HausaTv:
2025-12-12@15:47:54 GMT

Duniyarmu A Yau: Iran Da Amurka A Yakin Kwanaki 12 Wa Ya Sami Nasara

Published: 12th, December 2025 GMT

Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin Shirin na duniyarmu a yau shiri wanda yake kawo maku labarai masu muhimmanci a makon da ya gabata, wadanda suka shafi siyasa tattalin arziki zamantakewa tsaro da sauransu. Sannan daga karshe idan akwai lokaci mu ji ra’ayin masana dangane da su.

Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu.

///…Madallah, masu sauraro labarimmu na farko a wannan Shirin shi ne, dangane da furucin jakadan Amurka na musamman a kasar Tom Barrack wanda ya bayyana ‘shirin Amurka na 5’ dangane da siyasar Amurka a kan kasar Iran ya wargaje bayan rashin nasarar da ta fuskanta a yankin kwanaki 12 na watan yunin da ya gabata.

Kamfanin dillancin labaran Parstoday na kasar Iran ya nakalto Barrack yana fadar haka a wata hira da ta hada shi da kamafanin dillancin labaran National ta

(UAE) a cikin yan kwanakin da suka gabata. Inda Baraka ya bayyana cewa manufar Amurka a yakin kwanaki 12 da kasar Iran ba ‘kifar da gwamnatin; JMI ba. Amma ganin yadda Shirin ya lalace, Amurka ta kasa cimma manufofinta a kasar Iran yanzun kuma sai wasu sibbin dabaru, saboda ganin mutanen kasar Iran suka taron suka taimakawa gwamnatin kasarsu. Suka kuma hanata faduwa saboda hare-haren da HKI da kuma Amurka suka kaiwa kasar.

Sai dai masana da dama suna ganin wannan ba gaskiya bane, saboda an jima da sanin cewa gwamnatin kasar Amurka da HKI suna Shirin kifar da gwamnatin JMI tun farkon nasarar juyin juya halin musulunci a kasar amma suka kasa yin hakan. .

Banda haka a aikace gwamnatin kasar Amurka ta nuna cewa tana son ganin bayana JMI, kama daga juyin mulkin da ta shiya a farko farkon nasarar juyin juya halin musulunci a shekara 1980. Wannan itace manufa. Sannan manufar kasashen yamma daga ciki har da Amurka na ingiza Sadam Hussain ya farwa kasar Iran da yaki da kuma tallafa masa da makamai, wadanda kuma suka hada har da makaman guba, ba kome bas ai don kifar da JMI tun tana jajiri. Amma sun kasa samun hana har aka kawo karshen yaki bayan shekaru 8.

Sai kuma yake-yaken da Amurka da kawayenta suka cilla a kan yankin Asiya da kudu da kuma Afganistan suna nufin karkaresu da kasar Iran ne. Mamayar Afganistan a shekara 2002 da kuma Iraki a shekara ta 2003 da tura yan ta’adda zuwa cikin kasar Siriya da Iraki a shekara ta 2014. Da sauransu duk tare da Shirin gurgurta kasar Iran ce da kuma kifar da ita idan hakan zai yu. Amma bai yu ba.

Banda haka takunkuman tattalin arziki  kasashen yamma musamman Amurka sun fara aiki a kan kasar Iran tun bayan nasarar juyin juya halin musulunci a shekara 1979 tare da dakatar da sayan danyen mai na JMI. Wadan nan takunkuman sun yi ta karuwa da kuma fadada harzuwa lokacinda suka kai kololuwarsu a zamanin Trump na farko wato 2018.

Kuma a lokacin John Bulton mai bawa shugaban kasar Amurka shawara a kan harkokin tsaro yana fada a wani taro na masu adawa da JMI a birnin Paris na kasar Faransa kan cewa JMI ba zata ga bukukuwan juyin juya halin musulunci nag aba ba. Duk wannan ya zo ya wuce ba tare da samun nasara ba.

A wani bangare kuma gwamnatocin Amurka daya bayan daya, sai da suka yi kokarin tada rikici a cikin kasar Iran, don kawo karshen gwamnatin JMI daga cikin gida. Kama daga rikicin zabe na shekara ta 2009, inda suka yi amfani da yan Takara wadanda basu sami nasar a zaben ba, wato Mir Hussain Musawi da kuma Karubi suka hadda rikicin da ba’a taba yi ba a kasar, da nufin kawo karshen JMI amma a nan ma suka kasa, saboda goyon bayan da mutanen kasar Iran suke bawa tsarin JMI.

Sannan masa Amini ba kurdiya wacce ta yankje jiki ta fada a ofishin jami’a tsaro masu kula dahalaye masu kyau da kuma tabbatar da dokar sanya hijabi. A nan ma ma’aikatan CIA da MOSAD a cikin gida sun yi amfani da wannan damar don ingiza mutane su kawo karshen JMI, amma ma har rikicin ya lafa basu cimma manufarsu ba. Haka ma rikicin kara farashin man fetur a kasar kasashen yamma sun yi kokarin ingiza mutanen kan gwamnatin JMI don kawo karshenta amma suka gaza.

Bayan dukkan wannan gazawar ne Trump da HKI ya shigo kai tsaye da manufar kifar da JMI a ranar 13 ga watan Yulin shekara ta 2025, bayan kashe manya -manyan gwamnadojin sojojin kasar Iran. Kama daga shugaban rundunar IRGC Shahid Manjo Janar Hissain Samali, da babban hafsan hafsoshi kuma babban kwamandan sojojin  kasar Iran Manjo janar Mohammad Bakiri, da babban kwamandon sojojin kare sararin samaniya, da kuma bangaren makamai masu   Amir Ali  Hajizadeh da sauransu.

Suna tsamman idan sun kashe wadanda sun rikita harkokin tsaron JMI kenan kome kuma zai rugurgije, amma a cikin yan sa’o’I aka maye gurbinsu sanna JMI ta fara maida martini mai tsanani a kan HKI, sannan a kan Amurka daga baya a kan sansanin sojojinta take al-udait a kasar Qatar.

Bayan haka ne Trump ya gano cewa, illar da JMI tayi mata da kuma HKI sun bayyana a fili ga kowa a duniya, a sannan ne ya sauya shawara ya kuma bukaci a tsada yakin.

Wadan na dukka, shaidu ne wadanda suka tabbatar da cewa gwamnatocin kasashen yamma musamman Amurka suna son ganin bayan JMI. Don haka maganar Tom Barrack na cewa manufar Amurka a yakin kwanaki 12 ba kifar da gwamnatin JMI ba, ba gaskiya bane. Sai dai sun kasa samun hakan.

Ko a cikin yan makonni da suka gabata Tom Barrack da kansa ya bayyana cewa sun yi kokarin kifar da gwamnatin JMI har sau biyu a kasar Iran sun kasa, sannan a halin yanzu ya zo yace manufarsu ba kifar da gwamnatin ba? Wannan ba haka ne ba. Kuma abinda ya tabbata a tarin rikci tsakanin Amurka da JMI ya nuna cewa Amurka tana da wannan manufar tun farkon nasarar juyin juya halin musulunci a nan Iran.

Masana suna ganin zancen wai Amurka bata nufin sauya gwamnati a kasar, hanya ce ta kaucewa irin koma bayan da Amurka ta fuskanta a wannan fagen. Don Iran ta bayyana cewa tana da karfi.

Masana suna ganin rashin nasarar da Amurka ta yi a yakin da ita da HKI suka kaddamar a kasar Iran ya kara bayyana cewa al-amura da dama sun sauya a duniya, kuma yanking abas ta tsakiya kafin yakin kwanaki 12 ba kuma daya take da yankin a bayan yakin ba.

Banda haka matsayin Amurka a duniya ba kuma matsayin ta a bayan yakin ba. Saboda yadda Amurka take kallon Iran bayan yakin ba kuma haka take kallonta a bayansa ba. Amurka bata tsammanin kasar Iran tana da karfin jurewa farmakon da ita da HKI suka kai mata a cikin watan yunin da ya gabata ba. Su suka fara yaki amma kuma su suka bukaci a tsagaita budewa juna wuta, bayan da suka dandana wutan makamai masu linzami na kasar Iran kuma suka ji zafinsa.

Don haka bayan wannan yakin sun tabbatar da cewa makomar yanking abas ta tsakiya kuma ba a Washington ake fayyace shi ba, sai dai a filin daga a kasar Iran.

 A wani labarin kuma MDD ta bukaci gwamnatin Amurka ta kawo karshen takaita zirga-zirgan jami’an diblomasiyya JMI a birnin NewYork.

Farhan Haq mataimakin kakakin majalisar dinkin duniya ya bayyana cewa gwamnatin Amurka bata da hakkin takaita zirga-zirgan jami’an diblomasiyyar kasar Iran a birnin NewYork, saboda su ma jami’an diblomasiyya ne na MDD kamar ko wace kasa don haka a bisa yarjeniyan da aka da ita tun farkon kafa MDD a birnin News York Amurka bata da hurumin takaita ayyuka ko zirga zirgan Jami’an diblomasiyya na ko wace kasa mamba a matsalisar dinkin duniya.

Haq ya ce: matsayin MDD ita ce duk kasan da take daukar cibiyoyin MDD to dole ne su bar jami’an diblomasiyyar kasashen duniya wadanda suka zo kasar su gudanar da harkokinsu na rayuwa a cikin kasar, kasar Iran ko wata kasa.

Kafin haka dai JMI ta zargi gwamnatin kasar Amurka da takurawa jami’an diblomasiyyar kasarta wadanda suke aiki da MDD a birnin NewYork tare da korafi kan cewa gwamnatin Amurka tana sanya shinge da takunkumai a zirga zirgan jami’an diblomasiyyar kasar a cikin birnin NewYork.

Majiyar gwamnatin kasar Iran ta bayyana cewa gwamnatin kasar Amurka ta na takurawa Jami’an diblomasiyyar kasar Iran a birnin NewYork daga ciki har da hanasu zuwa sayayya na bukatun yau da kullom.

Iran da bukaci MDD ta tabbatar da cewa Gwamnatin Amurka ta bawa dukkan jami’an diblomasiyyar kasar Iran wadanda suka aiki da MDD hakkinsu na zama a birnin NewYork ta kuma tabbatar mata da cewa yin haka ya sabawa yarjeniyar samar da cibiyar MDD a birnin NewYork.

Kafin haka a watan Satumban da ya gabata jakadan kasar Iran a MDD Amir Hussain Iravani ya kai karar Amurka a gaban MDD kan yadda ta takaita zirga-zirgan shugaban kasa Masoud Pezeshkiya da kuma Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi a taron babban zauren MDD karo na 80th.

Labarin ya kara da cewa a bayan ma’aikatar harkokin wajen kasar Amurka ta kafawa Jami’an jakadancin kasar Iran a MDD doka ta fita daga gidajensu don sayayya a cikin unguwar Manhatan na birnin NewYork sai da shaida mata kwanaki 5 kafin su fita.

Labarin ya kara da cewa jami’an diblomasiyyar kasar Iran sukan fita zuwa manya-manyan shaguna ko kasuwanni dake birnin NewYork wadanda suka hada da Costco wadanda suka sayarda kayaki masu yawa da kuma farashi mai sauki.

Jami’an diblomasiyyar kasar Iran dai sukan dauka hankali kafafen yada labaran Amurka a duk lokacinda suka je birnin NewYork saboda abubuwan da suke fada masu jan hankali.

Sannan jami’an tsaron Amurka da kuma wani lokaci har da yan jaridu sukan bisu zuwa kasuwannin don gani da kuma bada rahoton abubuwan da suke saya.

 A bangaren gwamnatin Amurka dai, tana cewa gwamnatin kasar ta sanyawa kasar Iran takunkuman tattalin arziki don haka jami’an diblomasiyyar kasar Iran, saboda wadan nan takunkuman basu da yencin sayan abinda suka ga dama a cikin kasar Amurka, a yayinsa mutanen kasar Iran basa samun wannan damar.

Labarin ya ce ma’aikatar harkokin wajen kasar Amurka tana kula da hatta asusun ajiyar kudin jakadun kasar Iran wadanda suke aiki a MDD.

Labarin ya kara da cewa, tun bayan kama jami’an diblomasiyyar kasar Amurka wanda daliban Jami’o’I a nan Tehran suka yi a shekara 1980 gwamnatin kasar Amurka ta takaita fitar Jami’an diblomasiyyar kasar Iran a birnin NewYork zuwa kilomita 25 kacal daga cibiyar MDD da ke birnin New York.

Labarin ya kara da cewa a wasu lokuta yansanda a birnin NewYork suke kubutar da Jami’an diblomasiyyar kasar Iran daga hannin Iraniyawa yan adawa da gwamnatin JMI idan sun shiga cikin gari don wata bukata ko don sayayya.

Sannan a baya-bayan nan gwamnatin shugaba Donal Trump ta takaita hatta abinda jami’an diblomasiyyar Iran zasu saya a birnin NewYork a lokacinda suka zama a cikinsa.

Tun shekara ta 1980 Iran da Amurka suka katse dangantakar diblomasiyya tsakaninsu, kuma amurka ta takaita fitar jami’an diblomasiyyar JMI a mdd zuwa mile 25 kacal a cikin unguwar manhatan, banda Iran gwamnatin Amurka tana dorawa jami’an diblomasiyyar kasashen Cuba, siriya a lokacin da kuma Korea ta Arewa irin wadannan dokoki.

A shekara ta 2019 gwamnatin Trump ta takaita zirga-zirgan jami’an diblomasiyya kasar Iran tsakanin cibiyar MDD a birnin NewYork, ofishinsu na jakadanci na MDD, da gidajen jakadan Iran a MDD da kuma zuwa tashar jiragen sama na JF kenedi kadai.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Pezeshkian: Duniya Tana Bukatar Amintaccen Madogara, Zaman Lafiya Da Kuma Hadin Kai December 12, 2025 Iran Zata Dauki Bakoncin Taro Dangane Da Kasar Afganistan Da Tsaron Yankin December 12, 2025 Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Amince Ya Ziyarci Beirut December 12, 2025 Islami: Yaki Ba Zai Hana Iran Ci Gaba A Shirinta Na Makamashin Nukliya Ba December 12, 2025 Za A Yi Manyan Zabuka A Kasar Habasha A Watan Yuni Na 2026 December 12, 2025  Turkiya A Shirye Take Ta Aike Da Sojoji Zuwa Yankin Gaza December 12, 2025 Kremlin: Putin Ya Bayyana Wa Shugaba Maduro  Na Venezuela Goyon Bayansa December 12, 2025 Ben Gafir Ya Sha Alwashin Rushe Kabarin Sheikh Izzuddin Alkassam December 12, 2025 Maduro: Amurka Ta Bude Sabon Salon Fashi Akan Doron Ruwa December 12, 2025 Ayatollah Khamenei : Iran na samun ci gaba duk da kalubale da dama December 11, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: nasarar juyin juya halin musulunci a zirga zirgan jami an diblomasiyya zirga zirgan Jami an diblomasiyya jami an diblomasiyyar kasar Iran Jami an diblomasiyyar kasar Iran Labarin ya kara da cewa gwamnatin kasar Amurka gwamnatin Amurka ta kifar da gwamnatin a gwamnatin kasar da gwamnatin JMI yakin kwanaki 12 kasar Amurka ta kasashen yamma cewa gwamnatin kasar Iran ya a cikin kasar wadanda suka bayyana cewa a kasar Iran kasar Iran a kasar Iran A da ya gabata a shekara ta kawo karshen A shekara ta tabbatar da

এছাড়াও পড়ুন:

Yadda APC Da ADC Ke Amfana Da Rikicin Jam’iyyar PDP

PDP wanda ke da gwamnonin 11 bayan zaben 2023, yanzu tana da biyar kawai tare da karin wasu suna nuna suna son barin jam’iyyar.

Yawancin gwamnonin da suka sauya sheka a cikin wannan lokaci sun koma APC, yayin da jam’iyyar Accord ta samu guda daya.

Gwamnonin da suka bar PDP zuwa APC su ne Umoh Eno na Akwa Ibom da Sheriff Oborebwori na Delta da Douye Diri na Bayelsa da Peter Mbah na Jihar inugu. Gwamnan Jihar Taraba, Agbu Kefas, ya dade yana son barin PDP kuma yanzu yana jiran lokaci mai ya yi ne ya shiga APC.

Akwai fargaba cewa gwamnonin Caleb Muftwang na Jihar Filato da gwamnan Zamfara, Dauda Lawal ma na iya canza sheka. Gwamnonin PDP kadai da suka bayyana a fili cewa za su tsaya cikin jam’iyyar don gyara al’amuran gida su ne gwamnan Jihar Bauchi, Bala Muhammad da abokin aikinsa na Jihar Oyo, Seyi Makinde, yayin da Ahmadu Umaru Fintiri na Adamawa ya bayyana tamkar yana son sauya sheka.

Rikicin PDP y afara kuno kai ne tun bayan zabukan 2023, baya ga gwamnoni, jam’iyyar ta rasa karin ‘yan majalisa, ciki har da manyan mambobin majalisar tarayya zuwa APC.

Daga cikin ‘yan majalisar tarayya da suka bar tsohuwarsu zuwa APC akwai Sanata Agom Jarigbe daga Jihar Kuros Ribas da Sunday Marshal Katung daga Kaduna.

Tun daga shekarar 2023 har zuwa yanzu, jam’iyyun adawa a majalisar wakilai sun rasa akalla mambobi 66 zuwa jam’iyyar APC mai mulki.

Babbar jam’iyyar adawa ta PDP wadda ta rasa ‘yan majalisu 44, sai LP 14, NNPP 6, ADC 1 da YPP 1.

A lokacin da aka kaddamar da majalisar a watan Yuni 2023, tsarin majalisar wakilai ya kasance APC tana da kujeru 178, PDP 115, LP 35, NNPP 19, APGA 5, SDP 2, YPP 2 da ADC 2.

Bayan guguwar sauya sheka, yawan ‘yan majalisar yanzu sun kasance kamar haka: APC 246, PDP 71, LP 21, NNPP 13, APGA 5, SDP 2, ADC 1 da YPP 1.

A ranar Juma’a da ta gabata, mambobi 16 na majalisar dokokin Jihar Ribas karkashin jagorancin shugaban majalisan, Martin Amaewhule, sun sauya sheka daga PDP zuwa APC.

Lokacin da aka kaddamar da majalisar dokoki ta kasa ta 10 a ranar 13 ga Yunin 2023, jam’iyyar APC ta rike kujeru 59 a majalisar dattawa.

Amma jam’iyyar ta kara tumbatsa zuwa samu sanatoci 76, ta wuce kashi biyu bisa uku na samun rinjaye, bayan samun sauya sheka da ‘yan majalisar dattawan suka shiga cikinta.

Lokacin da aka amince da ADC a matsayin jam’iyyar hadaka ta tsofaffin shugabannin PDP, jam’iyyar ta sami sabon rayuwa tare da shigowar manyan mambobin PDP da suka hada da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da tsohon shugaban majalisar dattawa, Dabid Mark da tsohon gwamnan Jihar Osun, Rauf Aregbesola da wasu.

Yawan wadanda ke barin PDP suna shiga APC ne, yayin da kadan daga ciki suke shiga ADC.

Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir Elrufai ya sauya sheka daga APC zuwa SDP, sannan daga baya ya shiga ADC.

PDP ita ce kawai babbar jam’iyya da ba ta amfana daga guguwar sauyin sheka ba, amma tana ci gaba da rasa babban adadin mambobinta.

Wani masanin siyasa kuma farfesa a fannin kimiyyar siyasa, Gbade Ojo, wanda ya yi magana da wakilinmu kan wannan batu, ya lura cewa rushewar jam’iyyun adawa yana da babban tasiri wajen yawan tserewar mambobi, yana mai cewa hakan ya kara rage gwarin gwiwar al’ummar Nijeriya.

“Idan ka kalli majalisa, APC yanzu tana da gagarumi rinjaye a duka majalisar wakilai da majalisar dattawa. Ayyukan sa ido nasu suna da rauni sosai saboda shugaban kasa ya nada jami’an da su ne za su je su gudanar da ayyukan sa ido a kansu. Amma yawancinsu yanzu suna cikin jam’iyyar gwamnati,” in ji shi.

Sau da dama PDP ta yi kokari dawo da martabar jam’iyyar. Ta gudanar da babban taro a matakin gundumomi da karamar hukumomi da jihohi da dama kuma kasa baki daya, inda mambobi suka zabi sabon shugaban jam’iyyar na kasa.

Amma lamarin ya ci tura, inda magoya bayan ministan Abuja, Nyesom Wike suka kalubalantar babban taron.

Wasu na cewa ko da an gudanar da babban taron zaben, jam’iyyar ta kasa haifar da irin amincewar da zai sa mambobinta su ci gaba da kasancewa wuri guda.

Duk da yake akwai alamun da ke cewa ko wadanda suka saura na iya barin jam’iyyar a kowane lokaci.

Masana na cewa ci gaban rikicin a jam’iyyar da shari’o’i da dama na iya sanya ‘yan takararta a 2027 cikin hadari ta fuskar doka, musamman gwamnonin da ke neman wa’adi na biyu su nemi wasu jam’iyyar.

A hankali, ADC tana samun karuwa a matsayin babban jam’iyyar adawa a kasar, tana matsar da PDP zuwa baya, wacce ta rike wannan matsayi tun bayan ta fadi a zaben shugaban kasa a 2015, zuwa matsayi na biyu.

A kwanan nan, jam’iyyar ta ce tana shirin karbar sama da mambobin majalisar ta 10 guda 100 kafin zaben shekarar 2027.

A halin yanzu APC na da yawancin ‘yan majalisa a duka majalisun dokoki kasar nan tare da zargin cewa wasu na shirin shiga jam’iyyar.

Akwai rahotannin da ke cewa a jihohi kamar Benuwai, Kano, Adamawa da Yobe cewa ADC ta kafu kuma za ta bunkasa c

ikin ‘yan watanni kadan masu zuwa.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Farashin Kayan Abinci Na Sauka Yayin Da Bikin Kirsimeti Da Sabuwar Shekara Ke Matsowa December 12, 2025 Manyan Labarai Ƴan Bindigar Daji: Jihohin Arewa 7 Sun Kaddamar Da Rundunar Fatattakar Su December 12, 2025 Manyan Labarai Gwamnonin Arewa Sun Yi Rawar Gani A Kafa Gidauniyar Fuskantar Matsalar Tsaro December 12, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Dan sanda ya yi batan dabo a bakin aikinsa a Katsina
  • Yadda APC Da ADC Ke Amfana Da Rikicin Jam’iyyar PDP
  • Yadda Bunkasar Tattalin Arzikin Kasar Sin Ke Samar Da Karin Damammaki Ga Kasashe Masu Tasowa
  • Bankin Duniya Ya Daga Hasashen Ci Gaban Tattalin Arzikin Sin Na 2025 Da Maki Kaso 0.4
  • Gwamnatin Jigawa Ta Kara Samar da Shirye-shiryen Inganta Rayuwar Masu Buƙata ta Musamman
  • Shugaban Iran Ya Isa Astana Babban Birnin Kazakhstan
  • Amurka ta matsa lamba a kan kotun ICC don janye bincike kan yakin  Gaza da Afghanistan: Reuters
  • Real Madrid  za ta ɓarje gumi da Manchester City a Santiago
  • Nasarar Da Iran Ta Samu A Yakin Kwanaki 12 Kan HKI Yana Jawo Hankalin Kasashen Duniya