Hukumar Alhazai ta Jigawa ta Kiyasta Naira Biliyan 3 Don Ayyukan Hajjin 2026
Published: 12th, December 2025 GMT
Daga Usman Muhammad Zaria
Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta yi kiyasin kashe naira miliyan dubu 3 domin gudanar da aikace-aikacenta a lokacin aikin Hajjin 2026.
Shugaban hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo ya bayyana haka lokacin da ya ke kare kiyasin kasafin kudin sabuwar shekara a gaban kwamatin harkokin addini na majalisar dokokin jihar Jigawa.
Alhaji Ahmed Umar Labbo yace hukumar za ta sayi motar daukar marasa lafia wato ambulance domin dawainiya da mahajjatan da za su gamu da rashin lafiya a lokacin hajji a kasa mai tsarki.
Yana mai bayyana cewar za a yi amfani da wasu daga cikin kudaden wajen kaiwa da komowa yayin aikin hajji.
Sai kama masauki ga ma’aikatan hukumar da ma’aikatan wucin gadi kamar tawagar ma’aikatan lafiya da malamai da ‘yan jarida da ke taimakawa hukumar wajen samun nasarar gudanar da aikin Hajji.
A don haka, Ahmed Labbo ya bukaci maniyyata aikin Hajji da su rika halartar cibiyoyin bita domin koyon ibadar aikin Hajji a aikace bisa doron ilimi.
A nasa jawabin, shugaban kwamatin harkokin addini na majalisar dokokin jihar Jigawa kuma wakilin mazabar Garki, Alhaji Abdu Ila Muku, ya jaddada kudurin kwamatin na duba sansanin Alhazai.
Abdu Muku yace kwamitin zai kuma duba sauran shirye-shiryen hukumar aikin hajji ta jihar domin tabbatar da samun nasarar aikin hajji mai zuwa.
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Hukumar Alhazai Jigawa
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Kano ta haramta kafa hukumar Hisbah mai zaman kanta
Gwamnatin Jihar Kano, ta haramta kafa Hukumar Hisbah mai zaman kanta tana, wadda tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje, yake ƙoƙarin kafawa.
Gwamnatin ta ce kafa hukumar ya saɓa da doka, kuma zai iya zama barazana ga zaman lafiya a jihar.
Zan yi amfani da Salah a wasan Liverpool da Brighton — Arn Slot Zaɓen 2027 ya hana ni korar wasu ma’aikata – BagoA cikin wata takarda da Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya sanya hannu a ranar 8 ga watan Disamba, 2025, gwamnatin ta ce ta gano an fara ɗaukar mutane aiki a hukumar ba tare da neman izini ba.
Gwamnatin ta ce hakan ya saɓa wa Dokar Hukumar Hisbah ta Jihar Kano.
Da yake zantawa da ’yan jarida, Kwamishinan YaɗaLabarai da Harkokin Cikin Gida na jihar, Ibrahim Abdullahi Waiya, ya ce Hukumar Hisbah ce kaɗai doka ta amince da ita wajen gudanar da ayyuka a jihar.
Ya ce kafa wata ƙungiya ko hukuma ta daban ba bisa ƙa’ida ba na iya kawo cikas ga zaman lafiya.
Umarnin ya bayyana cewa babu wani mutum ko ƙungiya da ke da ikon ɗaukar mutane aiki, tara su, horas da su ko tura su domin kafa wata hukumar Hisbah mai zaman kanta a jihar.
Gwamna Abba, ya kuma ayyana ayyukan hukumar a matsayin haramtattu, tare da gargaɗin cewa duk wanda ya yi amfani da kayan Hisbah, alamominta ko ikonta ba tare da izini ba zai fuskanci hukunci.
Gwamnan, ya umarci jami’an tsaro, ciki har da ’Yan Sanda, DSS, NSCDC, da sauran hukumomin tsaro, da su binciki waɗanda suka kafa sabuwar hukumar.
Gwamnatin ta kuma gargaɗi jama’a cewa duk wanda ya shiga, ya goyi baya ko ya haɗa kai da sabuwar hukumar, zai fuskanci hukunci.
An shawarci waɗanda aka ɗauka aiki su fice daga hukumar nan take tare da komawa ofishin Hisbah, ko Ƙaramar Hukuma.
Umarnin ya kuma tanadi hukunci ga waɗanda suka saɓa wa dokar, ciki har da gurfanar da su a gaban kotu bisa laifin gudanar da taro ba bisa ƙa’ida ba, kwaikwayon hukumomin gwamnati, da kafa rundunar tsaro ba tare da neman izini ba.
Wannan umarni ya fara aiki nan take, kuma za a yaɗa shi a kafofin watsa labarun Gwamnatin Jihar Kano.