Gwamnan Kano ya naɗa mace ta farko a matsayin shugabar Jami’ar Northwest
Published: 11th, December 2025 GMT
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da naɗin Farfesa Amina Salihi Bayero, a matsayin sabuwar Shugabar Jami’ar Northwest.
Naɗin nata zai fara aiki daga ranar 1 ga watan Disamban 2025, har zuwa tsawon shekaru biyar.
EFCC ta tsare tsohon ministan ƙwadago, Chris Ngige An koro ’yan Najeriya 32 kan kasuwancin miyagun ƙwayoyi a IndiyaMai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis.
Sanarwar, ta ce gwamnan ya amince da naɗin ne bayan tantancewa da kwamitin gudanarwar jami’ar ya yi mata.
A matsayinsa na jagoran jami’ar, Gwamna Abba, ya yaba wa shugaban kwamitin da mambobinsa kan jajircewarsu wajen bin ƙa’idojin tantancewar.
Haka kuma ya nemi a yi mata addu’ar samun nasara wajen gudanar da jagorancin Jami’ar.
Farfesa Amina Salihi Bayero ƙwararriya ce a fannin Chemistry, musamman Analytical Chemistry, kuma ita ce mace ta farko da ta samu digiri na uku a fannin daga Jami’ar Bayero Kano.
Ta taɓa riƙe muƙamai da dama a harkar ilimi da gudanarwa, ciki har da shugabar sashen Chemistry, da kuma Mataimakiyar Shugabar Jami’a (DVC) a Jami’ar Yusuf Maitama Sule.
Ana girmama ta saboda jajircewarta wajen horar da matasan masana kimiyya.
Ana sa ran naɗin nata zai ƙara ɗaukaka martabar jami’ar, ya inganta tsarin ilimi, tare da bai wa mata ƙofar samun manyan muƙamai a Jihar Kano.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Farfesa Amina Bayero Jami ar Northwest Naɗi
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Kasar Iran Yace Mata Su ne Ginshin Gina Makomakar Kowacce Kasa
Shugaban kasar |iran Mas’ud pezeshkiyan da yake Magana a wajen taron ranar mata a kasar iran ya bayyana cewa maza ta da mata suna taka rawa iri daya wajen ciyar da alumma gaba, kan kyawawan ayyukan, kana ya jaddada cewa mata musamman iyaye suna taka muhimmiyar rawa wajen samar da matasa masu tasowa da kuma nusar da Alumma kyakkyawar makoma.
Kyawawan halayen musulunci wasu ginshi kai ne da suke daidaita maza da mata, saboda Al’qur’ani yayi alkawarin kyakkyawar rayuwa ga wadanda suka yi kyawawan ayyuka, da gaskiya ba tare da la’akari da jinsin su suba, haka zalika ya jaddada wannan ka’ida inda aka tsara mata ba a matsayin na biyu ba, amma a matsayin muhimmin abokan hulda wajen gina ci gaban rayuwar zamantakewa.
Pezeshkiyan yace maza da mata daya suke wajen aikata ayyukan kwaraai wanda dole ne ya hada da Imani da ayyukan kwarai acikin jama’a. kuma jaddada tasirin mata fiye da na maza musamman ta hanyar bada gudunmawa wajen renon iyalai da kuma tsara dabiu na managarta.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label Name* Email* Website Label Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran Ta yi Tir Da Kisan Karen Dangin Isra’ila A Gaza A Ranar Yaki Da Kisan Kiyashi Ta MDD December 10, 2025 Borkina Faso Ta Saki Sojojin Sama Na Najeriya 11 Da ta Kama Bayan Jirginsu Yayi Saukar Gaggawa. December 10, 2025 Hamas Ta yi Tir Da Sabbin Matsugunan Yahudawa Da Isra’ila Ke yi A Yankunan Da Ta Mamaye December 10, 2025 Iran Tana Daukar Bakwancin Taron BRICS Na Binciken Kimiya Da Kuma Ci Gaban Ilmi December 10, 2025 Nasarar Da Iran Ta Samu A Yakin Kwanaki 12 Kan HKI Yana Jawo Hankalin Kasashen Duniya December 10, 2025 ‘Yan Ta’adda Sun Kai Hare-Hare Kan Sojojin Pakistan Sun Kuma Kashe 6 Daga Cikinsu December 10, 2025 Najeriya: Majalisar Dattawa Ta Bawa Tunubu Damar Kai Sojoji Zuwa Kasar Benin December 10, 2025 Ministan Makamashi: Iran Tana Da Sanayya Ta Ilimi Na Samar Da Hadari Domin Yin Ruwan Sama December 10, 2025 Kasar China Ta Zartar Da Hukuncin Kisa Akan Wani Babban Jami’in Banki December 10, 2025 Ganawa A Tsakanin Mataimakan Ministocin Waje Na Kasashen Saudiyya, China Da Minista Arakci Na Iran December 10, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci