Aminiya:
2025-12-10@17:06:30 GMT

EFCC ta tsare Malami kan binciken kuɗaɗen Abacha

Published: 10th, December 2025 GMT

Hukumar EFCC ta tsare tsohon Antoni-Janar na Tarayya, Abubakar Malami, saboda binciken da ya shafi dawo da wani ɓangare na kuɗaɗen Abacha.

Hukumar ta kira Malami a makon da ya gabata, inda ta yi masa tambayoyi kan wani bincike da ta ke inda ta sake shi daga bisani, amma yanzu ta tsare shi.

Real Madrid  za ta ɓarje gumi da Manchester City a Santiago Najeriya da Saudiyya sun rattaba hannu kan yarjejeniyar samar da tsaro

Malami ya ce bai aikata komai ba, kuma ba shi da alaƙa da abin da ake zargi.

A cikin wata sanarwa, ya ce: “Ba a taɓa zargina, gayyata ko bincikena game da tallafa wa ta’addanci ba. Duk wani yunƙuri na danganta ni da irin wannan laifi ƙarya ne.”

Ya ƙara da cewa rahotannin kafofin yaɗa labarai ke watsawa sun yi masa mummunar fassara.

“Ba daidai ba ne a ce aikina na gwamnati ya zama hujja ta tallafa wa ta’addanci. A lokacin aikina, na yi aiki tuƙuru wajen ƙarfafa yaƙi da ta’addanci, ba goyon bayansa ba.”

EFCC ba ta fitar da wata sanarwa kan tsare Malami ba.

Haka kuma bai wallafa komai a shafukan sada zumunta ba tsawon kwanaki huɗu.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Kuɗaɗe zargi

এছাড়াও পড়ুন:

‘Yan Bindiga 18 Sun Muta a Wata Arangama da Rundunar Operation Fansan Yamma

Daga Nasir Malali

An kashe ’yan bindiga guda goma sha takwas a wani samame da Rundunar Hadin Gwiwa ta Operation Fansan Yamma ta kai a kauyen Kurawa da ke Karamar Hukumar Sabon Birni ta Jihar Sokoto.

A wata hira ta wayar tarho, wani shaida daga yankin, Malam Aminu Muhammad, ya shaida wa Rediyon Najeriya a Sokoto cewa, nasarar samamen ta fara ne bayan rundunar ta samu bayanin cewa wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da mazauna yankin da ke kan hanyarsu ta zuwa kasuwar mako-mako a kan hanyar Tarah zuwa Karawa a Sabon Birni.

Sojojin sun garzaya cikin gaggawa bayan jin harbe-harbe, inda suka kusan awa guda suna musayar wuta da maharan.

Shaidan gani da idon ya ce sojojin sun  kwato bindigogi da babura takwas, tare da tabbatar da cewa babu jami’in tsaro ko farar hula da ya rasa ransa ko ya ji rauni a samamen.

Da aka tuntube shi ta waya, dan majalisar dokoki mai wakiltar Sabon Birni a Majalisar Dokokin Jihar Sokoto, Honarabul Aminu Boza, ya tabbatar da lamarin, yana mai cewa rundunar hadin gwiwar na ci gaba da gudanar da aikin bincike a maboyar ’yan bindigar tare da taimakon wani dan bindiga da aka kama wanda ke nuna wa sojojin hanya a yayin binciken.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An kama wani mutum a Abuja yana ƙoƙarin kai harsasai ga ’yan bindiga a Zamfara
  • Iran Tana Daukar Bakwancin Taron BRICS Na Binciken Kimiya Da Kuma Ci Gaban Ilmi
  • ’Yan jaridar Daily Trust da Trust TV sun lashe kyautar binciken ƙwaƙwaf ta Wole Soyinka ta bana
  • An Yaba Ma Iyaye Bisa Goyon Bayansu ga Shirin Rigakafin Shan Inna a Karamar Hukumar Ringim
  • Za a Yi wa Yara 194,000 Rigakafin Cutar Shan Inna a Karamar Hukumar Birnin Kudu
  • An dakatar da Shugaban Karamar Hukumar Lafia
  • ‘Yan Bindiga 18 Sun Muta a Wata Arangama da Rundunar Operation Fansan Yamma
  • Kasashen Iran Da Azarbaijan Sun Amince Da Ci Gaba Da Tuntubar Juna Domin Warware Duk Wani Rikici
  • An gano gawar malamin Islamiyya da ya ɓace a Neja