Aminiya:
2025-12-12@16:23:09 GMT

Mangal ya bayar da tallafin N257m don yi wa marasa galihu aikin ido kyauta a Katsina

Published: 12th, December 2025 GMT

Fitaccen attajirin nan Alhaji Dahiru Mangal, ya ɗauki nauyin yi wa marasa galihu a Jihar Katsina aikin ido kyauta, inda ɗaruruwan mutane ke samun kulawar likitoci ba tare da biyan ko sisi ba.

A yayin da wakilin Aminiya, ya ziyarci Asibitin Ido da ke birnin Katsina, marasa lafiya da dama da suka ci gajiyar aikin sun bayyana farin cikinsu da godiya kan tallafin na sama da Naira miliyan 257.

Matatar man Dangote ta rage farashin fetur zuwa N699 Kotun Koli ta soke afuwar da Tinubu ya yi wa Maryam Sanda

Malama Indo, wadda ta fito daga garin Dankama da ke Ƙaramar Hukumar Kaita, ta bayyana farin cikinta da samun tallafin.

Ta ce: “Na kwashe kusan shekara guda ina fama da ciwon ido. Da zarar yamma ta fara yi, sai na kasa fitowa saboda duhu. Amma yanzu ina gani lafiya lau, babu wata matsala.

“Mun kwana uku a nan asibiti, ba mu rasa komai ba, har abinci ake ba mu. Wallahi ba zan iya cewa na kashe komai ba sai kuɗin mota kawai.

“Muna roƙon Allah Ya saka wa wanda ya ɗauki nauyin wannan aiki da alheri,” in ji ta.

Shi ma wani dattijo mai suna Malam Khalha Jibiya, ya bayyana jin daɗinsa game da aikin.

Ya ce an masa aiki, an kuma ba shi tabarau, sannan yanzu yana gani ba tare da wata matsala ba.

“Idan waɗanda Allah Ya hore musu dukiya za su riƙa taimaka wa gajiyayyu kamar haka, da matsalolinmu da dama sun ragu.

“Muna addu’a Allah Ya saka wa mai ɗaukar nauyin wannan shiri da alheri.” inji Malam Khalha.

Dukkanin marasa lafiyan da Aminiya ta zanta da su, sun yi godiya, musamman ganin cewa aikin ido da magungunan da ake ba su kyauta ne baki ɗaya.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Ɗaukar Nauyi marasa galihu

এছাড়াও পড়ুন:

Annabi SAW Ya Zarce Duk Sauran Annabawa Yawan Mu’uzijoji

Wata rana, Abu Huraira (RA) yunwa ta kama shi matuka, har yazu wurin mimbarin Annabi SAW da ke cikin masallacin Annabi, sai ya fadi a wurin, duk wadanda suka zo wurin suka ganshi, sai suce Allah Sarki, wane ba shi da lafiya har sai da Annabi ya zo ya ganshi, sai yace masa, Abu Hurairah kana jin yunwa ko? Sai ya amsa da eh. Take Annabi SAW ya ce masa, biyo ni zuwa daki na. Annabi yasa aka kawo masa nono a dan koko kamar yadda aka saba, Abu Hurairah yana jira a ce masa ya sha, sai Annabi SAW ya ce masa ya kira ‘yan uwansa Ahlul suffati, kuma jama’a ne masu yawa, da isowarsu, Annabi SAW ya sa wa Nonon albarka, suka fara sha, tawaga bayan tawaga, har sai da kowa ya sha ma’ishi, babu wanda ya yi saura sai Annabi SAW da Abu Huraira, sai ya ce, Abu Huraira fara sha iya shanka, sannan ya ci gaba da ce masa, kara sha, kara sha, har sai da Abu Huraira ya ce, na rantse da wanda ya aiko ka, ya ishe ni, sannan Annabi SAW ya karba ya yi Bismillah ya sha sannan ya kare.

Don haka, wata rana, Annabi SAW ya ta shi ya yi kuka yana tuna masoyansa a gaban Sahabbansa, sai suka ce, ya Rasulullah ba mu ne masoyanka ba, sai ya ce, A’a ku Abokaina ne, wadan can sun yi imani da ni, ba suga mu’uzija ko daya ba, ku kuma kun yi imani da ganin irin wannan abu: Nono dan kadan, a shayar da tawaga da shi, ruwa ya fito ta tsakanin ‘yan yatsu, halittarsa mai kyau, sadaukanta, jarumta, Ilimi, fasaha, cika alkawari, Amana, kyauta, ga su nan da yawa ba iyaka.

A yakin Kandak, lokacin da Sayyadina Aliyu ya kashe Amru bin Waddu (mai karfin kasar Larabawa gaba daya a zamanin) bayan ya yi wa Sayyadina Ali rawani, ya ba shi takobin shi sannan ya ce “rabbi la tazarni farda wa anta kairul warisin”, bayan ya kashe shi sai Annabi ya tambaye shi, ya kake jin kanka a yanzu? Sai ya ce, ina jin da za a tattara min mutanen Madina, zan iya kashe su gaba daya! Sai Annabi SAW ya ce masa, to shirya, akwai wani Saurayi sadauki zai fito daga wannan dajin, za ku yi yaki. Bayan fitowar saurayi sadauki, sai ya tambaya, kai ne Ali? wurinka aka turo ni, yau daya ne zai tsira tsakanin ni da kai, bayan gwabzawa, saurayi ya yi wata wujijjiga da Sayyadina Ali, nan take ya ga ne cewa, wannan saurayi ba kowa ba ne face SAW. Don babu wani da ya isa ya yi wa Sayyadina Ali irin haka duk duniya sai Annabi SAW, sai ya fahimci cewa, akwai sama da shi. Fakrurrazi mai Hadisi ne ya fitar da wannan Hadisin.

15 – Annabi Adam da duk ‘ya’yansa Annabawa suna karkashin tutar Annabi Muhammad SAW a ranar Alkiyama: wannan ya tabbatar cewa, duka Annabawa suna kasa da shi. Ya zo cikin Hadisi Annabi SAW yana cewa, “ana sayyadi waladi Adam wala fakr – ni ne shugaban ‘ya’yan Annabi Adam ba alfahari ba”, sabida Manzon Allah SAW, zuciyarsa tana da fuska biyu – yadda yake kallon hadarar Allah da yadda ya ke kallon bayin Allah. Don haka, Annabi SAW in yana gaban Ubangiji, sunan shi “Abdu”, amma in ya taho wurinmu sauran bayi, shugabanmu ne. Annabi Yahya a wurinmu ma, Ubangiji kiranshi ya yi da cewa, “Sayyidan wa hasuran wa nabiyyan minassalihin – Shugaba, katangagge kuma Annabi daga cikin managarta bayi”

A wani wuri kuma, Annabi SAW ya ce, babu wanda zai shiga Aljannah daga Annabawa kafinsa SAW, kuma babu wata al’umma da za ta shiga daga al’ummomin da suka gabata kafin al’ummarsa SAW! Duka wannan saboda albarkar Annabi SAW.

An ruwaito hadisi daga Anas bin Malik yana cewa, manzon Allah SAW ya ce, “ni ne farkon halitta wanda zai fara fita daga kabari idan an tashi al’umma a ranar Alkiyama, ni ne wanda zan wakilce su wurin yin bayani a gaban Ubangiji don kowa ya tsira, ni ne zan yi musu bushara idan gwiwoyinsu sun sage sun ga kamar ba za su tsira ba, tutar godiya tana hannuna, ni ne mafi girman dan Adam a wurin Ubangijina, kuma ba alfahari nake ba, cewa aka yi in fada, “wa amma bini’imati rabbika fahaddis – ka bayyana ni’imomin Ubangijinka a gareka”.

Wannan magana da Annabi ya fada wa Sahabbansa, ita muke kira da Maulidi. A tara Jama’a a fada musu girma da darajar fiyayyen halitta, Annabi Muhammad SAW.

An karbo Hadisi daga Abdullahi bin Abbas yana cewa, wasu daga cikin sahabban Annabi SAW sun taru suna hirar karatu, sai wasu suka ce, ” ittakazallahu Ibrahima kalila – mamakin yadda Allah ya riki Annabi Ibrahim Badadi (Kalila)”, wasu kuma suka ce, “wannan ai ba abin mamaki ba ne, kamar yadda Ubangiji ya yi hira da Annabi Musa, – wakallamallahu Musa taklima,” wasu kuma suka ce, ina kuka bar Annabi Isa, “Kalimatullahi wa ruhuhu – Kalmar Allah kuma ruhinsa yadda ya dace da shi”, wasu kuma Adamu “isdafahu – Allah ya zabe shi”, kuma duk babu wanda ya san Annabi SAW yana jinsu.

Da Annabi SAW, ya fahimci abun na su ya ki kare wa kuma suna shirin fadawa hadari, sai ya fito ya dakatar da su, ya ce musu, na ji duk batutuwanku da hujjojinku, kuma duk abinda kuka fada haka ne! Kun ce, “Annabi Ibrahim Kalilullah, Musa kalimullahi wa najiyyahu, Adamu isdafahu, duka haka ya ke, amma duk ku saurara kuji! Ni Habibullahi ne ba alfahari ba, saboda mukamin na shi ne! Ni nake rike da tutar godiya, ni ne wanda zai yi ceto, ni ne farkon wanda za a karbi cetonsa a ranar Alkiyama, ba alfahari ba! Ni zan fara kwankwasa kofar Aljannah don a bude, sai a bude in shiga, tare da ni akwai Mu’uminai fukara’u.

Don haka, ya tabbata a hadisi, ranar Alkiyama, ana neman ceto, kowa ya dimauce, sai a tafi wurin Annabi Adam, ya ce, ba ni ba, sai a tafi wurin Annabi Musa, shi ma ya ce ba ni ba, a tafi wurin Annabi Isa, shi ma haka, a tafi wurin Annabi Ibrahim shi ma haka, amma dai a tafi wurin Rasulullah SAW.

A ranar Alkiyama, bayan Annabi SAW ya bude kofar shiga Aljannah, Shahidai za su taho zuwa shiga Aljannah, sai a tambayesu, waye ya kira ku? Sai suce Malamai suka gaya mana cewa, mune farko, sai a ce musu, to kubari Malamai su fara shiga; Malamai da jin haka, sai su ta so za su shiga, sai a tambayesu, ku su waye? Sai su ce, mu ne Malamai, to ya aka yi kowa bai zama Malami ba sai ku kadai, sai suce, saboda duk sun tafi wurin neman abinci muka muna wurin koyon ilimi, to ku ba ku cin abinci? Muna ci, wasu ne suka dauki nauyin cin abincinmu, to ku bari masu ciyarwa su fara shiga. Don haka, sai mai ciyarwa ya fara shiga Aljannah, sannan Malami sannan Shahidi.

Annabi SAW, ya kara ce musu, kuma ni ne mafificin mutanen farko da na karshe, ba alfahari ba!

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Dausayin Musulunci Allah Ya Bai Wa Annabi (SAW) Mu’ujizozi Fiye Da 2,000 A Alƙur’ani   December 5, 2025 Dausayin Musulunci Allah Ya Bai Wa Annabi (SAW) Mu’ujizozi Fiye Da 2,000 A Alƙur’ani November 28, 2025 Dausayin Musulunci Allah Ya Tsarkake Iyalan Annabi (SAW) Daga Kazanta November 21, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Dan sanda ya yi batan dabo a bakin aikinsa a Katsina
  • Annabi SAW Ya Zarce Duk Sauran Annabawa Yawan Mu’uzijoji
  • Shugabannin Sin Sun Yi Taron Koli Na Tattauna Aikin Raya Tattalin Arziki Don Tsara Abubuwan Da Za A Aiwatar A 2026
  • BUA ya tallafa wa ɗaliban Sakkwato 200 da miliyan 40
  • Katsina Ta Amince Da Bayar Da Alawus Na Naira 30,000 Duk Wata Ga Malaman Karkara
  • NAFDAC Ta Ƙona Kayayyaki Marasa Inganci Na Naira Biliyan 5 A Nasarawa
  • Iran Ta Yi Tir Da Yanke Tallafin Da MDD Take Bawa Yan Gudun Hijiran Afganistan
  • Kisan Zariya: Na bar Buhari da Allah — Sheikh El-Zakzaky
  • Kamfanin Mangal ya kori direba kan dauko yara 21 da aka kama a Kogi