Shirin kafa ‘Hisbar Ganduje’ ya tayar da ƙura a Kano
Published: 14th, December 2025 GMT
Yunƙurin tsohon Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, na kafa wata rundunar tsaro mai kama da Hisbah ya jawo ce-ce-ku-ce a faɗin jihar.
Wannan shiri da ya kira Hisbah mai zaman kanta, an tsara shi ne domin ɗaukar ma’aikata 12,000 waɗanda gwamnatin Kano mai ci ta sallama daga a Hukumar Hisbah.
Sanarwar ta haifar da ra’ayoyi mabambanta, inda wasu ke goyon baya, wasu kuma na adawa, yayin da wasu ke taka-tsantsan.
Kazalika, mutane da dama na tambayar sahihancin kafa rundunar a bisa doka, manufar shirin da kuma tasirinsa ga tsaro da shugabanci a jihar.
Tushen taƙaddamarHukumar Hisbah ta Jihar Kano, wacce gwamnati ta kafa a jihar, tun da daɗewa ita ce take da alhakin inganta tarbiyyar mutanen jihar bisa tsarin addinin Musulunci, umarni da kyawawan ayyuka da hani da munana, da kuma aiwatar da wasu sassa na dokar Shari’ar Musulunci.
A baya, Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta sallami ’yan Hisbah 12,000, bisa hujjar cewa akwai matsaloli a yadda aka ɗauke su aiki da kuma yadda suke gudanar da ayyukan nasu.
Ganduje, wanda shi ne tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, ya bayyana korar a matsayin rashin adalci. Don haka, ya kafa kwamitin da tsohon Shugaban Hukumar Kula da Ababen Hawa ta jihar (KAROTA) a zamanin mulkin na Ganduje, Baffa Babba Ɗan Agundi ya jagoranta domin tantance sunayen ma’aikatan da abin ya shafa.
Ɗan Agundi yayin gabatar da rahoton, ya ce kwamitin ya yi nasarar tantance ma’aikatan da aka sallama.
“Ranka ya daɗe, ga rahoton ma’aikata 12,000 da gwamnatin Kano ta sallama. Mun tabbatar da su da bayanansu. Dukkansu suna tare da kai a wannan tafiya,” in ji Baffa ga Ganduje.
Dalilin kafa ‘Hisbah mai zaman kanta’Ganduje ya sanar da kafa sabuwar runduna da za ta yi aikin da ya kira na ƙungiya mai zaman kanta, ba wai wata hukumar gwamnati ba.
“Za a kira ta Hisbah mai zaman kanta. Na san akwai wasu da dama da za su so shiga banda waɗannan 12,000. Nan gaba kaɗan za a ba ku wani aikin na ƙaro wasu mutanen da ke ƙoƙarin shiga,” in ji shi.
An tsara rundunar za ta kasance ƙarƙashin jagorancin Sheikh Muhammad Harun Ibn Sina, tsohon Babban Kwamandan
Hukumar Hisbah a zamanin mulkin Ganduje a Kano.
Ibn Sina ya bayyana cewa za a kira rundunar da suna ‘Khairun Nas’, kuma za ta kasance ƙungiyar sa kai mai ayyuka makamantan na Hisbah, amma ba tare da zama hukuma ta gwamnati kamar Hisbar ba.
Ya ce: “Ma’aikata 12,000 da aka ɗauka a lokacin [Ganduje] kuma wannan gwamnatin ta sallama sun koka. Ya ce za a iya kafa ƙungiya mai zaman kanta, amma ba hukuma ba, domin gwamnati ce kaɗai za ta iya kafa hukuma. Don haka aka kafa kwamitin da muka jagoranta tare da Ɗan Agundi da wasu mutum huɗu domin tantance mutanen da kuma shirinsu na shiga.”
Ya ƙara da cewa ba a kai ga kammala ƙungiyar ba tukuna, kuma za ta kasance a buɗe ga duk mai sha’awar shiga. Dangane da alawus ɗin dakarun ƙungiyar, Ibn Sina ya ce ƙungiyar za ta kasance ta sa kai, sai dai idan an sami tallafi daga ɗaiɗaikun mutane ko ƙungiyoyi sannan za a iya ba su ɗan kuɗin alawus.
A cewarsa, manufar ƙungiyar za ta haɗa da “umarni da kywawan ayyuka da hani da mummuna, bayar da taimakon gaggawa, nasiha da taimakon jama’a.”
An fara ɗaukar dakarun a ƙarƙashin Gidauniyar GandujeSai dai ƙasa da mako biyu bayan sanarwar, Gidauniyar Ganduje ta ƙaddamar da ɗaukar ma’aikatan rundunar da aka sanya wa suna ‘Independent Hisbah Fisabilillah’.
A wajen ƙaddamarwa a Kano, Ɗan Agundi da Ibn Sina sun jaddada cewa sabuwar Hisbar ba hukuma ba ce ta gwamnati, illa dai ƙungiyar sa kai ce domin ayyukan addini da jin ƙai.
Ana sa ran ɗaukar ma’aikatan zai ƙunshi tsofaffin ’yan Hisbar da aka sallama tare da buɗe ƙofa ga sabbin masu son shiga daga dukkan ƙananan hukumomin jihar 44.
Matakin ya saɓa doka — Gwamnatin KanoA nata ɓangaren, gwamnatin Kano ta nuna damuwa kan yunƙurin. Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’amuran Cikin Gida na jihar, Ibrahim Waiya, ya zargi Ganduje da yin maganganun tunziri, musamman kan hare haren ’yan bindiga a jihar.
Waiya ya ce ’yan bindiga sun fara kai hare-hare a jihar kasa da sa’o’i 48 bayan maganganun Ganduje, yana mai danganta lamarin da “maganganun tayar da hankali” na tsohon gwamna Ganduje da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin.
Kwamishinan ya kuma buƙaci hukumomin tsaro da su binciki Ganduje tare da kama shi bisa zargin ƙoƙarin nasa na kafa wata rundunar ba bisa ƙa’ida ba.
Amma Ganduje ya yi watsi da zarge zargen a matsayin “marasa tushe” da “rashin kan gado,” yana mai jaddada cewa ba a taɓa danganta shi da tashin hankali ko wani abu da zai iya tayar da zaune tsaye a Kano ba.
Ganduje na da ’yancin kafa rundunar… — LauyaWani lauya a Kano, Barista Kamilu Ahmad, ya ce doka ta ba da dama ga mutum ya kafa rundunar tsaro ta ƙashin kansa, amma dole ne a yi hakan bisa tsarin doka.
Ya Dokar Kafa Kamfanonin Tsaro Masu Zaman Kansu ta 1986, inda ya ce “duk wani ɗan Najeriya na da ’yancin kafa kamfanin tsaro a Nijeriya ta hanyar bin tsarin da doka ta tanada.”
Sai dai ya jaddada cewa bai kamata ayyukan irin wannan rundunar su yi iri ɗaya da ayyukan ’yan sanda ko wata hukumar tsaro ba.
Lauyan ya ce Ganduje na iya yin rajistar kamfanin tsaro a Kano a matsayin ƙungiya mai zaman kanta, amma ya gargaɗe shi da kada ya yi amfani da sunaye ko alamomi da za su yi kama da na gwamnatin da doka ta kafa.
“Ba zai yiwu ya yi amfani da sunan Hisbah ba, kuma manufar kamfaninsa ba za ta yi kama da ta Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ba. Ba za a yi amfani da kayan sawa da suka yi kama da na kowace rundunar tsaro ba, kuma ayyukan rundunar na asali ba su kamata su yi iri ɗaya da na ’yan Hisbah ko sauran jami’an tsaro ba,” in ji lauyan.
Barista Kamilu ya ƙara da cewa Hukumar Kula da yi wa Kamfanoni Rajista (CAC) da dokar NSCDC sun fayyace matakai da sharuɗɗan yin rajista da kamfanonin tsaro masu zaman kansu.
Ya ce CAC ba za ta yi rajista ga kowace ƙungiya mai ɗauke da sunan Hisbah ba, saboda kawai hukuma mai sunan haka a Kano.
Ya kuma kafa hujjar cewa shirin na Ganduje na iya fuskantar manyan ƙalubale, musamman a lokacin da yanzu haka ake ci gaba da muhawara kan kafa ’yan sandan jihohi.
Kanawa sun bayyana mabambantan ra’ayoyiWasu mazauna Kano da suka zanta da Aminiya sun bayyana mabambantan ra’ayoyi kan batun. Yayin da wasu suka yi maraba da shirin a matsayin hanyar samar da ayyukan yi da kuma gyara ɗabi’un mutane, wasu kuma sun nuna tsoron cewa batun zai iya ƙara rarrabuwar kai irin ta siyasa ko kafa wata hukuma mai kama da ta gwamnati.
A cewar Abdulaziz Ibrahim, ba shi da matsala da kafa ƙungiyar muddin ba za ta wuce gona da iri ba. “Sun ce kawai domin umarni da kyakkyawa da hani da mummuna ne, ban ga matsala a hakan ba. Amma idan suka yi wani abu daban, to a nan ne matsalar take,” in ji shi.
A nasa bangaren, Abdullahi Hassan ya ce lokacin da ake ƙoƙarin kafa ƙungiyar da kuma manufarta ne ke sa mutane ɗariɗari da ita.
“Me ya sa sai yanzu da zaɓe ya ƙarato za a kafa ta kuma me ya sa ɗan siyasa ne zai kafa ta? Mutum 12,000 ba ƙaramin adadi ba ne, za su iya ƙirƙirar wata hukuma mai kama da ta gwamnati,” in ji shi.
Amma ga Habiba Musa, tun da batun ya riga ya jawo muhawara da shakku a tsakanin jama’a, ya fi dacewa a dakatar da shi domin maslahar zaman lafiya da haɗin kan jihar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Tarbiyya Tsaro gwamnatin Kano Hukumar Hisbah ƙungiya mai ta gwamnati Ɗan Agundi wata hukuma
এছাড়াও পড়ুন:
Taɓarɓarewar rashin tsaro ya nuna rashin shugabanci na gari — Obi
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP, Peter Obi, ya ce taɓarɓarewar rashin tsaro a Najeriya na nuna gazawar shugabanci.
Ya yi kira da a gudanar da bincike mai zurfi cikin gaggawa kan zargin wasu jami’an gwamnati da taimaka wa ’yan ta’adda.
Buɗe cibiyar horas da sabbin sojoji a Kudu zai taimaka — Janar Shaibu Shirin kafa ‘Hisbar Ganduje’ ya tayar da ƙura a KanoObi, ya bayyana hakan ne bayan wani bidiyo da aka yaɗa a kafafen sada zumunta, inda wasu da ake zargin ’yan ta’adda ne suka ce jami’an gwamnati ne ke taimaka musu da makamai.
Ya ce wannan zargi abu ne mai matuƙar muhimmanci da bai kamata a yi watsi da shi ba.
“An ga wani bidiyo mai tayar da hankali a Jihar Kwara inda waɗanda aka kama suka ce jami’an gwamnati ne suka ba su harsasai da kayan aiki.
“Wannan zargi na buƙatar bincike cikin gaggawa kuma a bayyane.”
Obi ya ce duk da maƙudan kuɗaɗen da aka kashe a fannin tsaro tsawon shekaru, rashin tsaro na ƙara taɓarɓarewa a ƙasar.
“An kashe tiriliyoyin juɗi da biliyoyin daloli a fannin tsaro, amma duk da haka rashin tsaro na ƙara taɓarɓarewa a faɗin ƙasar nan.”
Ya kuma tambayi dalilin da ya sa ba a amfani da na’urorin zamani da fasahar tsaro wajen gano da kama ’yan ta’adda, duk da cewa ƙasar na da irin waɗannan damarmaki.
“Gwamnati na da iko da hanyoyin sadarwa, bayanan sirri da bin sahun kuɗaɗe, amma duk da haka satar mutane da ta’addanci na ci gaba da ƙaruwa.”
Obi ya kuma soki yadda ake murnar sakin waɗanda aka sace ba tare da kama waɗanda suka aikata laifin ba, inda ya ce hakan na nuna rashin ɗaukar al’amarin da muhimmanci.
A ƙarshe, ya yi gargaɗin cewa ƙaruwar rashin tsaro na nuni da gazawar gwamnati da kuma yin sakaci, inda ya jaddada cewa babban aikin kowace gwamnati ne kare rayuka da dukiyoyin al’umma.