Sakkwatawa na murnar kisan da sojoji suka yi wa mataimakin Bello Turji
Published: 10th, December 2025 GMT
Al’ummar ƙaramar hukumar Sabon Birni da ke jihar Sakkwato sun bayyana farin ciki bayan samun labarin kashe fitaccen ɗan bindiga da ya dade yana addabar yankin gabashin jihar, Kacalla Kallamu.
Rundunar Sojoji ta 8 ta hallaka jagoran ’yan bindiga, Kachalla Kallamu, a wani samamen haɗin gwiwa da aka kaddamar a ƙaramar hukumar Sabon Birni.
Wata majiyar soja da ta tabbatar da lamarin ga manema labarai a ranar Talata ta bayyana samamen a matsayin “babbar asara ga cibiyar ’yan bindigar Bello Turji,” tana mai cewa Kallamu shi ne babban na hannun daman Turji.
A cewar majiyar, an kashe Kallamu tare da wani daga cikin manyan masu samar wa Turji kayayyakin aiki a lokacin samamen da aka gudanar da safe a kauyen Kurawa ranar Litinin.
Majiyar ta ƙara da cewa aikin ya samu muhimmiyar gudunmuwar kungiyoyin sa‑kai na yankin.
“Mun dade muna bibiyar Kallamu. Kashe shi wata babbar nasara ce wajen raunana karfin ’yan bindigar da ke Sabon Birni da kewaye,” in ji majiyar.
Mamacin, wanda asalin ɗan Garin Idi ne a Sabon Birni, ya dade yana addabar al’ummar yankin.
Ana zargin ya gudu zuwa Jihar Kogi bayan ya tsere wa luguden wutar sojoji a watan Yuni 2025, amma ya sake shigowa yankin kwanan nan ba tare da an sani ba.
Majiyar ta yaba da ƙarin bayanan sirri da ake samu daga al’ummomin yankin, tana mai cewa haɗin kai tsakanin mazauna yankin da jami’an tsaro ya taka muhimmiyar rawa wajen nasarorin baya‑bayan nan.
Manema labarai sun ruwaito cewa an ci gaba da murnar labarin a Sabon Birni, yayin da mashawarcin musamman ga Gwamna Ahmad Aliyu kan harkokin tsaro, Kanal Ahmed Usman (mai ritaya), ya yaba wa dakarun bisa “ci gaba da jajircewa da ƙwarewa” wajen yaƙi da ’yan bindiga.
Mutanen garin Sabon Birni sun fito maza da mata suna murnar nasarar da aka samu, har suna cewa suna jin wannan rana kamar ta Sallah.
Sun yi fatan a ci gaba da samun nasarori irin wannan domin kawar da ’yan bindiga a yankin, a jihar, da kuma Arewacin Najeriya gaba ɗaya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Sakkwato yan bindiga
এছাড়াও পড়ুন:
Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima Ya Isa Abidjan Wajen Rantsar da Shugaba Ouattara
Daga Bello Wakili
Mataimakin Shugaban Najeriya, Kashim Shettima, ya isa Abidjan na kasar Côte d’Ivoire, domin wakiltar Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu a wajen rantsar da Shugaban Alassane Ouattara a wa’adinsa na hudu.
Za a rantsar da Shugaban ne a yau Litinin, 8 ga watan Disamban 2025, a Fadar Shugaban Kasa da ke Abidjan, wanda shugabanni daga kasashen Afrika da sauran manyan baki daga sauran kasashen duniya za su halarta.
Shugaba Ouattara ya sake lashe zabe ne a ranar 25 ga watan Oktoban 2025, inda ya sake samu wani sabon wa’adi na jagorantar kasar. Sake Rantsar da shi na nuna da ci gaban da dimokuradiyya a kasar ta Côte d’Ivoire da kuma kyakkyawar dangantakarta da Najeriya.
A cewar Fadar Shugaban Kasar, halartar Mataimakin Shugaban Kasa Shettima a taron na tabbatar da jajircewar Najeriya kan goyon bayan mulkin dimokiradiyya a yammacin Afrika. Najeriya na ci gaba da jaddada muhimmancin bin muradin jama’a da tabbatar da sauyin mulki cikin lumana a yankin.
Najeriya da Côte d’Ivoire na da kyakkyawar hulda ta aiki karkashin ECOWAS, Tarayyar Afrika, da kwamitin kasashe biyu, inda suke yin hadin gwiwa a fannoni irin su tsaro, kasuwanci, noma, yakar safarar mutane, da tattalin arzikin dijital. Dubban al’ummar ‘yan Najeriya da ke Côte d’Ivoire ma na kara zurfafa dangantakar tattalin arziki da al’adun kasashen biyu.
Ana sa ran Mataimakin Shugaban Kasa zai koma Abuja bayan kammala taron rantsarwar.