Radio Nigeria Kaduna Hausa:
2025-11-04@20:49:06 GMT

Gazawar Shugaba Bola Tinibu Ne Ya Sa Sanata Marafa Ficewa Daga APC

Published: 20th, September 2025 GMT

Gazawar Shugaba Bola Tinibu Ne Ya Sa Sanata Marafa Ficewa Daga APC

Shugaban kungiyar goyon bayan Sanata Marafa, Alhaji Surajo Garba Maikatako, ya ce ficewar Sanata Kabir Garba Marafa daga jam’iyyar APC ya kara karfafa masa siyasa tare da jaddada goyon bayansa ga magoya bayansa.

 

A wata sanarwa mai dauke da sa hannun sa da kan sa, Alhaji Maikatako ya bayyana cewa Sanata Marafa ya yanke shawarar ficewa daga jam’iyyar APC ba wani yunkuri ne na kashin kai ba, sai dai an dauki matakin ne na gama-gari bayan tattaunawa da magoya bayan sa.

 

Ya ce tun bayan wannan sanarwar kungiyar ta fara samun sakonni da ziyarce-ziyarcen hadin kai daga fadin jihar Zamfara da Arewa maso Yamma da kuma wajenta, inda da yawa ke bayyana shirin tafiya da sabuwar alkiblar siyasa.

 

A cewarsa, wannan ci gaban alheri ne kuma ya zama wani sauyi a tafiyarsu ta siyasa.

 

Alhaji Surajo Garba Maikatako ya bayyana Sanata Marafa a matsayin daya daga cikin shugabanni masu kishin kasa kuma masu hangen nesa wadanda siyasarsu ta ginu akan adalci, rikon amana da yiwa al’umma hidima.

 

Alhaji Maikatako ya ci gaba da cewa, sabanin ikirari da shugabannin jam’iyyar APC na Zamfara ke yi, Sanata Marafa yana samun goyon bayan talakawa, inda ya ce har yanzu jam’iyyar ba ta lamunta da ficewar sa.

 

Ya yi zargin cewa jam’iyyar APC a Zamfara ta rasa nasaba da siyasa, inda ya nanata cewa, wadanda ake yi wa lakabi da wadanda za su maye gurbin Sanata Marafa ba su da ra’ayin jama’a kuma ba za su iya gabatar da zaben jam’iyyar nan gaba ba.

 

Shugaban kungiyar ya kuma alakanta ficewar Sanata Marafa da gazawar shugaban kasa Bola Tinubu wajen cika alkawuran yakin neman zabe, musamman kan rashin tsaro a jihar Zamfara, duk kuwa da rawar da Sanatan ke takawa a matsayin kodinetan yakin neman zaben jihar a zaben 2023.

 

Ya kuma jaddada cewa kungiyar tasu a yanzu tana shirye-shiryen wani abin da ya bayyana a matsayin yakin neman zaben shugaban kasa mai cike da tarihi, inda ya bukaci magoya bayansa da ‘yan Najeriya masu kishin kasa da su hada kai wajen kwato mulkin dimokaradiyya da dawo da martabar mulki.

REL/AMINU DALHATU.

 

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Marafa Zamfara jam iyyar APC Sanata Marafa

এছাড়াও পড়ুন:

Ziyarar Shugaba Xi A Koriya Ta Kudu Ta Bude Babin Yaukaka Hadin Gwiwar Yankin Asiya Da Fasifik

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Taron APEC Na 2026 Da Za A Shirya A Kasar Sin Zai Bude Sabon Babin Na Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik November 2, 2025 Daga Birnin Sin An Bude Sabon Babin Huldar Sin Da Koriya Ta Kudu November 2, 2025 Daga Birnin Sin Sin: Katsalandan Cikin Harkokin Kamfani Da Netherlands Ta Yi Ya Kawo Tsaiko Ga Tsarin Masana’antu Da Samar Da Kayayyaki Na Duniya November 1, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tsohon Mataimakin Shugaban Amurka Dick Cheney ya mutu
  • Kungiyar Likitocin Kasar Sudan: Rundunar RSF Tana Garkuwa Da Dubban Fararen Hula A Al-Fasha
  • Zamfara Ta Tashi Daga Matsayi Na 36 Zuwa Na 17 A Shekara Biyu Ƙarƙashin Gwamna Lawal — Rahoton BudgIT
  • Uwargidan Gwamnan  Zamfara Ta Yaba Wa  Karamar Hukumar Gusau Bisa Shirin Tallafawa Jama’a
  • Shugaba Xi Ya Mika Sakon Taya Murnar Bude Babban Gidan Tarihi Na Kasar Masar
  • Ziyarar Shugaba Xi A Koriya Ta Kudu Ta Bude Babin Yaukaka Hadin Gwiwar Yankin Asiya Da Fasifik
  • Shin Mene Ne Matsalar Liverpool A Wannan Kakar?
  • Tinubu zai gana da Trump kan zargin kisan Kiristoci a Nijeriya 
  • An Kashe Mutum 3 Yayin Da ‘Yan Bindiga Suka Kai Hari Kan Iyakokin Kano
  • Rikicin PDP: Tsagin Wike ya dakatar da Damagum