Kin Amincewar Japan Game Da Muggan Laifukan Yakin Da Ta Aikata Ya Dakatar Da Bukatar Sin Ga Hukumar UNESCO
Published: 21st, September 2025 GMT
A ranar Alhamis 18 ga watan nan, aka kaddamar da fara nuna fim din nan mai taken “Evil Unbound” a dukkanin sassan duniya, fim din da ya ba da labarin yadda a yayin yakin kin mamayar dakarun Japan, wata rundunar dakarun sojin kasar Japan ta aiwatar da wani shirin sirri, na gwaje-gwajen kimiyya ta makamai dake iya illata lafiyar bil’adama, a wani boyayyen wuri dake lardin Heilongjiang na arewa maso gabashin kasar Sin.
Duk da cewa akwai shaidu na hakika, da suka tabbatar da aukuwar muggan laifukan da rundunar ta 731 ta tafka, bukatar kasar Sin ta shigar da wannan lamari cikin kundin killace abubuwan tarihi na UNESCO ya gamu da tsaiko, har na tsawon sama da shekaru shida. Kazalika, bukatar da Sin ta gabatar ga hukumar, dangane da shigar da batun “matan da aka tilasta musu zama karuwan sojoji” cikin kundin, ita ma ta gamu da irin wannan cikas.
Sakamakon bincike na bidiyo da aka fitar a Asabar din nan, ta wani shafin sada zumunta mai lakabin “Yuyuan Tantian”, mallakin kafar CMG ta kasar Sin, ya nuna cewa, akwai sa hannun gwamnatin Japan, da wasu masu ra’ayin rikau na kasar, wajen dakile cimma wannan bukata ta Sin.
Kafin hakan, a shekarar 2021 ma, hukumar UNESCO ta yiwa wasu dokokinta kwaskwarima, ta yadda duk wata memba a hukumar ke da damar dakatar da bukatar shigar da wani abu cikin kundin na UNESCO, ta hanyar gabatar da korafi. Masu sukar wannan sauyi dai na ganin hakan zai baiwa kasashen da suka aikata wata ta’asa a tarihi, dama ta hana shigar da laifin da suka aikatawa wasu sassa cikin kundin tarihin mai kiyaye gaskiya na hukumar ta UNESCO. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
SEMA Jigawa Da NEMA Da UNICEF Sun Bada Horo Akan Agajin Gaggawa A Auyo
Hukumar ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Jigawa, SEMA, tare da hadin gwiwar Hukumar ba da Agajin Gaggawa ta Kasa NEMA, da Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, sun shirya gwajin yadda za a gidanar ayyukan ceton ambaliyar ruwa a karamar hukumar Auyo.
Gwajin wanda ya tattaro masu ruwa da tsaki daga hukumomi daban-daban, an yi shi ne da nufin baiwa mahalarta taron kwarewa da ilimin da suka dace don ceto da kuma mayar da martani ga al’ummomin da ambaliyar ruwa ta shafa.
Aikin ya ƙunshi mahimman wurare kamar dabarun bincike da ceto, taimakon farko, da hanyoyin ƙaura.
Wannan yunƙurin ya nuna himmar SEMA, NEMA, da UNICEF don haɓaka ƙarfin masu ruwa da tsaki na cikin gida wajen rage haɗarin bala’i da sarrafa su.
A nasa jawabin, Kodinetan kula da sashen ayukkan ceto na kungiyar bada agaji ta Red Cross, Ali Yohanna ya yabawa SEMA, NEMA, UNICEF da sarakunan gargajiya bisa halartar taron da zai taimaka wajen ceto mutanen da ke bukatar kulawa cikin gaggawa.
KARSHE/USMAN MZ