Aminiya:
2025-12-10@06:04:51 GMT

Majalisar Dattawa ta amince Tinubu ya tura sojojin Najeriya zuwa Jamhuriyar Benin

Published: 10th, December 2025 GMT

Majalisar Dattawa a ranar Talata ta amince da bukatar Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta tura sojojin Najeriya zuwa Jamhuriyar Benin domin tabbatar da dimokuradiyya a kasar.

Majalisar ta kuma ce tana goyon bayan matakin da shugaban ya ɗauka kwanaki kafin haka domin hana yunƙurin kifar da tsarin dimokuraɗiyya a makwabciyar kasar.

Gwamnan Jihar Ribas ya sauya sheka zuwa APC Juyin Mulki: ECOWAS ta ayyana dokar ta-baci a kasashenta

Bukatar dai na kunshe ne a cikin wata wasiƙa da Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio, ya karanta a zauren majalisa yayin zamanta.

Tinubu ya umarci tura sojojin makon da ya gabata domin dakile yunƙurin karɓar mulki ba bisa ka’ida ba a Jamhuriyar Benin da kuma kaucewa rikicewar tsaro a yankin yammacin Afirka.

Sai dai Tinubu bai nemi amincewar majalisa ba kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.

Bayan karanta wasiƙar, majalisar ta koma zaman kwamiti domin tantance bukatar. A yayin zaman, ’yan majalisa sun tattauna kan tasirin tsaro, jin‑ƙai da diflomasiyya da ke tattare da wannan mataki.

Babbar damuwar a cewarsu ta haɗa da yiwuwar kwararar ’yan gudun hijira zuwa Najeriya, tsaron iyaka da kuma tasirin matakin ga zaman lafiya da tsaro a yankin.

Bayan doguwar muhawara, majalisar ta koma zama a zaurenta, inda ta kada kuri’ar amincewa da matakin shugaban ƙasa cikin rinjaye.

Shugaban Majalisar, Akpabio, ya gabatar da rahoton kwamitin domin tabbatarwa, inda ’yan majalisa suka amince ba tare da wata adawa ba kafin su amince da tura sojojin ta hanyar kada kuri’ar murya karo na biyu.

A jawabin sa, Akpabio ya yabawa Shugaba Tinubu bisa ɗaukar matakan da suka tabbatar da zaman lafiya a yankin da kuma bin ka’idojin kundin tsarin mulki ta hanyar neman amincewar majalisa, ko da bayan tura sojojin cikin gaggawa.

“Wannan mataki ne da ya zama dole. Shugaban Ƙasa ya yi aiki ne domin kare tsaron ƙasa da kuma kare dimokuraɗiyya a yammacin Afirka. Barazana ga kasa ɗaya barazana ce ga kowa,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa za a isar da kudurin majalisar ga Shugaban Ƙasa nan take.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Jamhuriyar Benin Tura sojoji tura sojojin

এছাড়াও পড়ুন:

Sojoji sun yi juyin mulki a Jamhuriyar Benin

Sojoji a kasar Jamhuriyar Benin sun kifar da gwamnati a wani juyin mulki da suka sanar a ranar Lahadi.

Sojojin sun bayyana ne a gidan talabijin na kasar inda suka sanar da tsige Shugaban Kasa Patrice Talon da kuma rushe duk hukumomin kasar.

Dakarun, karkashin jagorancin Laftanar Kanar Pascal Tigiri, sun rufe iyakokin kasar da rushe jam’iyyun siyasa.

Zuwa lokacin kammala wannan labarin babu labarin halin da Shugaba Talon wanda ke kan karagar mulkin tun a 2016 yake ciki.

Amma ministan harkokin kasar, Olusegun Ajadi Bakari, ya ce an samu yunkurin kifar da gwamnati, amma ana neman shawo kan lamarin.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An dakatar da Shugaban Karamar Hukumar Lafia
  • Najeriya: Jirgin Sojojin Kasar Yana Kan Hanyarsa Ta Zuwa Portugal, Amma Ta Sauka A Burkina Faso
  • Nigeria Ta Aike Da Jiragen Yaki Zuwa Kasar Benin Domin Dakile Yunkurin Juyin Mulki
  • Kasashen Iran Da Azarbaijan Sun Amince Da Ci Gaba Da Tuntubar Juna Domin Warware Duk Wani Rikici
  • Ecowas Ta Tura Sojoji Zuwa Jamhuriyar Benin Don Dakile Juyin Mulki
  • Matsalar Tsaro: Tinubu Ya Yi Ganawar Sirri da Gwamnonin Jihohi Shidda
  • Juyin mulki: An kama sojojin da suka yi yunƙurin kwace mulki a Benin
  • Tawagar Majalisar Amurka ta iso Nijeriya Don Bincika Zargin Tauye Haƙƙin Addini
  • Sojoji sun yi juyin mulki a Jamhuriyar Benin