsaro a yankin.

Ya ce kwamitin gwamnonin Arewa zai gina sakatariyarsa a Kaduna, inda gwamnonin Arewa goma sha tara suka bayar da Naira Miliyan Dari Dari na tsawon shekara guda.

Gwamna Abdullahi Sule ya kuma yi karin bayani kan dakatar da ayyukan hakar ma’adinai a jihar Nasarawa, inda ya bayyana cewa wannan dakatarwar ba haramta dukkan ayyukan hakar ma’adinai na tsawon watanni shida ba ce, an dakatar da bayar da sabbin lasisi ne, har sai an kammala tantance sahihan masu hakar ma’adinai.

Manufar tantancewar ita ce gano masu hakar ma’adinai na gaskiya da kawar da masu hakar ma’adinai na fasa-kwauri wadanda ba sa kawo kudaden shiga ga jihar, tare da haifar da matsalolin tsaro.

Gwamnan ya bayyana cewa kasancewar masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba a jihar ta zama mafakar ‘yan bindiga, masu garkuwa da mutane da sauran matsalolin tsaro, wanda hakan ya sa aka bukaci tsauraran dokoki da ingantaccen tsari.

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Arewa Gwamnoni Tsaro masu hakar ma adinai gwamnonin Arewa

এছাড়াও পড়ুন:

Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Jigawa ta Kare Kasafin Kudin 2026 a Gaban Majalisa

Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Jigawa ta ce za ta gudanar da aikin shigar da sabbin dokokin jihar cikin kundin bayanan dokoki da aka yi a jihar.

Babban Sakataren ma’aikatar, Barrister Lawan D. Baba, ya bayyana haka lokacin da ya ke kare kiyasin kasafin kudin sabuwar shekara ta 2026 a gaban kwamatin harkokin shari’a na majalisar dokokin jihar Jigawa.

Barrister Lawan D. Baba ya bayyana cewa ma’aikatar ta yi kiyasin kashe naira milyan 311 da dubu 847 a kasafin kudin sabuwar shekara.

Babban sakataren yace za su mayar da hankali ga batun kawar da jinkiri wajen gudanar da shari’o’i domin karfafa matakan samun shari’a cikin sauri ga al’ummar jihar.

A nasa jawabin, Shugaban kwamatin harkokin shari’a na majalisar dokokin jihar Jigawa kuma wakilin mazabar Hadejia, Barrister Abubakar Sadiq Jallo, ya jaddada bukatar wanzuwar dangantakar aiki tsakanin kwamatin da bangaren shari’a domin inganta aikin shari’a a kotu.

Kazalika, magatakardar Babbar kotun jihar da sakataren hukumar kula da ma’aikatan shari’a da kuma sakataren hukumar bada tallafin shari’a su ma sun kare na su kiyasin kasafin kudaden a gaban kwamatin.

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ASUU-SSU Ta Zargi VC Da KaryDokokin Jami’ar Jihar Sakkwato
  • Matsalar Tsaro: Tinubu Ya Yi Ganawar Sirri da Gwamnonin Jihohi Shidda
  • Rashin Tsaro: Gwamnatin Tarayya ta gaza — Kwankwaso
  •  Macron Na Faransa Ya Yi Wa Najeriya Alkawalin Taimakawa Akan Matsalolin Tsaro
  • Yadda muka daƙile yunƙurin juyin mulki a Benin — Sojin Saman Najeriya
  • Tawagar Majalisar Amurka ta iso Nijeriya Don Bincika Zargin Tauye Haƙƙin Addini
  • Ma’aikatar Ayyuka da Sufuri ta Jigawa Ta Bada Kiyasin Kasafin Kudi na Sama da Naira Biliyan 161
  • Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Jigawa ta Kare Kasafin Kudin 2026 a Gaban Majalisa
  • Akwai hannun ƙasashen waje a rashin tsaron Najeriya —Sheikh Gumi