Aminiya:
2025-12-12@13:17:21 GMT

Kotun Koli ta soke afuwar da Tinubu ya yi wa Maryam Sanda

Published: 12th, December 2025 GMT

Kotun Kolin Najeriya ta soke afuwar da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya yi wa Maryam Sanda, inda ta ce shugaban ya wuce makadi da rawa ta hanyar yin afuwa ga wacce har yanzu kararta ke gaban kotu.

A hukuncin da aka yanke ranar Juma’a, kotun ta yanke hukunci da rinjayen alƙalai huɗu cikin biyar, inda ta tabbatar da hukuncin kisa da Babban Kotun Abuja ta yanke, kuma Kotun Daukaka Kara ta tabbatar.

‘Haduwata da masu garkuwa da ɗan uwana a dajin Zamfara’ Jam’iyyar PDP ta tabbatar da mutuwar mataimakin Gwamnan Bayelsa

An yanke wa Sanda hukunci ne a shekarar 2020 bisa laifin kashe mijinta, Bilyaminu Bello, a lokacin rikicin cikin gida a gidansu da ke Abuja.

Kotun ta yi watsi da ƙarar da ta shigar, tana mai cewa masu gabatar da ƙara sun tabbatar da laifin kisan kai ba tare da wata shakka ba.

A hukuncin jagoran alkalan, Mai Shari’a Moore Adumein ya ce Kotun Daukaka Kara ta yi daidai wajen tabbatar da hukuncin kotun farko.

Ya ce shiga tsakani na shugaban ƙasa bai dace ba a irin wannan yanayi.

Mai Shari’a Adumein ya ce: “Ba daidai ba ne ga bangaren zartarwa ya yi ƙoƙarin amfani da ikon afuwa kan laifin kisan kai, wanda har yanzu kararsa na gaban kotu.”

A watan Oktoba, an rage hukuncin Maryam zuwa shekaru 12 a kurkuku bayan Shugaba Tinubu ya amince da jerin sunayen wadanda ya yi wa afuwa.

Wannan mataki ya biyo bayan nazari da ya fara da sunaye 175, kafin daga baya a cire wasu saboda irin laifukan da suka aikata.

A lokacin, Mai Ba da Shawara na Shugaban Ƙasa, Bayo Onanuga, ya ce rage hukuncin Sanda “ya dogara ne da tausayi saboda amfanin ’ya’yanta da kuma kyakkyawan halinta,” sannan ya ce ta nuna “nadama.”

Wannan mataki ya janyo suka a fadin Najeriya, ciki har da adawa daga dangin marigayi Bello.

Hukuncin na Kotun Kolin yanzu dai ya soke afuwar ta Shugaban Ƙasa.

Maryam Sanda ta shafe kusan shekaru shida a kurkuku, kuma hukuncin da aka rage zai bar ta da kusan shekaru shida nan gaba. Amma da hukuncin na ranar Juma’a, an dawo da hukuncin kisa da aka yanke mata tun farko.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Maryam Sanda tabbatar da

এছাড়াও পড়ুন:

Kasashen ECOWAS sun rage kudin sufirin jiragan sama a tsakaninsu  

Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) ta amince da wasu sauye-sauye da nufin rage tsadar tafiye-tafiyen jiragen sama a tsakanin kasashe mambobin kungiyar.

A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Laraba, Hukumar ECOWAS ta sanar da cewa shugabannin kasashe da gwamnatoci, a taronsu a Abuja, sun amince da wata manufa ta kawar da harajin sufurin jiragen sama da kuma rage kudin tikitan jirgin sama da kashi 25 cikin 100, wanda zai fara aiki daga ranar 1 ga Janairu, 2026.

Hukumar ta bayyana cewa wannan matakin ya biyo bayan shekaru da dama na koma baya a fannin sufurin jiragen sama a Yammacin Afirka, galibi saboda yawan haraji, wanda ke hana bukatar tafiye-tafiye da kuma raunana jarin da ake zubawa a fannin tafiye tafiye na jiragen sama.

Nazarin da ECOWAS da Tarayyar Afirka, da Kungiyar Jiragen Sama ta Afirka (AFRAA), da Kungiyar Sufurin Jiragen Sama ta Duniya (IATA) suka gudanar sun nuna cewa Yammacin Afirka ya kasance daya daga cikin yankuna mafi tsada don tafiye-tafiyen jiragen sama, inda fasinjoji wani lokacin ke biyan har zuwa caji 66 daban-daban, yayin da kamfanonin jiragen sama ke fuskantar kudade daban-daban.

ECOWAS ta yi gargadin cewa hauhawar farashin jiragen sama na hana tafiye-tafiyen fasinjoji, rage yawan yawon bude ido, kawo cikas ga ciniki, da kuma lalata ajandarta ta ‘yancin zirga-zirga da hadewar yankuna.

A cewar sanarwar, amincewa da Dokar na da nufin magance wadannan kalubalen da kuma daidaita yankin da ka’idojin jiragen sama na duniya.

Kungiyar ta jaddada cewa ya kamata wadannan gyare-gyare su taimaka wajen rage farashin tikiti, kara yawan fasinjoji, karfafa kamfanonin jiragen sama na yankin, bunkasa ayyukan filayen jiragen sama da kuma samar da karin damammaki na tattalin arziki ga al’ummomin da ke karbar bakuncin.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Dakarun IRGC 3 Sun Yi Shahada A wani Harin Ta’addanci A Kudancin Kasar Iran December 11, 2025 Hamas: HKI Tana Ci Gaba Da Keta Bangaren Farko Na Yarjejeniyar Tsagaita Wuta A Gaza December 11, 2025 Iran Ta Yi Tir Da Yanke Tallafin Da MDD Take Bawa Yan Gudun Hijiran Afganistan December 11, 2025 Ansarallah: Dole Ne Kasar Yemen Ta Tsarin Musulunci Na Kaiwa Ga Daukaka December 11, 2025 Shugaban Iran Ya Isa Astana Babban Birnin Kazakhstan December 11, 2025 ECOWAS ta bukaci waware batutuwa na siyasa ta hanyoyin lumana a yammacin Afirka December 11, 2025 Reuters: Amurka na matsa lamba kan kotun ICC don janye bincike kan yakin  Gaza da Afghanistan December 11, 2025 Ghana ta yi Allah wadai da cin mutuncin ‘yan kasarta da ke balaguro a Isra’ila December 11, 2025 Sakamkon Jin Ra’ayi: Yawancin Amurkawa na adawa da kai hari kan Venezuela December 11, 2025 Hamas Ta yi Tir Da Sabbin Matsugunan Yahudawa Da Isra’ila Ke yi A Yankunan Da Ta Mamaye December 10, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Dan sanda ya yi batan dabo a bakin aikinsa a Katsina
  • Ƴan Bindigar Daji: Jihohin Arewa 7 Sun Kaddamar Da Rundunar Fatattakar Su
  • Kotu Ta Yanke Wa Wani Mutum Hukuncin Kisa Bisa Garkuwa Da Kashe Mai Gidansa A Kano
  • Jam’iyyar PDP ta tabbatar da mutuwar mataimakin Gwamnan Bayelsa
  • Kasashen ECOWAS sun rage kudin sufirin jiragan sama a tsakaninsu  
  • Yadda za ku cike neman aikin dan sandan Najeriya na 2025/2026
  • Karamar Hukumar Agwara ta Jinjinawa Gwamnati Bisa Tabbatar da Tsaron Rayuka da Dukiyoyin Jama’a
  • An kama wani mutum a Abuja yana ƙoƙarin kai harsasai ga ’yan bindiga a Zamfara
  • Kasar China Ta Zartar Da Hukuncin Kisa Akan Wani Babban Jami’in Banki