Rashin Tsaro: Gwamnatin Tarayya ta gaza — Kwankwaso
Published: 8th, December 2025 GMT
Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma dan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce Gwamnatin Tarayya ta gaza wajen shawo kan matsalar tsaro da ke ƙara ta’azzara a faɗin kasar nan, lamarin da ya ce yana barazana ga haɗin kan ƙasa da zaman lafiya.
Kwankwaso, wanda ya taɓa zama Ministan Tsaro, ya bayyana a shafinsa na Facebook cewa yana da “damuwa ta musamman” kan yadda gwamnati ta kasa daƙile ayyukan ’yan ta’adda, ’yan bindiga, rikice-rikicen ƙabilanci da kuma yaɗuwar makamai ba tare da kulawa ba.
Ya ce abin da ya fi nuna gazawar gwamnati shi ne yadda aka bar jihohi su kafa ƙungiyoyin sa-kai ba tare da horo na musamman ba, abin da ya ƙara yaɗuwar kananan makamai a ƙasar.
“Abin takaici, Gwamnatin Tarayya ta gaza. Hakan ya bayyana a yadda ta amince da jihohi su kafa kungiyoyin sa-kai ba tare da horo na kwararru ba,” in ji shi.
An kama tsohon fursuna da bindiga ƙirar AK-47 Dalilin yawaitar juyin mulki a ƙasashen ECOWASKwankwaso ya gargadi cewa wasu ’yan siyasa suna amfani da wannan dama wajen kafa kungiyoyin su na musamman, abin da ya kara jefa kasar cikin hadari.
Ya kuma nuna damuwa kan yadda ake ƙara samun wariyar ƙabilanci da yankuna, inda ya ce ’yan Najeriya musamman daga wani yanki ke fuskantar tsangwama ba bisa ƙa’ida ba, tare da cin zarafi da azabtarwa a sassa daban-daban na kasar.
“Hakan ya kara muni da yadda ake samun cin zarafi, tsangwama da maganganun ƙiyayya a kafafen sada zumunta, wanda ake cusawa da kabilanci da addini. Wannan na barazana ga hadin kan ƙasa,” in ji shi.
Kwankwaso ya buƙaci gwamnati ta ɗauki mataki cikin gaggawa don dakatar da wannan hatsari kafin ya ƙara tsananta.
Ya ce a matsayinsa na tsohon Ministan Tsaro da kuma Shugaban Kwamitin Kula da Yaɗuwar Ƙananan Makamai, yana matuƙar damuwa da yadda makamai ke yaɗuwa cikin sauki a kasar.
Sai dai ya taya Janar Christopher Gwabin Musa murnar nada shi Ministan Tsaro, yana mai fatan zai yi nasara idan aka ba shi goyon bayan siyasa da ya dace.
“Ina da yaƙinin cewa idan aka ba shi goyon bayan siyasa da ya dace, yana da ƙwarewa da gogewa da za su taimaka wajen dawo da tsaro da zaman lafiya a kasar,” in ji Kwankwaso.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: gwamnati Gwamnatin tarayya Kwankwaso Tsaro
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Iraki Ta Kore Saninta Da Shigar Da Sunayen Hizbullah Da “Ansarullah” A Cikin Na ‘Yan Ta’adda
Fadar gwamnatin kasar Iraki ta sanar da cewa ba ta masaniya akan yadda aka shigar da sunayen Ansarullah na Yemen da kuma Hizbullah ta kasar Lebanon a cikin jerin sunayen kungiyoyin ‘Yan ta’adda da aka rike kudadensu dake bankunan kasar.
Bayanin fadar gwamnatin kasar ta Iraki ya kuma kara da cewa; Matakai irin wadannan da ake dauka a kasar ba a aike wa da su zuwa fadar shugaban kasa,abinda ake aikewa fadar shi ne dokokin da majalisar dokokin kasar ta yi, domin a sake tantancewa da kuma amincewa.”
Haka nan kuma sanarwar ta ce; wasu daga cikin abubuwan da ake aikewa fadar mulkin kasar sun hada da tsare-tsaren fadar shugaban kasa,amma abinda ya shafi matakan majalisar ministoci, da na kwamitin dake dakatar da kudaden ‘yan ta’adda da na kwamitin da yake sa ido akan masu wanke kudaden haram, ba a aikewa fadar gwamatin kasar.”
A karshe bayanin ya ce, fadar gwamantin kasar ba ta da wata masaniya akan matakan da aka dauka na bayyana Ansrullah da Hizbullah a matsayin kungiyoyin ‘yan ta’adda tare da daukar matakan hana amfani da kudadensu a cikin bankunan kasar ta Iraki.
Sanarawar da aka yi a kasqar Iraki a shekarun jiya Alhamis na cewa an hana wasu kungiyoyi da su ka hada “Isis, alka’ida, Ansarullah da kuma Hizbullah, amfani da bankunan kasar domin hada-hadar kudade, ya tayar da kura a cikin da wajen kasar. Mutane sun fito kan titutan kasar ta Iraki domin yin tir da wannan sanarwa.
Sai dai daga baya gwamantin kasar ta janye wannan sanarwa.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Limamin Tehran: Idan Abokan Gaba Su Ka Sake Yin Kuskure Akan Iran Za Su Sake Cin Kasa December 6, 2025 Iran Da Pakisatan Sun Amince Da Farfado da Layin Dogo Tsakanin Istambul, Tehran Zuwa Islamabad December 5, 2025 Iran Ta Raya Ranar Haramta Takunkuman Bangare Guda A Duniya December 5, 2025 Trump Ya Yabawa Rwanda Da Kongo DMK Kan Sulhuntawa A Yakin Gabancin Kongo December 5, 2025 Najeriya: Tinubu Ya Nada Wasu Karin Jakadu 65, Sanatoci Da Tsoffin Gwamnoni Na Daga Cikinsu December 5, 2025 Shin Ziyarar Putin a Indiya alama ce da ke nuna cewa New Delhi na yin watsi da gargadin Trump? December 5, 2025 Iran Ta Mayar Da Martani Kan Sanarwar Bayan Taron Majalisar Kasashen Yankin Tekun Fasha December 5, 2025 Afirka ta Kudu Za Ta Dauki Hutu Daga Halartar Tarukan G20 A Karkashin Shugabancin Trump December 5, 2025 Microsoft Za Ta Fuskanci Hukunci Kan Taimaka Wa Laifukan Isra’ila A Kan Falasdinawa December 5, 2025 Amurka Tana Sake Yin Bitar Alakar Da Ke Tsakaninta Da Tanzania December 5, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci