Ya Kamata Sin Da Amurka Su Hau Turbar Hadin Gwiwa Da Samun Moriyar Juna A Sabon Lokaci
Published: 21st, September 2025 GMT
A daren ranar 19 ga wannan wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na kasar Amurka Donald Trump sun tattauna ta wayar tarho, inda shugaba Xi ya jaddada cewa, alakar Sin da Amurka na da matukar muhimmanci, Sin da Amurka na iya cimma nasarar bai daya da wadata tare, ta yadda za su amfani kawunansu, da ma sauran sassan duniya baki daya.
A cikin wannan tattaunawar, shugaba Xi ya bayyana ra’ayi da matsayin Sin kan batutuwan dake shafar dangantakar kasashen biyu, ya yi nuni da cewa, ya kamata Sin da Amurka su yi kokari da hadin gwiwa, kana kasar Amurka ta magance daukar matakan kayyade ciniki daga bangare daya, ta haka za a magance kawo illa ga nasarorin da kasashen biyu suka samu yayin shawarwarinsu a zagaye da dama. Game da batun TikTok, ana son ganin kamfanoni su tattauna bisa tushen ka’idojin kasuwanci, da cimma daidaito bisa dokokin kasar Sin da ka’idojin daidaiton samun moriya, ana fatan Amurka za ta samar da yanayin ciniki mai bude kofa da adalci da rashin nuna bambanci ga kamfanonin Sin da suka zuba jari a Amurka. Shugaba Trump ya bayyana cewa, Amurka tana fatan za a ingiza hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya a tsakanin kasashen biyu, kuma zai nuna goyon baya ga tawagogin kasashen biyu da su yi shawarwari don daidaita batun TikTok yadda ya kamata.
Akwai sharhin da aka yi game da cewa, tattaunawar dake tsakanin shugabannin kasashen biyu ta shaida cewa, Sin da Amurka sun samu muhimmin ci gaba kan cimma yarjejeniyar daidaita batun TikTok. Direktan ofishin nazarin siyasar kasa da kasa na kungiyar masana masu nazarin manufofin duniya na kwalejin ilmin zamantakewar al’ummar kasar Sin Zhao Hai ya yi fatan cewa, idan Sin da Amurka suka iya daidaita batun TikTok, to za a samar da sharadi ga kamfanonin kasashen biyu a kan yadda za su yi harkokin kasuwanci a kasuwar kasashen biyu, inda ta hakan za a sa kaimi ga Sin da Amurka wajen ganin sun daidaita sauran batutuwan tattalin arziki da cinikayya baki daya. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Baje Kolin CIIE Ya Bayar Da Tabbaci Ga Duniya
A sa’i daya kuma, kamfanonin kasashen ketare sun samu tabbacin bunkasar kasar Sin ta hanyar halartar bikin na CIIE. Wasu shugabannin kamfanonin kasashen ketare sun bayyana cewa, kasar Sin na da manyan kasuwanni masu bude kofa, da yanayin zuba jari mai dacewa, tare da manufofi masu karko, wadanda suke janyo hankulansu matuka.
Haka zalika kuma, a matsayin dandalin shigowa da kayayyaki na musamman a duniya, bikin CIIE ya samar da tabbacin cimma moriyar juna ga kasashen duniya. A bana, a karon farko, an kafa dandalolin nune-nunen kayayyaki daga kasashe mafiya fama da talauci, tare da fadada yankunan nune-nunen kayayyakin kasashen Afirka. A halin yanzu, akwai kamfanoni har 163 daga kasashe mafiya fama da talauci da suka halarci baje kolin na CIIE, adadin da ya karu da kaso 23.5 bisa dari, idan aka kwatanta da na bara. Kana, yawan kamfanoni daga kasashen Afirka ya karu da kaso 80 bisa dari a wannan karo. (Mai Fassara: Maryam Yang)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA