Mutum biyu sun mutu a harbin bindiga a Jami’ar Brown ta Amurka
Published: 14th, December 2025 GMT
Jami’ar Brown a Amurka ta ba da rahoton mutuwar mutum biyu, tare da jikkatar guda tara dake cikin tsanani a harbin da aka yi a makarantar.
An ruwaito cewa mutane da yawa sun jikkata a harbin da aka yi kusa da harabar Ivy League da ke Rhode Island.
Hukumomi yankin sun bukaci jama’a da su ci gaba da kasancewa a kulle yayin da maharin ya tsere.
“Zan iya tabbatar da cewa akwai mutane biyu da suka mutu da yammacin yau, kuma akwai wasu mutane takwas da ke cikin mawuyacin hali, kodayake basu cikin damuwa sosai,” in ji Magajin Garin Brett Smiley, a wani taron manema labarai.
“Muna amfani da duk wata hanya da za mu iya don gano maharin in ji Mataimakin Shugaban ‘Yan Sanda Timothy O’Hara.
Wannan harbin shi ne na baya-bayan nan a cikin jerin hare-haren makarantu a Amurka, inda yunkurin takaita damar malllakar makamai cikin sauki ke fuskantar kalubalen siyasa.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Shugabannin kasashen (ECOWAS) na taro a Abuja December 14, 2025 Kasashen AES zasu kafa bankin dogaro da kai December 14, 2025 Sheikh Na’im Kassim: Idan Duniya Baki Daya Za Ta Taru, Ba Wanda Zai Iya Kwace Makaman Hizbullah December 13, 2025 DRC: Kungiyar M23 Ta Kwace Iko Da Wani Gari Mai Muhimmanci December 13, 2025 Syria: Sojojin “Isra’ila” Sun Kutsa Cikin Yankin Qunaidhara December 13, 2025 Kalibaf: Iran Da Habasha Suna Bunkasa Alakokin Siyasa Da Tattalin Arziki December 13, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan(a) 171 December 13, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan(a) 170 December 13, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan(a) 169 December 13, 2025 Isra’ila Ta Kai Hari A Kudancin Labanon A Ci Gaba Da Keta Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta December 13, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sheikh Na’im Kassim: Idan Duniya Baki Daya Za Ta Taru, Ba Wanda Zai Iya Kwace Makaman Hizbullah
Babban sakataren kungiyar gwgawarmayar musulunci ta Lebanon Sheikh Na’im Kassim ya bayyana cewa; Amurka ta kwana da sanin cewa, za mu kare kanmu, ko da sama da kasa za ta hade.
Babban magatakardar kungiyar ta Hizbulllah Sheikh Na’im Kassim ya kuma ce; Babu wanda ya isa ya kwace makaman Hizbullah saboda kare manufofin Isra’ila ko da kuwa duk duniya za ta shelanta yaki akan Lebanon.
Sheikh Na’im Kassim ya kuma kara da cewa: Ku saurar da kyau ku fahimta! Kasa, da makami da rai, abu ne guda daya, don haka duk wanda yake son kwace abu daya, to dukkanin wadannan guda ukun yake son kwacewa.”
Sheikh Na’im kassim ya kuma ce abinda kwace makamai yake nufi, shi ne shafe samuwarmu, ba kuwa za mu bari hakan ta faru ba.
Babban maatakardar kungiyar ta Hizbullah ya kuma ce: Ba za mu taba yin ko gizau ba akan matsayarmu, domin wannan shi ne matsayi na daukaka, ba kuma da bukatuwa da shaida daga masu aikata laifuka da barna a doron kasa. Ko daga wadanda tarihinsu shi ne haddasa fitina, ko barna.”
Sheikh Na’im Kassim ya ce; Idan kun kashe mu, to jininmu da ya zuba zai tsiro.:
Haka nan kuma ya yi kira ga gwamnatin kasar ta Lebanon da ta dakatar da mika kai bori yana hawa a gaban abokan gaba.
Babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah ya kuma ce; Abu daya kawai da abokan gaba suke bukata shi ne Lebanon ta mika wuya, ta zama a karkashin ikon Isra’ila.”
Sheikh Na’im Kassim ya ce; Idan kuwa Lebanon ta mika wuya, to ta gama rushewa, domin ga Syria nan a gabanmu a matsayin misali, duk abinda yake faruwa acan yaudara ce.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka DRC: Kungiyar M23 Ta Kwace Iko Da Wani Gari Mai Muhimmanci December 13, 2025 Syria: Sojojin “Isra’ila” Sun Kutsa Cikin Yankin Qunaidhara December 13, 2025 Kalibaf: Iran Da Habasha Suna Bunkasa Alakokin Siyasa Da Tattalin Arziki December 13, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan(a) 171 December 13, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan(a) 170 December 13, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan(a) 169 December 13, 2025 Isra’ila Ta Kai Hari A Kudancin Labanon A Ci Gaba Da Keta Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta December 13, 2025 Ziyarar Da Shugaban Rasha Ya Kai Indiya Ta Kara Karfafa Dangantakar Mosko Da Delhi December 13, 2025 Amurka Ta Sanya Sabbin Takunkumi A Bangaren Manfetur Na Venuzuela December 13, 2025 Hamas Ta Ce Ci Gaba Da Kai Hare-Haren Isra’ila Ya Nuna Gazawar Tsarin Duniya Na Dakatar Da Ita. December 13, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci