Wannan yana faruwa sosai gaskiya, kuma ƙarshe ba a wayewa da lafiya gaskiya. Masu yi gaskiya tun wuri su daina wallahi, dan aure ya sha mutuwa ta sanadin haka ƙarshe azo ana nadama mara amfani. Sosai ana samun gagarumar matsala tsakanin ma’aurata zargi ya shiga tsakani, daga nan ma dai wani aure ka ji ya mutu.

Su yi wa kansu faɗa, su daina gaskiya.

 

Sunana Haj. Maryama Ahmad, daga Jihar Kaduna:

Wannan matsaloli suna faruwa sosai, kuma rashin tunani ne yake janyo hakan. Dalili kuwa ko da namiji ba shi da wannan tunanin na soyayya da wata to, kin ƙirƙirar masa ke da kanka, kin riga da kin nemo masa hanyar da zai riƙa samun damar bibiyar wasu. Haka lambar da za ki ara ko da ace ita macen ba ta bibiye shi ba, watarana zai ji yana son bibiyar lambar musamman lokacin da ki ka ɓata masa, sharrin ɗa namiji na da yawa ya san hanyoyin da dama waɗanda zai bi ya tursasa ita wannan me lambar ko da kuwa ba ta buƙatar sauraronshi har sai ya cimma burinshi. Kin ga kenan kin kawo wa kanki da kanki wata masifar kuna zaune lafiya ke da mijinki, Allah dai ya kyauta. Wannan darasi ne babba musamman ga ƴ an’uwa mata manya da yara, dan wata babbar kamar ƙaramar yarinya haka take. Allah ya sa mu dace.

 

Sunana Fadila Lamiɗo daga Jihar Kaduna:

In ban da ganganci akan wani dalili za ki ɗauki ‘number’ mijinki ki saka a wayar wata? wannan tamkar bawa mage ajiyar kifi ne, idan ma kina tunanin kin goge ‘number’ bayan kin gama ne shi mijin naki yau da gobe kina masa haka zai iya bin bayan ‘number’ don shi ba walliyi bane, garin neman gira sai a rasa ido. Ina kira ga mata su guji tsananta buncike, su sa a zuciyarsu kishiya ƙaddara ce kuma bawa baya iya gujewa ƙaddararsa. Su mayar da hankali wajen roƙon Allah abin da suke so wa kan su na alheri, in sha Allahu Allah zai shiga cikin lamarinsu, ba tare da sun ɗaga wa kansu hankali ba, wajen binciko abin da ka iya kawo masu rashin kwanciyar hankali.

 

Sunana Princess Fatimah Mazadu, daga Jihar Gomben Nigeria:

Tirƙashi kin san wauta da dolanci wallahi wannan shi ne, kat! ah to, in ba wauta ba ke kin isa ki gama sanin ɗa namiji? Ko chat da neman hanyoyi ta zamani za ta isar miki ki gane halayen mijinki ko sanin ƴ an matanshi ko neman aurenshi da makamantansu?. Ai tonon asiri ne da rashin sanin zafin kai, da ƙoƙarin saka zargi tsakanin zamantakewarku. Ai kira da babbar murya in har akwai masu niyyya ma wallahi kar su kuskura, dan wata in ta yi ta wanye lafiya, wata gidansu za a korata. Shurme ne sosai ace wai mace tana bibiyar namiji akan dole ta san ainihin abun da ke tafiya a rayuwarshi, an ce mana mazan daƙiƙai ne? ai sun fi mu wayewa a wannan fannin. Tunda dai ban taɓa jin an ce ga mace ta ƙirƙiri Tiktok ko Facebook ko Instagram ba, kawai ki kasance mai yadda da shi akowani hali idan bai saɓawa addininmu. Matsaloli kam, ai ba adadi dan garin gwadashi wallahi za ki gwado bala’i a ƙoƙarinki na ki san meke tafiya, kawai ana cikin hira ya ce misali “yau ina komawa ma zan saki matata tun da zan mallakeki…” Dan Allah ya za ki yi?  Shin za ki tonawa kanki asiri ne, ko za ki cigaba da chat ɗin?,  ko daga ya dawo za ki tare shi?, ko za ki hau haɗa kayanki ne?, kin ga wannan ƙaramin misali ne, wallahi mata su kiyayye wannan shurme ne. Matsaloli kamar; rashin kwanciyar hankali, zargin juna, nadama, da-na-sani, banzar aƙida.

 

Sunana Lawan Isma’il (Lisary), Rano LGA Jihar Kano:

Idan za a yi ba mai zurfi ba, kuma za a yi gwajin da zuciya ɗaya bada niyyar tayar da fitina ba a nawa fahimtar babu matsala. Akwaisu matsaloli kam, idan har ita cen ta fiye gwajin mai zurfi. Shawarata a nan ita ce, kawai duk wata mace tana yi wa mijinta kyakykyawan zato musamman akan ƙarin aure, domin Allah ne da kansa ya halastawa namiji ya auri mace har guda huɗu amma fa idan zai yi adalci, shi kuma adalci ubangijinmu ne kaɗai mai yinsa daidai. Allah kasa mu dace amin.

 

Sunana Hadiza Ibrahim D. Auta, Ɗaura-Namoda Jihar Zamfara:

Babban ƙalubale ne ga mata masu irin wannan halin bin diddigi, ko ga namiji ballantana ga mace wadda ba ta isa ta saka ko ta hana ba. Kira na ga masu irin wannan halin su daina gwajin su tsayar da hankalinsu a kan abin da suka gani zahiri. Saboda Allah da kansa ma ya ce kada mu tsananta bincike, gudun garin tone-tone kaza ta tono wuƙar yanka ta. Akwai illoli masu tarin yawa dangane da matsalolin da wannan gwajin yake haifarwa ga masu riƙo da shi a matsayin wayewa, ko babban makamin da suke riƙo da shi domin tabbatar ko gano; ana son su ko ba a son su, kuma mijinsu yana kula wasu matan ko babu ruwansa da su. Saboda ba a gwada namiji da mace komai muninta. Don akwai wata da ta taɓa saka ƙawarta ta yi wa saurayinta gwajin; daga haka aure ya ƙullu a tsakaninsu ya bar budurwarsa ta asali ya auri ƙawarta. Haka ma ƙawa ta taɓa kwace mijin ƙawarta a irin wannan gwajin daga wasa. Shawarata ga masu yi kawai su daina, a wannan zamanin da muke ciki miji ko saurayi duka ɓoye su ake yi kamar an samu kuɗi. Wata ko ba a saka ta yin gwajin ba gaban kanta take yi, idan ta samu dama sai dai ƙawar ta ji labari a sama zancen ya sauya, mai son ta ya koma kan ƙawarta ko kuma ƙawarta za ta aure mata miji.

 

Sunana Muktari Sabo, Jahun A Jihar Jigawa:

Mata mutanenmu lallai hakan tana faruwa wato mace take bibiyar mijinta ta hanyoyi mabambanta ciki kuma har ta waya. Kiran da zan yi akan haka shi ne, mata su ji tsoron Allah kuma su sani bibiyar ba abin da za ta hana wanda Allah ya sa zai faru. Akwai matsaloli; na farko dai ta ɗorawa kanta rashin kwanciyar hankali, sannan hakan zai iya haifar mata matsala tsakaninta da mijinta. Shawara a nan ita ce mata masu wannan hali su daina, domin yin hakan ba zai hana ayi musu abin da suke tsoro ba wato kishiya.

 

Sunana Hafsat Sa’eed, daga Jihar Neja:

A nawa tunanin hakan bai kamata ba, mace ta gwada kiran mijinta matsayin wata daban, duk abin da ya je ya zo kuwa ita ta jaho. Dan wannan kowaye ya ji ya san dole a samu matsala a gaba, kuma abin da macen ke tsoro za ta iya janyo shi da kanta. Idan ma zargi take kan yana aikata wani abun, sai ta barshi shi da ubangijinsa ya fi mata.

 

Sunana Hauwa Abubakar Sarki, daga Suleja Jihar Neja:

Kishi na iya sa mace ta aikata komai, duk yadda mace ta kai ga bin diddigin mijinta da sanya ido akan al’muransa, wai dan saboda kada ya ƙara aure yayyo mata kishiya wallahi aikin banza ne. Idan mijinki ya yi niyyar aikata abu musamman ƙara aure kuma bai yi niyyar gaya maki ba duk buncikenki ba za ki taɓa ganewa ba. Kiran da zan yi a gare su shi ne su bari, duk abin ki, baki isa ki hana namiji abun da yayi niyya ba. Musamman akan ƙarin aure, addu’a da miƙa al’amura zuwa ga Allah shi ne kaɗai mafita a gare mu. Sosai kuwa, illah ta farko shi ne, idan har ki ka kamasa da abin da ki ke zargin yana aikatawa babu abun da zai haifar maki sai tashin hankali. Shawarar da zan basu shi ne, idan har ba saɓon Allah yake da wanda yake neman ba  mafi a’ala shi ne ki bi shi da fatan alkhairi.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Taskira

এছাড়াও পড়ুন:

Jerin Gwarazan Taurarinmu!

3. A Hangen Nesansa wajen jagorancin al’umma, ya mayar da hankali kan masana’antu, sabunta ababen more rayuwa da kuma gina Dan’adam; domin mayar da Jihar Nasarawa matsayin wata babbar cibiyar zuba jari a Nijeriya da horar da aikin injiniya tare da kyautata jin dadin al’ummar jihar; an zabi Injiniya Abdullahi A. Sule a matsayin Gwarzon Gwamnan Shekarar 2025.

Injiniya Abdullahi Sule: Wanda Ya Fi Yin Fice Kan Harkokin Masana’antu A Duk Fadin Arewa

4. Shugabancinsa ya yi matukar kawo sauye-sauye a Jihar Ekiti, musamman ta hanyar gudanar da mulki na adalci, sabunta ayyukan more rayuwa, karfafa matasa da fadada aikin gona; sakamakon tawali’un da yake da shi da horon da ya samu wajen tafiyar harkokin kudi da gina jama’a tare kuma karfafa al’adun demokuradiyya; ya sa aka zabi Biodun Abayomi Oyebanji a matsayin Gwarzon Gwamnan Shekarar 2025.

Biodun Abayomi Oyebanji: Wanda Ya Kawo Juyin-juya-hali A Jihar Ekiti

5. A sauyin da ya kawo a shugabancinsa, jajircewarsa na kawo ci gaba a fannin tsaro, zuba jari mai yawan gaske a fannin ilimi, kiwon lafiya da sauran ababen more rayuwa; kazalika a kokarinsa na sake mayar da Jihar Zamfara kan turbar zaman lafiya da ci gaba mai dorewa, Dauda Lawal shi ne Gwarzon Gwamnanmu na wannan shekara.

Dauda Lawal: Ceto Zamfara Domin Ci Gaba

6. Ya dukufa wajen mayar da hankali kan manufar da ya sanya gaba, mai taken; “MORE Agenda”, wanda ya sake fasalin tsarin mulkin Jihar Delta ta hanyar zaman lafiya, hadin kai da kuma jajircewa wajen samar da ababen more rayuwa, ilimi, lafiya da kuma gina al’adun jama’a bisa gaskiya, tsantseni a sha’anin harkar kudi ta bangarori da dama; Rt. Hon. Sheriff Oborebwori, shi ne gwarzon gwamnanmu na 2025.

Sheriff Oborebwori: Gwamnan Da Ya Ginu Kan Tabbatar Da Zaman Lafiya Da Ci Gaban Al’umma

7. Saboda kasancewarsa mai sasanta mutane da hada kansu duk da bambance- bambancensu; ga kuma samar da abubuwan more rayuwa a kauyuka, farfado da lamarin kula da lafiyar al’umma, taimaka wa manoma da matasa yadda za su tsaya da kafafunsu; tafiyar da gwamnati ta tausaya wa al’umma, yin biyayya da dokoki, da tunanin yadda gaba za ta yi kyau; shi ya sa aka zabi Sanata Uba Sani a matsayin Gwarzon Gwamnan shekarar 2025.

Sanata Uba Sani: Mai Hada Kan Al’ummar Da Suka Rarrabu

Gwarzon Dan Majalisa Na Shekarar 2025

8. Saboda yadda ya shahara wajen yin doka, wakilci, nuna damuwa da sai abu ya kasance; yadda yake da hazaka, sa ido kan ci gaban inda yake wakilta, da kokarin samar da zaman lafiya, tsarin da ya sa aka samu cimma buri a gyaran tsarin mulki, hadin kan kasa;. Honorabul Benjamin Okezie Kalu, PhD, CFR don haka shi ne dan majalisar shekarar 2025.

Benjamin Okezie Kalu: Wakili A Majalisa Saboda Hadin Kan Kasa, Zaman Lafiya, Da Ci Gaba

Gwarzon Ma’aikacin Gwamnati Na Shekarar 2025

9. Bisa la’akari da yadda ya tafiyar da sha’anin kawo gyara a lamarin tara haraji, abin da aka aiwatar ta yadda ya dace a yi da gaskiya domin habbaka hanyoyin samun kudaden shiga ba ta hanyar man fetur ba, amma ta hanyar bullo da wasu dabaru ta kafar sadarwa ta zamani; da yake an dauki hukumomin gwamnati da su ma abokan tafiya ne domin samun ci gaba, ba tare da an sa wani abu na matsi ba; Dakta Zacch Adedeji a yanzu shi ne gwarzon ma’aikakaci na shekarar 2025.

Dakta Zacch Adedeji: Wanda Ya Kara Daukaka Darajar Haraji A Nijeriya

Gwarzon Dan Kasuwa Na 2025

10. Saboda hangen nesansa wajen kawo gyara a lamarin bunkasa samar da takin zamani a Nijeriya da kuma harkar kasuwancin amfanin gona; don tallafa wa miliyoyin manoma hanyar amfani da abubuwan gida. Da kuma kokarinsa na samar da wata hanyar taimakawa masu karamin karfi yadda za su cimma burinsu na maida aikin gona a matsayin wata hanya da za ta taimaka wa al’umma; don haka Thomas Etuh shi ne gwarzon Dan kasuwa na shekarar 2025.

Thomas Etuh: Gwarzo Wajen Samar Da Hanyoyin Dogaro Da Kai Ga Matasa

Gwarzon Shugaban Kamfani Na Shekarar 2025

11. Domin jagorantar bangaren hakar mai da iskar gas na tekun Nijeriya da ya yi nasarar samar da ganga miliyan 1.8 na man fetur a kowace rana; da kuma jagorantar hukumar NUPRC ta zarce burinta na samun kudaden shiga da kashi 84.2 cikin dari, Injiniya Gbenga Komolafe shi ne Gwarzon Shugaban Kamfani na Shekara ta 2025.

Gbenga Olu Komolafe: Jagorantar Tsarin Samar Da Makamashi A Nijeriya

Gwarzon Ma’aikacin Banki Na Shekarar 2025

12. Domin jagorantar harkar kudi ta hanyar kirkire-kirkire tare da karfafa samar da kanana da matsakaitan sana’o’i (MSME) 700,000 da karfafa tubalin tattalin arzikin Nijeriya da kuma sake fasalta banki; an zabi Dakta Tony Okpanachi a matsayin Gwarzon Ma’aikacin Banki Na Shekarar 2025.

Dr Tony Okpanachi: Gina Makomar Nijeriya Ta Hanyar Tallafa Wa Kananan Kamfanoni

Wanda Da Ya Fi Tasiri A Kafofin Sada Zumunta Na Shekarar 2025

13. Domin sauya rikici zuwa hadin kai, da tashin hankali zuwa ci gaba mai ma’ana da kirkirar ayyukan yi, samar da zaman lafiya da sabunta zamantakewa, al’adu da tattalin arzikin Neja Delta da zuba jari a ilimi, kiwon lafiya, muhalli da karfafa ci gaba, an zabi Babban Sarki Oweizide Ekpemupolo (Tompolo) a matsayin mafi tasiri a Kafofin Sada Zumunta na 2025.

Babban Sarki Oweizide Ekpemupolo (Tompolo): Hiddimta Wa Al’umma Ba Tare Da Gajiyawa Ba

Gwarzuwar Hukumar Gwamnati Ta Shekarar 2025

14. Domin fadada iyakokin aiwatar da doka a Nijeriya tare da dawo da fiye da naira biliyan 10 ga masu amfani da kayayyaki tare da kalubalantar rashin adalci na kamfanoni da kafa sabbin ka’idoji kula da kasuwanci ta kafafen sadarwar zamani da tabbatar da adalci da shugabanci na na gari — Hukumar Kare ‘Yancin Masu Amfani da Kayayyaki ta Kasa (FCCPC), ita ce Gwarzuwar Hukumar Gwamnati ta Shekarar 2025.

Hukumar Kare ‘Yancin Masu Amfani Da Kaya (Fccpc): Tabbatar Da Adalci A Kasuwa

SkalesShi Ne Gwarzon Mawakin Shekarar 2025

15. Sakamakon tasirin da ya dade yana yi a fannin waka a Nijeriya da kasashen waje. Shahararriyar wakarsa “Shake Body”, wacce ta kai ga samun miliyoyin masu sauraro a Spotify da kuma kwarewarsa a fannin fasahar hada al’umma daban-daban. SKALES ne Gwarzon Mawakin Shekarar 2025.

Kanyenyachukwu Tagbo Okeke Shi Ne Gwarzon Mai Zane Na Shekarar 2025

16. Saboda sanya Nijeriya a taswira ta duniya tare da Guinness World Record (GWR) na Mafi Girman Zanen Canbas da mutum daya ya yi a wannan shekara, da kuma wayar da kan jama’a kan cutar autism a Nijerriya, tare da amfani da fasaha wajen karfafa hadin kai da ilimi ga mutane masu kwarewa daban-daban, Kanyenyachukwu (wanda aka fi sani da Kanye) Tagbo-Okeke shi ne Gwarzon Mai Zane na Shekara 2025.

Gwarzon Mai Koyar Da Wasanni Na Shekarar 2025

17. Saboda jagorantar Super Falcons zuwa nasarar lashe kofin WAFCON karo na 10, wanda ya kara musu tasiri; da nuna kwarewa a dabaru da shugabanci da dawo da aminci a kwallon kafar Nijeriya da kuma karfafa sabon karni na masu horar da kwallo a Afirka, Justine Madugu shi ne gwarzon mai koyar da wasanni na Shekarar 2025.

Justine Madugu: Mai Dabaru Dawo Da Darajar Kwallon Kafa A Nijeriya

Dabid Adeyemi Shi Ne Gwarzon Matashi Na Shekara 2025

18. Dangane da habaka kirkira, tausayi da kwarewa ta hanyar kirkirar manhajar AI wacce ke sauya yadda dalibai masu nakasar gani ke samun ilimi a Nijeriya da wajenta, Dabid Adeyemi shi ne Gwarzon Matashi na Shekarar 2025.

Gwarzon Ma’aikacin Lafiya Na Shekarar 2025

19. Domin ganin yadda ya sauya akalar samar da kiwon lafiya cikin tausayi da soyayya ga mabukata tare da yi wa mutane fiye 2,600 tiyata kyauta a sassan kasar nan. Dr Seidu Adebayo Bello shi ne Gwarzon Ma’aikacin Kiwon Lafiya na shekarar 2025.

Dr Seidu Adebayo Bello: Ya Dawo Da Fata Ga Al’umma

Misis Mabel Ijeoma Duaka Shi Ne Gwarzuwar Ma’aikaciyar Jinya Ta Shekarar 2025

20. Duk da ayyukan ta’addanci na Boko Haram, yayin da al’umma musamman baki ke gudu daga yankuna da dama na Jihar Borno, ta gwammace ta zauna a karamar hukumar Mafa domin ci gaba da bayar da kulawa ga wadanda suka jikkata na tsawon shekara 21. Mrs Mabel Ijeoma Duaka ce Gwarzuwar Ma’akaciyar jinya ta shekarar 2025

Bankin Probidus Ne Gwarzon Banki Na Shekarar 2025

21. Saboda kasancewa kan gaba wajen zamanantar da harkokin Banki a Nijeriya da kuma karfafa wa manya da kananan masa’na’antu tare da zama a kan gaba wajen daukaka darajar aikin Banki a Nijeriya, Bankin Probidus ne Gwarzon bankinmu na shekarar 2025.

Gwarzuwar Matashiya ‘Yar Makaranta Ta Shekarar 2025

22. Domin nasarar da ta samu wajen sanya sunan Nijeriya a fagen ilimi a duniya da jajircewa, hazaka da bayar da shawarwari don zaburar da sabbin dalibai don rungumar harshe Turanci da tabbatar da nasara na iya tasowa daga kowane bangare. An bai wa Nafisa Abdullahi Aminu lambar yabo ta Gwarzuwar Matashiyar 2025.

Nafisa Abdullahi Aminu: Yarinyar Da Ta Daukaka Darajar Nijeriya A Idon Duniya

Hukumar NASENI Ne Gwarzuwar Hukumar Da Ta Kawo Sauyi A Kula Da Muhalli A 2025

23. Domin yadda ta jagoranci ci gaban masana’antu, samar da makamashi, da fasahohin da suka dace da yanayin da ke rage fitar da iskar carbon mai guba da inganta hanyoyin samar da wutar lantarki mai tsabta; karfafa masu kirkire-kirkire na cikin gida, samar da dabarun tattalin arzikin mai dorewa, da habaka dogaro da kai a Nijeriya ta hanyar bincike da kula da muhalli, Hukumar NASENI ce Gwarzuwar Hukumar da ta fi tasiri wajen kare muhalli a shekarar 2025.

Gwarzon Kamfanin Fasahar Kudade Na Shekarar 2025

24. Don kawo sauyi a harkokin kudade ta hanyar fasahar zamani da suka hada da kirkira da gaskiya wajen karfafa miliyoyin ‘yan Nijeriya, kanana da matsakaitan kamfanoni (MSME) ta hanyar amfani da wayar hannu, don kawo karshen matsalolin kudade ta hanyar fasahar zamani, OPay Nigeria ya amsa sunansa na zama gwarzon kamfanin fasahar harkokin kudade na shekarar 2025.

OPay Nigeria: Tabbatar Da ‘Yancin Hada-hadar Kudi

Kamfanin GEIL: Gwarzon Kamfanin Samar Da Kayayyakin Gida Na Mai Da Gas Na Shekarar 2025

25. Domin jagorantar bunkasawa da gudanar da tashar fitar mai na farko a Nijeriya fiye da shekaru 50, Kamfanin GEIL shi ne Gwarzon Shekarar 2025

Gwarzon Kamfanin Samar Da Kaya Na Shekarar 2025

26. Domin habaka samar da ruwan sha mai inganci da arha, dandano da wayar da kan ‘yan kasa kan amfani da tsaftataccen ruwa, kamfanin Nestlé Pure Life Nigeria Plc shi ne gwarzon samar da kaya a shekarar 2025.

Kamfanin Nestlé Pure Life: Tsarinsa Da Manufa

Kamfanin Trade Modernisation Project: Gwarzon Kamfani Na Shekarar 2025

27. Domin sauya tsarin kasuwancin Nijeriya ta hanyar fasahar zamani da inganci, sarrafa ayyuka, kara habaka samun kudaden shiga da saukaka gudanar da kasuwanci, bunkasa hadin gwiwar gwamnati da masu zaman kansu, samar da ayyukan yi da karfafa gasa, Kamfanin Trade Mo

dernisation Project (TMP) shi ne gwarzon Kamfanin shekarar 2025.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Rahotonni Matsalar Tsaro: Janar Irabor Ya Nemi A Sa Dokar Ta-baci A Wasu Sassan Nijeriya October 17, 2025 Rahotonni Masana Sun Bayyana Yadda Za A Magance Ficewar Kamfanoni Da Masana’antu Daga Nijeriya October 11, 2025 Rahotonni Ranar Malamai Ta Duniya: Rashin Kulawa Ke Sa Malamai Barin Aiki October 11, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Jerin Gwarazan Taurarinmu!
  • An gano gawar wata mai shekara 96 a cikin masai
  • Zaben Kananan Hukumomi A Neja Ya Bar Baya Da Kura
  • Yadda Duniya Ta Fara Wayewa Tun Daga Zamanin Annabi Nuhu (AS) Har Manzon Allah (SAW) Ya Zo Ya Cika Komai (2)
  • Ma’aikatan NPA Wasu Ginshikai Ne Na Ciyar Da NPA Gaba —Dantsoho
  • Ɓarayi Sun Shiga Ofishin Shugaban Karama Hukuma A Kano, Sun Tafka Sata
  • Majalisa Ta Amince Da Ɗaurin Shekaru 14 A Gidan Yari Ga Malamai Masu Cin Zarafin Mata A Jami’o’i
  • Yara biyu sun mutu bayan faɗawa rijiya a Kano
  • Likitoci sun wayar da kan mata kan cutar Sankara a Gombe
  • Sin Za Ta Gyara Matakan Haraji Kan Kayayyakin Da Ake Shigowa Da Su Daga Amurka