Akwai fargaba kan noman ranin bana
Published: 14th, December 2025 GMT
A yayin da lokacin fara noman rani ya zagayo, manoma sun nuna fargabarsu, sakamakon matsalolin da suke hararowa, musamman faduwar farashin amfanin da aka noma a daminar bana da kuma tashin gwauron zabon kayan noma.
A duk shekara, manoman rani kan fara shiri da zarar an fara kawar da kayan amfanin noman damina, inda suke gyaran goma.
A yanzu da lokacin ranin ya zagayo, wasu manoma a jihohin Sakkwato da Yobe da Katsina sun bayyana fargaba kan yadda za ta kasance a wannan karon.
Alhaji Haruna, manomi a yankin Madatsar Ruwa ta Sabke da ke shiyyar Daura a Jihar Katsina, ya shaida wa wakilinmu yadda suke tunanin fuskantar lamarin.
Buɗe cibiyar horas da sabbin sojoji a Kudu zai taimaka — Janar Shaibu Sojoji sun daƙile harin ’yan ta’adda a Borno“Duk da cewa, tsadar kayan amfanin noman damina da na rani yana shan bambam kamar yadda yake ko a wajen aikin, to amma dole mu yi la’akari da irin yadda noman daminar bana ta kaya. Da damina mun ga yadda muka zuba kudi tun daga gyaran gona, yin haro da huda da shuka, ga tsadar yin noman, amma Allah sai Ya sa kayan suka yi wata irin arhar da ba mu yi zato ba. Wanda ya zuba jarin miliyan a gona da wuya ya samu rabin kudin da ya kashe.
“To ina ga shi noman ranin? Shi fa kullum kana gonar kuma kullum sai ka zuba kudi ko da kuwa na man injin ban-ruwa ne. Ga can baya wajen gyaran filin yin noman har zuwa yin dashen abin da za a noma. Saukin ma mu a nan ana samun kasuwar tattasai da tumatiri.
“Amma irin yadda muke ganin kayan aikatawar na tsada, amfanin kuma na yin arha, dole mu tsaya mu dan jinkirta mu ga yadda yanayin zai kama. Ka san shi noman rani lokacin ba ya karewa har sai ruwan damina ya zo. Abin da dai muke fata shi ne, gwamnati ta shigo ciki don karfafa mana guiwa.”
Fargabar sake asaraMalam Hassan Dogon Faci a Karamar Hukumar Batsari ta Jihar Katsina, ya bayyana yadda tsadar takin zamani da ta irin suka zame musu manyan kalubale, baya ga faduwar farashin amfanin da aka noma a daminar bana.
“Babban abin da muke fargaba shi ne, ta ina za a fara? Shin tsadar iri ko kuwa ta taki, tunda dai dole noma ne mai bukatar taki. Yadda noman damina ya ba manoma kashi na daga cikin dalilan da masu noman ranin ke zullumin sake zuba wata dukiyar ta wannan fuskar. Farashin kayan amfanin gona ya fadi warwas a bana, duk da cewa kayan noman sun yi mummunar tsada.
“Ga tsadar takin zamanin da ake fuskanta. Domin a gaskiya duk wanda a wannan shekarar ya fara noma na damina, to da wuya ya sake yi a shekara mai zuwa. Wasu wuraren an samu amfani, a wasu wuraren kuma sai dai addu’a.”
Manomin ya ce, matsalar da noman danima ya fuskanta ta yi wa noman ranin bana shinge a yankinsu. “Yankin Kasai da su Nahuta, da ma can ba a yin noman rani saboda babu ma’ajiyar ruwa, koramu ne gare su masu wucewa. Bayan noman damina sun fi yin noman dankali da rogo, musamman a wannan yanki na yammacin Batsari. Idan ma akwai inda ake yin noman ranin to sai dai wajen su Kagara da Zamfarawar Madogara.”
‘Ba ma sa ran tallafin noman rani’
Amma duk da haka, Saminu Mayenti a yankin Gabashin garin Batsari, ya shaida mana irin shirin da suke yi da cewa akwai yiwuwar masu yi a bana su fi na bara yawa.
“Mu a nan yankin Saki-jiki mun shirya wa wannan noma, kuma tuni ayyukan noman sun kankama. Ka ga yanzu muke ta hada-hadar gyaran gonakin domin yanzu ne daidai saboda lokacin bai kure ba. Sannan ina tabbatar maka, wadanda za su yi noman a bana sun ninka na bara kuma mafi yawa matasa.”
To ko matsalar tsadar kayan noman da faduwar farashin amfanin noman damina da aka samu ba zai kawo masu cikas ba? Saminu ya ce, abin da ya fi da mun su shi ne tsadar iri da kuma rashin takin zamani.
“Gaskiya ba mu sa ran samun tallafin takin noman rani daga gwamnati, saboda ko an ce ga shi an bayar a karshe kasuwa za mu je mu sayo shi kuma da tsada. Shi ya sa wasu daga cikin manoman suke tanadar iri da takin da kuma maganin kwari tun da wuri su ajiye. Amma fa ga masu halin sayen.”
Wani dattijo, Malam Shehu daga garin Girka ta Karamar Hukumar Kaita, ya ce, sama da shekara 50 yana noman rani a yankin, amma a bana akwai kalubale saboda tashin farashin kayan noma har a yanzu.
“Noman daminar ya ba mu kashi, yanzu kuma muna ganin alamu ga shi wannan noman ranin. Wadanda suka yi noman tumatir na damina da tattasai, munga yadda ta kaya. Misali, mun ga yadda attarugu ya yi tsada a baya, amma yanzu har na naira dari ana iya ba ka kuma ya biya bukata.
“Amma duk da haka, wannan bai kashe mana kwarin guiwa ba, musamman ga wannan Madatsar Ruwa ta Dankaba wanda ya shigo har wannan yankin. Amma gaskiya idan ba gwamnati ta shigo da tallafinta ba, musamman raba takin zamani cikin lokaci da maganin kwari [akwai damuwa]. Batun iri kuwa wannan kowa tashi ke fisshe shi,” inji Malam Shehu.
A yankin Gallu da ke Karamar Hukumar Mashi kuwa, manoman tuni sun yi nisa a noman ranin. Wani matashi, Sabi’u ya ce, tun da ruwan damina ya fara ja ya fara gyaran inda zai yi noman.
“Kasan nan mu nan yankin mun fi mayar da hankali a noman rani fiye da na damina, domin ya fi kawo mana riba. Muna noma tattasai, tumatiri, albasa, attarugu da sauran su. Muna kaiwa kasuwar Mai’aduwa da Mashi da Daura, kuma akwai masu yin lodi zuwa Kudu. Yanzu ma na kara filin da zan noma su Kabeji da Latas da sauran irin su.”
Da aka tuntubi matashin manomin kan tsadar kayan noman ga kuma saukar farashi, sai ya ce, “ai duk hannun da ya kirga riba, to dole wata rana ya kirga faduwa. Ga noma in ba a ci riba a wannan bangare ba, sai a ci a wani bangaren da ba a zato.” in ji Sabi’u Gallu.
Manoman rani a Sakkwato na neman tallafi
Manoman rani a Jihar Sakkawato sun koka kan yadda harkar take tabarbarewa a sakamon rashin tallafi daga gwamnati da kungiyoyin sa-kai. Sun bayyana fargabar cewa muddin ba a samu saukin man fetur da takin zamani ba, to harkar noman rani ba za ta farfado ba, sai dai a rika yi don samun abinci kawai, amma ba don sana’a ba.
A halin da ake ciki harkar noman rani ta kankama a Jihar Sakkwato, amma kuma manoma na kukan matsaloli uku.
Manomin albasa, alayyahu da daras da barkono da dankali, a Karamar Hukumar Sakkwato ta Arewa, Alhaji Lawali Muhammad mai shekara 53 ya ce, “Muna da matsaloli uku da ke hana mana bunkasa a harkar noman rani: na farko matsalar man fetur a kullum irina matsakaicin manaomi, a tsakanin man da ma’aikaci daya sai ka kashe dubu 10, kullum sai na dauki ma’aikata 6.
“Na biyu ba a samun takin zamani daga gwamnati, babu wani ma’aikaci da zai gaya maka ya samu takin zamani. Ba a samun maganin kashe kwari ko haki, manomi da kansa yake yin komai, gishirinka dai jikinka ba wani tallafi daga gwamnati, wanda ake bai wa tallafin ba su ke aikin ba,” a cewarsa.
Ya ce harkar noma za ta iya dawo da hayacinta in gwamnatoci suka daina baiwa manoman riga da siyasa kayan aiki suka dawo baiwa manoman gaskiya.
Muhammad Wurno mai shekara 45, ya ce a yanzu lokaci ne na noman albasa da karas da Dankali, amma lokacin dashen tafarnuwa ya wuce duk wanda bai yi ba sai a wata shekara.
Ya ce, “Mun fara noman rani da kanmu, babu wani manomin gaskiya da zai tsaya jiran gwamnati don ya san babu abin da za ta yi. Amma da za a samar mana da tallafin kudi mu sayi man fetur da takin zamani da lamarin zai iya sauyawa a harkar noman rani a Sakkwato da Arewa baki daya.”
Matsalar ban-ruwa
Shi ma wani manomin, Kamilu Yusuf Goronyo mai shekara 55, ya ce manoman rani suna cikin damuwa sosai musamman yadda gwamnati ba ta tallafa musu gaba daya. “Ka dubi yadda aka kyale Gulbin Goronyo ya cushe an ki yashe shi kasa ta cika gulbi ruwa ba sa tsayi a wurin, idan rani ya kai tsakiya sai ka ga ruwa sun yanke saboda babu su a gulbi, in damina ta tsaya an samu ambaliya tun da babu wurin ajiye su.
“Mu manoma a yankin Sakkwato, Kebbi da Zamfara idan aka yashe mana gulbin nan an taimaka mana kuma noma zai dawo da martabarsa duk da akwai matsalarfetur da takin zamani,” in shi.
Duk da cewa Gwamnatin Jihar Sakkwato ta ware Naira biliyan 33 domin gyara Madatsar Ruwa ta Lugu a Karamar Hukumar Wurno domin bunkasa aikin noma, amma har yanzu ba a kammala ba, kusan shekara biyu. A watan Agusta ta sake ware wasu Naira biliyan 22 don sayen taraktocin noma don bunkasa noman na rani. Amma duk haka, bai hana manoma kokawa ba kan matsalolinsu.
Aminiya ta so ta ji ta bakin gwamnatin jiha kan shirin da suke da shi a harkar noman rani na wannan shekara duk da ana matakin karshe a noman, amma ba ta yi komai ba a lokacin dashen farko dana biyu.
Duk kokarin da wakilinmu ya yi domin jin ta bakin Kwamishinan Noma a jihar, Alhaji Tukur Alkali, abin ya ci tura.
Ambaliyar gonaki da damina
A yayin da manoman rani a jihohin Yobe da Jigawa suka dukufa da aiki tun kimanin watanin biyu da suka shude, gwamnatocin jihohi na ikirarin cewa sun samar musu kayayyakin gudanar da noman.
A Jihar Yobe, tunin suka dukufa wajen kula da gonakinsu musamman na shinkafa, alkama, masara, waken soya, tumatiri, albasa, taruhu, kubewa da sauransu. Amma sun koka kan yadda ambaliyar da aka samu bara ta lalata yawancin gonakin ba tare da gwamnati ta gyara musu ba duk da kokawa da suke yi.
Haka nan wasu manoman na cewar babbar matsalarsu ita ce karancin takin zamani lura da cewar takin da gwamnatin ta samar musu kadan ne, sakamakon dokar hana sayarwa da shigar da wasu nau’ukan takin zamani saboda matsalar tsaro.
Barazanar rashin taki: Murna ta koma ciki
Wani manomin alkama, Alhaji Ago Dagona ya ce, shi da sauran manoman rani a yankin Dagona a Karamar Hukumar Bade sun noma alkama da shinkafa kuma Alhmadulillah amfanin gonarsu ya dauki harami, amma suna cikin damuwa kan karancin taki duk da cewar gwamnatin jihar ta taimaka musu da irin shuka mai kyau da maganin feshin kwari da kananan motocin noma wadda hakan ya taimaka musu.
Alhaji Haruna BD a Karamar Hukumar Jakusko ya ce, noman shinkafarsu a bana ta yi kyau, domin kuwa “in ba don karancin taki ba ma da muke fuskanta ba, ai da lamarin babu kama hannun yaro, domin kuwa takin yayi tsada tunda ba su samu a wadace.”
Shi kuwa Malam Auwalu a yankin Fika mai noman kayan miya ya ce, babbar matsalar shi da suran manoman rani ita ce, ga shi tun tunin sun yi dashen, amfanin lambunsu, amma karancin takin zamani da na maganin feshin kwari wadda a kullum gwamnatin na ikirarin tana ba su amma ba ya isowa gare su.
A ’yan watanin baya gwamnan Jihar Yobe ya kaddamar da kayayyakin aikin noman damina da na rani da suka hada da motocin noma manya da kanana, injunan ban ruwa, magungunan feshin kwari, takin zamani na ruwa da mai tsaba da makamantan su don saukaka wa manoman.
Da Aminiya ke tuntubi wani masani noman rani, Malam Abdullahi Ahmed a kan ko korafin da manoman zai iya shafar irin amfanin da za su samu? Ya ce, tabbas rashin sa taki ga amfanin gonar kan iya kawo koma baya ga amfanin gonarsu, haka rashin maganin kwari ma babbar matsalar ce.
Tallafin kayan aikin noma a Jigawa
A Jigawa gwamnatin jihar ta ce babu abin da ba ta samar wa manomanta ba don su kai ga nasara, ta hanyar tallafin iri, taki, kayan aiki na zamani, horarwa kan sabbin dabaru, da nufin habaka noma, tabbatar da tsaron abinci, da kuma mayar da noma kasuwanci mai riba.
Gwamna Umar Namadi ya ce gwamnatin jihar ta mayar da hankali kan noma rani a matsayin mafita ga matsalar ambaliyar ruwa da ke ci gaba da faruwa, wadda galibi ke lalata gonaki.
Wani manomin alkama da shinkafa daga Karamar Hukumar kafin Hausa Alhaji Hamisu Takaji ya ce “A Jigawa musamman man mu dake noma alkama da shinkafa babu abin da zamu ce sai godiya, illa dan abin da ba a rasa ba na barnar makiyaya.”
Malam Isiyaku Nomau a Karamar Hukumar Auyo, ya ce gwamnatin jihar takan taimaka da wasu abubuwan amma “abubuwan da ake cewar ana ba mu tallafin suna ne kawai domin ala tilas a mafi yawan lokaci sai shiga kasuwanni don nemowa musamman ma takin zamani, injunan ban ruwa da sauran su.”
Malam Abdulsalam Yelwa mai noman alkama a Karamar Hukumar Kafin Hausa ya ce, babbar matsalarsu ita ce makiyaya da a duk shekara sukan far wa amfanin don haka suke rokon gwamnatida ta yi wani abu a kai don ganin sun tsira daga barnar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Noman rani gwamnatin jihar ta a Karamar Hukumar harkar noman rani babbar matsalar manoman rani a daga gwamnati karancin taki wani manomin noman rani a Wani manomin a noman rani noman ranin harkar noma duk da cewa
এছাড়াও পড়ুন:
Dan sanda ya yi batan dabo a bakin aikinsa a Katsina
Wani dan sandan mai suna Ahmed Tukur ‘Yantumaki ya yi batan dabo yayin da yake a bakin aikinsa a Babban Ofisishin ‘Yan sanda na Karamar Hukumar Danmusa da ke Jihar Katsina.
Bayanai sun nuna cewa, a ranar 25 ga watan Nuwamba, 2025 jami’in ya je bakin aiki inda ya ajiye jikkarsa da kular abincinsa a ofishinsu da ke cikin garin Danmusa sanna ya sanya hannu a kan rajistar kama aiki ta wannan rana, kuma ya nemi izni ya fita da nufin zai je ya sawo wani abu waje. Inda tun daga wannan lokaci ba’a sake ganinsa ba har kawo yanzu.
Da Aminiya ta tuntubi mahaifinsa mai suna Malam Tukur ‘Yantumaki don jin ta yadda ya samu labarin batan dansa sai ya ce, shi ma sai bayan kwana biyu da faruwar lamarin ne ‘yan sanda suka fada masa.
Malam Tukur ya ce, “’yan sandan ne da kansu suka zo har nan cikin gidana a karkashi jagorancin Babban Jami’in ‘Yan sanda na Karamar Hukumar Danmusa, DPO Isah Sule. Kuma shi ne ya fada min cewa, dana ya je aiki kwana biyu da suka wuce ya ajiye kayansa sannan ya sa hannu ya fita waje da nufin zai sawo wani abu amma ba a sake ganinsa ba.”
Ya ci gaba da cewa, “ya kuma bayyana min cewa, suna bakin kokarinsu don ganin sun gano shi don haka mu taya su da addu’a kuma mu sauke Alkur’ani. Ya kuma bayyana min cewa, sun yi ta kiran wayoyinsa amma ba sa samun, saboda duk wayoyin dana a kashe suke, sun ce, kuma duk lokacin da suka yi kokarin tirakin din layikansa sai na’urar binciken ta nuna masu ba ta iya ganin inda yake.”
Da yake wa Aminiya karin bayani yayan jami’in dan sandar da ya bata mai suna Ibrahim Tukur ya ce, “tun ranar da suka zo suka fada mana zancen batansa har yau babu wanda ya sake tuntubarmu game da zancen. A namu bangare, mun yi kokarin sanya labarin batansa a kafafen sada zumunta kuma mun samu wasu manyan don su taimaka mana su yi wa Kwamishinan ‘Yan sanda naJihar Katsina bayanin halin da ake ciki. Kuma muna nan muna kara jira mu ji bayanan da za su dawo mana das u tunda yake sun yi alkawari taimakawa.”
A cikin damuwa mahaifin dan sandan da ya bata wanda tunanin abin day a faru da dansa ya sa rashin lafiya ta kama shi yana kwance ya sheda wa Aminiya cewa, “ ina kira da babbar murya ga Gwamna Jihar Katsina Dakta Dikko Radda da Kwamishinan ‘Yan sanda na Jihar Katsina da su tabbatar sun gano min dana kuma sun dawo min da shi cikin ‘yan’uwansa lafiya, su tuna wannan hakki ne a kansu.
“Bai yiyuwa a ce, mutum kuma jami’in dan sanda da suka ce mana ma a lokacin da ya bace yana dauke da bindigarsa kuma a tsakiyar gari, wato tsakanin ofishin ‘yan sanda zuwa masallacin Juma’a ya bace kamar wata dabba. Ba duriyarsa ba kuma wani bayani gamsasshe ballanata kuma wani nuna damuwa daga bangarensu.”
Ya kara da cewa, “ba a gano inda yake ba, babu wanda ke yi min bayani game da inda yake, a gaskiya ma babu wanda ya nuna wata damuwa sosai daga bangaren gwamnati. Shin hakan yana nufin babu wanda ya damu da shi a matsayin dan sanda kuma babu wanda ya damu da mu a matsayinmu na talakawa? Shin haka kuwa labarin zai kasance idan da a bin ya faru da daya daga cikin ‘ya’yansu ne?”
Aminiya ta yi kokarin jin ta bakin jami’an ‘yan sanda na Jihar Katsina, inda ta farad a kiran DPO Isah Sule na Karamar Hukumar Danmusa amma hakan ya ci tura, domin layin wayarsa baya shiga sannan kuma bai bayar da amsar sakon da aka tura masa a waya ba.
Haka kuma Mai Magana da Yawun ‘yan sandar Jihar Katsina DSP Abubakar Sadik Aliyu wanda wakilin Aminiya ya tura wa sakon kart a kwana ba tare day a maido da amsa bat un jiya, daga bisani amsa kiran waya inda ya bayyana wa wakilinmu cewa, ya yi tafiya amma zai bincika yadda lamarin yake sannan ya yi bayani.