An Yaba Ma Iyaye Bisa Goyon Bayansu ga Shirin Rigakafin Shan Inna a Karamar Hukumar Ringim
Published: 10th, December 2025 GMT
Kananan yara sama da 93,200 ne ake sa ran yiwa allurar rigakafin cutar shan Inna da ake gudanarwa a Karamar Hukumar Ringim ta Jihar Jigawa.
Kazalika, kananan yara sama da 53,800 ne ake sa ran digawa sinadarin vitamin A a yankin.
Shugaban hukumar lafiya matakin farko na yankin Aminu Abubakar Kwandiko ya yaba da yadda iyaye ke bada hadin kai da goyan baya ga shirin.
Ya kuma ja hankalin ma’aikatan rigakafin da su sanya kishi da kwazo wajen samun nasarar aikin.
A sakon da ya aike da shi a taron tattara bayanan aikin rigakafi na yankin, Shugaban Karamar Hukumar, Mallam Badamasi Garba Dabi ya jaddada kudirin Karamar Hukumar na ci gaba da bada gudunmuwa wajen samun nasarar shirin rigakafin.
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jigawa Karamar Hukumar
এছাড়াও পড়ুন:
Kungiyar AU Ta yi Tir Da Harin Da RSF Takai A Makarantar Kananan Yara Da Ya Kashe Mutane 80
Kungiyar Tarayyar Afrika ta AU ta yi tir da harin RSF kan wata makarantar kananan yara a kudancin Sudan da ya kashe dimbin fararen hula tare da jikkata da dama, mafi muni a baya-bayan nan da kungiyar ta kai a kokarin da ta ke yi na ci gaba da kwatar yankuna a sassan Kasar.
Akalla mutane 80 mafiyawancinsu kananan yara ne suka mutu a harin da mayakan RSF suka kai bayan da suka jefa bama-bamai kan wata makarantar kananan yara da ke garin Kalogi na yankin Kordafan a kudancin Sudan.
Rahotanni sun ce hare-hare 3 da RSF ta kai a yankin lokaci guda, inda a farko mayakan suka jefa bama-bamai a makarantar kananan yara gabanin kai hari wani asibiti kana daga bisani suka sake jefa wani bom kan wadanda ke kokarin kai dauki a makarantar kananan yaran.
Shgaban gwamnatin garin na Kalogi da harin ya faru Essam al-Din al-Sayed ya ce yanzu haka babu sadarwa a garin sai dai ta hanyar amfani da Starlink, kuma tsagin RSF da Abdelaziz al-Hilu ke jagoranta ne ke kaddamar da hare-haren kan mata da kananan yara a yankin.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka MِِِِDD: Kisan Kare Dangin Da Isra’ila Ta yi A Gaza Shi Ne Farko Da Yafi Jan Hankalin duniya December 8, 2025 Kasashen Iran Da Azarbaijan Sun Amince Da Ci Gaba Da Tuntubar Juna Domin Warware Duk Wani Rikici December 8, 2025 Iran Da Kasashen Afrika Sun Daura Dammarar Karfafa Alakar Kimiyya Tsakaninsu December 8, 2025 Ecowas Ta Tura Sojoji Zuwa Jamhuriyar Benin Don Dakile Juyin Mulki December 8, 2025 IRGC: Makaman Iran Sun Fada Kan Matatan Man Haifa Har Sau Biyu A Yakin Kwanaki 12 December 8, 2025 Najeriya: Gwamnatin Tarayya Ta Bada Sanarwan Kubutar Da Yan Makaranta 100 Da Aka Sace December 8, 2025 Iraki Ta Musanta Cewa Ta Tushe Asusun Hizbullah Da Ansarallah December 8, 2025 Sabon Fada Ya Barke A Tsakanin Thailand Da Cambodia December 8, 2025 Iran Ta Yi Allawadai Da Kisan Fararen Hula A Kasar Sudan December 8, 2025 Macron Na Faransa Ya Yi Wa Najeriya Alkawalin Taimakawa Akan Matsalolin Tsaro December 8, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci