Yadda za ku cike neman aikin dan sandan Najeriya na 2025/2026
Published: 11th, December 2025 GMT
Hukumar Kula da Ayyukan ’Yan Sanda ta Najeriya, tare da haɗin gwiwar Rundunar ’Yan Sandan Kasar sun buɗe shafin neman aiki domin ɗaukar sabbin ’yan sanda na constables da kuma ma’aikata masu kwarewa ta musamman.
A kwanan nan Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin ɗaukar sabbin ’yan sanda 50,000 a fadin ƙasar domin ƙarfafa tsaron cikin gida da kuma ƙara yawan jami’an da za su taimaka wajen yaƙi da laifuka da rashin tsaro.
Za a buɗe shafin neman aiki daga 15 ga watan Disamba, 2025 zuwa 25 ga Janairu, 2026.
Ga yadda yadda za ku cike neman aikin daki-daki:
Mataki na 1: Duba cancantarka Dole ne ka kasance ɗan Najeriya ta hanyar haihuwa. Ka kasance lafiyayye a jiki da hankali. Ba ka da matsalar kuɗi ko bashin da ka gaza biya. Kana da kyakkyawar dabi’a hali, babu tarihin aikata laifi. Iyakar shekaru: 18–25 ga sauran ’yan sanda. Har zuwa 28 ga masu kwarewa ta musamman. Mata kada su kasance masu juna biyu ba a lokacin bayar da horo. Ka cika sharuddan jiki: Maza: tsawo 1.67m, fadin ƙirji 86cm. Mata: tsawo 1.64m. Mataki na 2: Tabbatar da ƙwarewarka Sauran ’yan sanda: Mafi ƙaranci, samun darussa biyar a jarabawar SSCE/NECO, ciki har da Turanci da Lissafi. Masu kwarewa: Mafi ƙaranci, darussa huɗu, ƙwarewar sana’a (shekaru 3 zuwa sama), da takardar amincewar aiki. Mataki na 3: Shirya takardunkaZa ka buƙaci kwafin takardu (soft copy) na:
Takardar kammala makarantar firamare. Sakamakon SSCE/NECO. Takardar haihuwa. Shaidar zama dan asalin karamar hukuma/jiha.Ga maus kwarewa ta musamman kuma:
Takardar shaidar aiki. Lasisin tuƙi (idan aikin direba ne). Mataki na 4: Yi rajista ta yanar gizo Ziyarci shafin: https://npfapplication.psc.gov.ng Ka tabbatar kana da: Lambar Shaida Ƙasa (NIN). Adireshin imel mai aiki. Lambar waya don sadarwa. Loda dukkan takardun da ake buƙata. Mataki na 5: Sanin rukuni Sauran ’yan sanda ’Yan Sandan Constables. Masu kwarewa ta musamman Harkar lafiya: Jami’an lafiya. Sufuri: Direbobi, Kanikawa, masu gyaran mota, masu kai sako. EOD‑CBRN: Masu binciken kwakwaf, sauran ’yan sanda. K9 Section: Masu kula da karnuka. Mounted Troop: Masu hawan doki. Marine: Direbobi, injiniyoyi, kanikawan jirgin ruwa. Artisans: Masu aikin lantarki, masu gyaran famfo, masu walda, masu gyaran AC. Tailoring: Masu dinki. Sadarwa: Kwararru da masu sarrafa na’ura. Band Section: Masu kula da kayan kiɗa. Mataki na 6: Shirin fara gwaje‑gwaje Gwajin jiki da na lafiya. Gwajin basira. Binciken bayanai. Mataki na 7: Bin ƙa’ida Neman aikin kyauta ne, kuma bisa cancanta. Duk wani cin hanci ko ƙoƙarin bayar da kuɗi zai jawo hukunci mai tsanani Mataki na 8: Karin bayani A ziyarci shafukan sada zumunta na Hukumar Aikin ’Yan Sanda ko shafin tambayoyi. Ko a kira: 09060483893, 09135006008, 09135006009.উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: dibar yan sanda kwarewa ta musamman masu kwarewa Masu kwarewa
এছাড়াও পড়ুন:
Cin hanci da rashawa sun yi ƙatutu a Najeriya — ICPC
Hukumar ICPC ta ce da ana aiwatar da dokokin yaƙi da cin hanci da rashawa yadda ya kamata, da kusan kashi 80 na ’yan Najeriya na ɗaure a gidan yari.
Kwamishinan ICPC na Jihar Kaduna, Sakaba Ishaku ne, ya bayyana haka a wani taron horaswa kan yadda ake kula da amana a ƙananan hukumomi.
Kisan Zariya: Na bar Buhari da Allah — Sheikh El-Zakzaky Najeriya za ta buga wasan sada zumunta da Masar kafin fara gasar AFCON ta 2025Ya ce cin hanci ya yi tasiri sosai a rayuwar ’yan Najeriya, kuma yana haifar da talauci, rikice-rikice, da jinkirta ci gaban ƙasa.
Ya ƙara da cewa yawancin dukiyar da wasu ke taƙama da ita a Najeriya ma da alaƙa da aikata rashin gaskiya, kuma mutane da yawa ba sa son jin batun yaƙi da cin hanci saboda suna jin daɗin aikata shi.
Ishaku, ya soki shugabannin ƙananan hukumomi da ke barin kujerarsu ba tare da sun aiwatar da wani gagarumin aiki ba.
Ya kuma nemi a tsaurara hukunci ga masu satar dukiyar gwamnati, inda ya ce duk wanda ya saci dukiyar jama’a bai kamata a masa hukunci mai sauƙi ba.
Kwamishinan Harkokin Ƙananan Hukumomi na Kaduna, Sadiq Mamman Legas, ya goyi bayan bayanan ICPC.
Ya ce gwamnati ta gyara na’urorin wutar lantarki a wasu yankuna, amma mazauna wajen suka lalata, tare da suka sace wasu.
Ya ce ba za a samu ci gaba ba idan mutane suna lalata dukiyar gwamnati.
Dukkanin jami’an sun yi kira da a ƙara ƙarfafa doka, a kula da ayyukan gwamnati sosai, kuma a wayar da kan jama’a domin rage cin hanci da kare kayayyakin gwamnati.