Leadership News Hausa:
2025-12-14@14:43:10 GMT

Na Ɗauki Harkar Fim Tamkar Aikin Gwamnati — Maryam Usman

Published: 14th, December 2025 GMT

Na Ɗauki Harkar Fim Tamkar Aikin Gwamnati — Maryam Usman

An haife ni a garin Kano, amma asalina ‘yar Adamawa ce, kuma asalina ‘yar Maiduguri ce, sannan kuma yaren Margi ce ni. Bayan na girma a Kano na fara karatu a makarantar sojoji ‘Bokabo Barrack’, daga nan muka bar ‘Katsina Road’ muka koma ‘Yar Akuwa. Na fara firamare ‘Gidan Gona Special Primary School’.

Bayan nan na tafi ‘Jigawa state’ wato Malam Madori, a ‘first time’ ‘yar’uwata ta rasu. Aka canja min makaranta aka dawo da ni ‘Gobernment Secondary School Kura’, a nan na kammala aji shida. Daga nan na tafi ‘Federal Polytechnic Yola’ a nan na karasa karatuna wanda nake da diploma. A yanzu kuma ina Na’ibawa a nan na girma, a nan aka yi min aure, yanzu komai nawa da Na’ibawa nake ‘bearing’.

 

Wane rawa ki ke takawa a cikin masana’antar Kannywood?

Ina taka rawa matsayin jaruma, kuma ina fitowa a matsayin mahaifiya me fadakarwa a cikin Kannywood, duk fim din da za a yi a uwa nake fitowa ba a taba canja min rol ba, kuma na san ba za a taba canja min rol din ba. Saboda ina aktin din iyaye, abin da iyaye suke yi shi nake yi. Shi ya sa a kowane fim za ki ga ana sha’awar saka ni na fito a uwa.

 

Me ya ja hankalinki har ki ka tsunduma cikin masana’antar Kannywood?

Ni dai na san abu ne me kyau, sannan kuma fadakarwa ne. Tun ina sakandare nake yin harkar fim. Babban abin da ya ja hankali na fadakarwar da fim yake, in kana son sako ya isa a minti daya to, harkar fim ita kadai za ta iya wannan abun,

 

Za ki yi kamar shekara nawa da fara fim?

Bayan na fito daga gidan mijina na dan kwan biyu ina wasu ‘business’ dina na harkar abinci, sai kuma na zo na shiga fim. Ban fi shekara biyu ba sai na yi aure, bayan na yi auren kuma da wasu shekaru sai na dada fitowa. Amma daga farawata zuwa yanzu zan yi shekara goma zuwa sha daya da harkar fim.

 

Ya gwagwarmayar shiga cikin masana’antar ta kasance?

Ni ban sha wata gwagwarmaya ba, saboda Sadik N-Mafia shi ya kai ni fim. Da akwai wata mawakiyar Sadi Sidi Sharifai wato Ummi Nagarta, ‘yar’uwa take a guna. Lokacin muna harkar siyasa an ba ni ‘women leader’ na ce mata ina son fim. Lokacin ina ta tunanin ina zan samu Sadik N-Mafia, ta ce to, tunda dan’uwanta ne na zo ta kai ni wajensa. Muna zuwa wajensa washegari na siyi ‘form’, wata washegarin aka fara fim da ni wani fim wai shi ‘Magana Jari’, aka ba ni wani rol me karfi, ban sha wahala ba. Da yake mu fim din kamar a jinin mu yake, ina da ‘yan’uwa da yawa a cikin Kannywood din nan, akwai; Halima Atete, Teemah Makamashi, Isma’il Fish, Aisha Humairan Rarara wacce ‘ya ce a guna uwarta aminiyata ce, sannan akwai Bana, sannan Stephening ta Arewa24 ‘yar’uwata ce to, kin ga mu mun mayar da fim sana’a.

 

Ya batun iyaye lokacin da za ki sanar musu kina sha’awar fara fim, shin kin samu wani kalubale daga gare su ko kuwa?

Gaskiya ban samu wata matsala ba, saboda akwai kanwata ana ce mata Sadiya ta rasu ita ta fara yin fim a gidanmu, har su Atete duk a bayanta suka yi fim. Sannan kuma mahaifiyata da mahaifina wayayyu ne duk abin da yaro yake so, indai ba na batanci bane suna so. Ko lokacin da na shiga fim mahaifina ya rasu sai mahaifiyata, zan iya lissafo miki manyan Kannywood wadanda suka san mahaifiyata wacce suka zo gabanta suka yi mata bayani ta ba ni ‘direct ticket’ ta ce na je, kuma a gabansu ta saka min albarka kuma har yau albarkar ce take dawainiya da ni.

 

A baya kin yi maganar kin fara fim me suna Magana Jari, ya karbuwar fim din ya kasance ga su masu kallon a lokacin?

Eh, na fara da Magana Jari, za ki ga ana yawan nuna shi a DSTB, sannan na zo na yi wani fim Sarka, lokacin ban waye ba sosai. Jamila Nagudu ce ta zaunar da ni ta ce in daina tsoron ‘Camera’, na tsaya na bude idona nayi abu me kyau, shi ma fim din ya karbu. Sannan na zo nayi Ibro Me Kilago, shi ma ya karbu sosai. Sannan a yanzu duk wani fim da ake yi a duniya indai aka saka ni za ki ga fim din ya fashe sosai, saboda wannan tijarar da nake yi.

 

Ya farkon farawar ya kasance?

Za ki ji na ce na tsoraci ‘camera’ Jamila ta gyara min, wannan shi ne na uku. Haske ne ya sa na tsoraci ‘Camera’, amma ko ranar da aka fara dora min ‘canera’ tambayata aka yi ta yi “daman kin saba yin fim?” na ce wannan ne na farko. Amma abin da ya sa ya yi kyau, wannan addu’ar mahaifiyar tawa ce. A fim dina na farko shi ne na hadu da Adaman Kamaye, ba na mantawa mun yi wasu finafinai muka fada tarkon ‘yan sanda ta dauko ni a motarta, muka dawo gida. Wannan shI ne dawowata na biyu kuma sai na dawo da daukaka da albarka.

 

Kin yi finafinai sun kai kamar guda nawa?

Wai! ai finafinan da na yi sun fi dari, bana iya kirga su, saboda ni a wata zan iya yin fim ashirin.

 

Ko za ki iya lissafowa masu karatu kadan daga ciki?

Akwai; Lulu da Andalu na darakta Dan Hausa, Mashahuri na Yakubu Muhammad, Mage da Wuri na Hussaini Bacci, Manyan Mata na Abdul Amart, So Ne na Sultan, Garwashi na Uk, Lokaci na Tijjani Asase. To, suna da yawa gaskiya.

 

Cikin finafinan da ki ka fito, wane fim ne ya zamo bakandamiyyar ki?

Kowane fim bakandamiyata ce, ko ‘comedy’ na yi sai ya zama bakandamiyata.

 

Ko akwai wani kalubale da ki ka taba fuskanta tun daga farkon shigarki masana’antar, zuwa yanzu?

Kalubalen da na fuskanta wata mata ce wacce ta tsaya tana ta tsine min a kan an saka ni a fim din Garwashi, ta ce na takurawa ‘ya ta. Amma na ga tsohuwa ce bata fuskanci mene ne fim ba, shi kadai ne kalubale na. Kuma ban ji haushi ba, da yake sana’a ta ce, ita bata san mene ne fim ba.

 

Wadanne irin nasarori ki ka samu game da fim?

A cikin wannan masana’antar ta Kannywood na samu wata daukaka ta zama ‘Women leader’ a kungiyar Adon Garin Kasar Hausa, ta rantsar da ni a matsayin shugabar mata a Jihar Kano ranar litinin. Da na a makaranta ya samu babban mukami a dalilin uwarsa ‘yar fim ce, sannan ‘ya ta, ta sami babban mukami a dalilin uwarta ‘yar fim ce. Kuma lokacin da aka tura min ita garin iyamurai aka ce ta je bautar kasa, da na je a take babu abin da na kashe aka ba ni inda nake so wato Maiduguri garinmu. Sannan kuma na samu kyaututtuka da dama wanda ba sai na bayyana ba, to, kin ga ni ba zan iya barin fim ba. Na samu abubuwa da yawa kudade, kayan sakawa, alfarma a asibiti, ‘yan’uwana sun sassami alfarma da yawa a dalilina. Kuma ‘yan’uwana da yawa suna aikin gwamnati a dalilin harkar fim na sassamu alfarma da yawa.

 

Ya ki ka dauki fim a wajenki?

Na dauki fim babbar sana’a, saboda yadda dan gwamnati yake jin kansa a aikin gwamnati, haka nake jin kaina a aikin fim. Yadda dan majalisa yake jin kansa a ofis, haka nake jin kaina. Kuma yadda shugaban kasa yake jin kansa yana da mulki a karkashin ikonsa, haka nake jin dadi ina fim ina fadakar da mutane,

shi ne sana’a ta.

Za mu ci gaba a makon gobe

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Nishadi Tun Ina Yarinya Sana’ar Fim Ke Burge Ni —Hafsat Salisu November 30, 2025 Nishadi Duk Niyyar Da Mutum Ya Shigo Da Ita Kannywood Ita Za Ta Bi Shi —HAUWA KUJAMA November 15, 2025 Nishadi Sau Ɗaya Na Taɓa Da-nasanin Fitowa A Cikin Fim – Tanimu Akawu November 13, 2025

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: masana antar

এছাড়াও পড়ুন:

Yadda za ku cike neman aikin jami’an lafiya a Hajjin 2026 da NAHCON

Hukumar Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON) ta fara ɗaukar likitoci da sauran ma’aikatan lafiya domin aikin Hajji da ke tafe a ƙasar Saudiyya.

Hukumar NAHCON ta bayyana cewa shafin neman aikin ya fara aiki daga ƙarfe 11 na dare ranar Juma’a 12 ga Nuwamba, 2025. Za a rufe shafin da ƙarfe 11.59 ranar Litinin, 15 ga watan Disamba, 2025

Latsa nan domin shiga shafin ɗaukar ma’aikatan lafiyan kai-tsaye.

NAHCON ta bayyana cewa jami’an lafiyan da za a ɗauka Su ƙunshi likitoci, masu haɗa magunguna, malaman jinya, da jami’an kula da lafiyar lafiya da ta muhalli (CHO/EHO). Su ne za su yi aikin kula da lafiyar alhazai a yayin aikin Hajjin na shekarar 2026.

NAHCON ta bayyana cewa jami’an da suka yi aiki da ita a matsayin kula da lafiyar alhazai a  shekaru uku da suka gabata (2023 zuwa 2025) ba ne kaɗai za a ɗauka domin wannan aiki na 2026.

Yadda za ku nemi aikin

Masu nema za su shiga shafinta kai-tsaye domin ganin ka’idodin da kuma cike bayanansu. Latsa nan domin lafiyan kai-tsaye.

Ko kuma su gaida babban shafinta daga nan su latsa wasu layuka huɗu da ke hannun dama daga sama.

Daga daga nan su latsa RESOURCES, sai su latsa su shiga NMT Application Portal.

A ciki za su ga ka’idodin neman aikin, su cike bayansu, da kuma sauke duk dakardun da su cike.

Hukumar NAHCON ta bayyana cewa daga bisani za a tuntuɓi duk waɗanda suka yi nasara.

Allah Ya ba da sa’a.

Ka’idodin neman aikin

NAHCON ta jaddada cewa:

– Ma’aikatan lafiya da suka cancanta ne kawai za su iya nema aikin ba Tawagar Lafiya ta Ƙasa (NMT) domin aikin Hajjin 2026

– Aikin NMT na 2026 zai gudana ne bisa tsarin sa-kai, bisa ƙa’idojin duniya da NAHCON ta amince da su.

– Bayanai da aka bayar za su taimaka wajen tantance cancanta da shirin shiga matakin gaba na tantancewa ko jarabawa.

– Duk bayanan da aka gabatar za a duba su. Duk wani kuskure. Ɓoye gaskiya, ko ƙirƙirar bayanan ƙarya zai iya jawo ƙin amincewa da aikace-aikacen ko cirewa daga jerin waɗanda cancanta.

– Wannan aikace-aikacen kyauta ne gaba ɗaya. NAHCON ba ta karɓar kuɗi kai tsaye ko a kaikaice, ko ta hannun wakilai ko hukumomi. Ku yi hattara!

– Cika fom ɗin ba ya nufin an amince da cancanta ko zaɓen ku.

 

Ƙa’idar shekaru:

– Likitoci: 27 zuwa 60 shekara

– Masu haɗa Magunguna: shekara 26 zuwa 60

– Nas da sauran rukuni: 22–60 shekara .

Sharuɗɗa

Dole masu neman shiga NMT su kasance:

1. Suna aiki a lokacin neman shiga.

2. Ba su halarci ayyukan NMT a shekara uku da suka gabata ba (2023, 2024, da 2025).

3. Su kasance a shirye su yi aiki na tsawon kwanaki 28 da kuma zama a Saudiyya har zuwa kwanaki 45 kafin dawowa Najeriya.

4. Ba za a sallame su a wurin aikinsu ba kafin su kammala aikin NMT.

5. Su nuna kyawawan halaye tare da bin ƙa’idojin aikin lafiya da na NAHCON.

6. Su gabatar da tabbacin mai tsaya musu (guarantor).

 

Sharuɗɗan Guarantor:

– Dole ya kasance mutum mai daraja: Ma’aikacin gwamnati (ba ƙasa da GL 15), basaraken gargajiya, Alƙali (Magistrate), ko Shugaban Ƙaramar Hukuma.

– Dole ya san mai neman aikin NMT tsawon aƙalla shekaru biyar kuma ya tabbatar da gaskiya, ƙwarewa, da iya aikinsa.

– Dole ya gabatar da kwafin katin shaida ko wata takardar shaida da ake amfani da ita a ofisoshin gwamnati na Najeriya.

 

Takardun da dole a haɗa da su:

– Fom ɗin Guarantor da aka cika

– Takardar shaidar ƙwarewar aiki (Basic Professional Certificate)

– Takardar NYSC (idan ta shafi mai nema)

– Lasisin aikin lafiya na wannan shekara

– Hoton fasfo (mai farin baya)

– Sanarwar mai nema (applicant’s declaration)

– Takardar izini daga wurin aiki (employer’s clearance letter) .

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Taɓarɓarewar rashin tsaro ya nuna rashin shugabanci na gari — Obi
  • An Fara Gyaran Tashar Talabijin Ta Jigawa Don Kara Mata Nisan Zango
  • ’Yan kasar Chadi 3 sun mutu a hatsarin kwalekwale a Borno
  • Yadda za ku cike neman aikin jami’an lafiya a Hajjin 2026 da NAHCON
  • Kotun Ƙoli Ta Tabbatar Da Hukuncin Kisa Kan Maryam Sanda
  • Kotun Koli ta soke afuwar da Tinubu ya yi wa Maryam Sanda
  • NLC Ta Shirya Zanga-Zangar Rashin Tsaro A Faɗin Ƙasa Ranar 17 Ga Disamba
  • ‘Yan Siyasa Ne Ke Zagon Ƙasa Ga Ci Gaban Nijeriya — Sarki Sanusi II
  • Shugabannin Sin Sun Yi Taron Koli Na Tattauna Aikin Raya Tattalin Arziki Don Tsara Abubuwan Da Za A Aiwatar A 2026