Aminiya:
2025-11-04@12:30:13 GMT

Mutum 1,666 ne suka kashe kansu a Legas cikin shekaru biyar – ’Yan sanda

Published: 19th, September 2025 GMT

Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ta ce akalla mutane 1,666 mazauna jihar Legas sun rasa ransu ta hanyoyin da ba su dace ba, ciki har da kashe kansu, tsakanin farkon 2020 zuwa karshen 2024.

Wannan bayani ya fito ne daga bakin likitan binciken gawarwaki na rundunar, ACP Samuel Keshinro, yayin gabatar da rahoton bincike kan kisan mata a wani taron da aka gudanar a jihar ranar Alhamis.

Cutar Kwalara ta kashe mutum 58 a Bauchi Amurka ta hau kujerar-na-ƙi kan buƙatar MDD ta tsagaita wuta a Gaza

A cewar Keshinro, rahoton ya mayar da hankali ne kan abubuwan da suka shafi kisan kai, kashe kai, hatsarurruka da sauran hanyoyin mutuwa da ba su da alaka da cuta, domin wayar da kan jama’a da ƙarfafa fafutuka kan matsalar kisan mata.

Bayanan da aka raba a wajen taron sun nuna cewa daga cikin mutuwar 1,666, 350 mata ne, yayin da 1,306 kuma maza ne, sai mutum 10 da ba a iya tantance jinsinsu ba.

Keshinro ya ce an tattara bayanan ne domin samar da madogara mai ƙarfi wajen yanke shawara da kuma wayar da kan jama’a kan hatsarin kisan mata.

Ya ce bayanan sun nuna cewa mafi yawan kisan mata ana aikata su ne daga abokan rayuwarsu na kusa.

“Mun fito da abubuwan da muka gano ta amfani da bayanan da ke hannun ’yan sanda a ofishin CID na jihar. Mun gano cewa daga cikin mutuwar mata 350, kusan guda 70 kisan abokan zamansu ne.

“Wannan yana nuna irin raunin da mata ke ciki, musamman a inda ake tsammanin za su samu ƙauna da kariya. Kuma ya zo a daidai lokacin da Majalisar Dinkin Duniya ta ware ranar 25 ga watan Nuwamba a matsayin ranar yaki da cin zarafin mata.”

Ya kuma ba da shawarar a rungumi amfani da tsarin adana bayanai ta kwamfuta da kuma inganta hanyoyin tattara bayanai a binciken laifuka.

A nasa jawabin, Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Legas, Olorundare Jimoh, ya bayyana cewa bisa ga bayanan da aka tattara cikin shekara guda, adadin kisan mata a jihar bai kai yadda ake tsammani ba idan aka kwatanta da yawan jama’ar jihar.

উৎস: Aminiya

এছাড়াও পড়ুন:

Zargin Kisan Kiristoci: Najeriya ba ta yadda da cin zarafin addini — Tinubu

Shugaba Bola Tinubu ya mayar wa da Shugaban Amurka, Donald Trump martani cewa Najeriya ba ta yadda da duk wani nau’in zarafin addini.

Tinubu, ya yi wannan bayani ne bayan Trump ya sake sanya Najeriya cikin jerin ƙasashen da ake kiran “Ƙasashen da ke da Babbar Matsala wajen ’Yancin Addini.”

PDP ta dakatar da Anyanwu da wasu ’yan tsagin Wike Sharrin son auren Mai Wushirya aka yi min — Mansura Isa

Trump ya yi iƙirarin cewa Kiristoci a Najeriya na fuskantar barazana, amma ya sha alwashin cewa Amurka za ta kare su.

A cikin wani saƙo da ya wallafa a kafafen sada zumunta, Trump ya rubuta cewa: “Addinin Kirista yana fuskantar babbar barazana a Najeriya. Ana kashe dubban Kiristoci.”

A ranar Asabar, Tinubu ya mayar da martani ta kafar sada zumunta, inda ya ce Najeriya ƙasa ce mai dimokuraɗiyya wadda kundinta ya tabbatar da ’yancin yin addini.

“Najeriya tana da cikakken tanadi a kundinta da ya tabbatar da ’yancin yin addini,” in ji Tinubu.

“Tun daga shekarar 2023, gwamnatina na aiki tare da shugabannin Kiristoci da Musulmai don magance matsalolin tsaro da ke shafar jama’a daga kowane ɓangare da addini.”

Ya ƙara da cewa, kiran Najeriya ƙasa mai matsala wajen gudanar addini ba gaskiya ba ne.

“Za mu ci gaba da kare ’yancin kowane ɗan ƙasa na yin addininsa cikin walwala. Najeriya ba ta goyon bayan zaluncin addini ko kaɗan,” in ji Tinubu.

Ya kuma ce Najeriya za ta ci gaba da haɗa kai da Amurka da sauran ƙasashe domin inganta zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin mabiya addinai daban-daban.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An kama barawo da wayoyin sata 17 a taron sauya shekar Gwamnan Bayelsa
  • Karuwanci da zubar da cikin ’yan mata ’yan gudun hijira ya karu a Maiduguri
  • ’Yan Sandan Legas sun ayyana neman Sowore ruwa a jallo
  • Yadda matata ta ɓace a Abuja aka tsince ta a Sakkwato
  • Ministar Jin Dadin Jama’a ta Sudan: Mayakan RSF Sun Kashe Mata 300 Da Yi Wa 25 Fyade A El Fasher
  • Ƙasashen Da Ba Su Yanke Hukuncin Kisa A Duniya Ba
  • An Kashe Mutum 3 Yayin Da ‘Yan Bindiga Suka Kai Hari Kan Iyakokin Kano
  • Kisan Kiristoci: Za mu kai hari Najeriya — Trump
  • Dalilin Gwamnatin Jihar Kuros Riba Na Raba Wa Manoma Taraktoci
  • Zargin Kisan Kiristoci: Najeriya ba ta yadda da cin zarafin addini — Tinubu