Najeriya: Jirgin Sojojin Kasar Yana Kan Hanyarsa Ta Zuwa Portugal, Amma Ta Sauka A Burkina Faso
Published: 9th, December 2025 GMT
Kakakin rundunar sama ta tarayyar Najeriya, wato ‘Nagerian Air Force’ Ehiment Ejodame ya bayyana cewa jirgin wani jirgin saman rundunar dauke da mutane 11 ya yi saukan gaggawa a kasar Burkina Faso a ranr litinin da ya gabata.
Jiridar Daily Trust ta Najeriya ta nakalto Ejodame yana fadar haka a yau Talata ya kuma kara da cewa kungiyar kasashen AES sun tilastawa jirgin sauka a Bobo Dioulasso na Burkina Faso bayan zargin cewa jirgin ya keta hurumin sararin samaniyar kasar ba tare da izini ba.
A halin yanzu dai ana saran za’a warware matsalar da ke tsakanin kasashen biyu sannan jirgin zai kama hanyarsa zuwa kasar Portigal kamar yadda aka tsara.
Labarin ya kara da cewa, jirgin ya tashi daga birnin Lagos sannan ya fuskanci matsala sannan ta yi saukan gaggawa Bobo-Dioulasso a Burkina faso.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Saudiya da Qatar Zasu Gina Layin Dogo Mai Sauri Tsakanin Kasashen Biyu December 9, 2025 Nigeria Ta Aike Da Jiragen Yaki Zuwa Kasar Benin Domin Dakile Yunkurin Juyin Mulki December 9, 2025 Pakistan ta Bai Wa Taliban Ta Aghanistan Zabi A Tsakanin Mu’amala Da Ita Ko Da ‘Yan Ta’adda December 9, 2025 Kasashen Iran Da Turkiya Za Su Bunkasa Alakarsu A Fagen Ilimi Da Musayar Fasaha December 9, 2025 An Fito Da Gawawwakin Shahidai 98 Da Aka Binne Cikin Gaggawa A Asibitin “Ash-Shifa” December 9, 2025 Talauci Yana Karuwa A “Isra’ila” Bayan 7 Ga Watan Oktoba December 9, 2025 AU Ta yi Tir Da Harin RSF A Makarantar Kananan Yara Da Ya Kashe Mutane 80 December 8, 2025 MِِِِDD: Kisan Kare Dangin Da Isra’ila Ta yi A Gaza Shi Ne Farko Da Yafi Jan Hankalin duniya December 8, 2025 Iran Da Azarbaijan Sun Amince Da Ci Gaba Da Tuntubar Juna Domin Warware Matsaloli December 8, 2025 Iran Da Kasashen Afrika Sun Daura Dammarar Karfafa Alakar Kimiyya Tsakaninsu December 8, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Rashin Tsaro: Gwamnatin Tarayya ta gaza — Kwankwaso
Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma dan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce Gwamnatin Tarayya ta gaza wajen shawo kan matsalar tsaro da ke ƙara ta’azzara a faɗin kasar nan, lamarin da ya ce yana barazana ga haɗin kan ƙasa da zaman lafiya.
Kwankwaso, wanda ya taɓa zama Ministan Tsaro, ya bayyana a shafinsa na Facebook cewa yana da “damuwa ta musamman” kan yadda gwamnati ta kasa daƙile ayyukan ’yan ta’adda, ’yan bindiga, rikice-rikicen ƙabilanci da kuma yaɗuwar makamai ba tare da kulawa ba.
Ya ce abin da ya fi nuna gazawar gwamnati shi ne yadda aka bar jihohi su kafa ƙungiyoyin sa-kai ba tare da horo na musamman ba, abin da ya ƙara yaɗuwar kananan makamai a ƙasar.
“Abin takaici, Gwamnatin Tarayya ta gaza. Hakan ya bayyana a yadda ta amince da jihohi su kafa kungiyoyin sa-kai ba tare da horo na kwararru ba,” in ji shi.
An kama tsohon fursuna da bindiga ƙirar AK-47 Dalilin yawaitar juyin mulki a ƙasashen ECOWASKwankwaso ya gargadi cewa wasu ’yan siyasa suna amfani da wannan dama wajen kafa kungiyoyin su na musamman, abin da ya kara jefa kasar cikin hadari.
Ya kuma nuna damuwa kan yadda ake ƙara samun wariyar ƙabilanci da yankuna, inda ya ce ’yan Najeriya musamman daga wani yanki ke fuskantar tsangwama ba bisa ƙa’ida ba, tare da cin zarafi da azabtarwa a sassa daban-daban na kasar.
“Hakan ya kara muni da yadda ake samun cin zarafi, tsangwama da maganganun ƙiyayya a kafafen sada zumunta, wanda ake cusawa da kabilanci da addini. Wannan na barazana ga hadin kan ƙasa,” in ji shi.
Kwankwaso ya buƙaci gwamnati ta ɗauki mataki cikin gaggawa don dakatar da wannan hatsari kafin ya ƙara tsananta.
Ya ce a matsayinsa na tsohon Ministan Tsaro da kuma Shugaban Kwamitin Kula da Yaɗuwar Ƙananan Makamai, yana matuƙar damuwa da yadda makamai ke yaɗuwa cikin sauki a kasar.
Sai dai ya taya Janar Christopher Gwabin Musa murnar nada shi Ministan Tsaro, yana mai fatan zai yi nasara idan aka ba shi goyon bayan siyasa da ya dace.
“Ina da yaƙinin cewa idan aka ba shi goyon bayan siyasa da ya dace, yana da ƙwarewa da gogewa da za su taimaka wajen dawo da tsaro da zaman lafiya a kasar,” in ji Kwankwaso.