Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Zamanin kebe kai ya ƙare, Haɗin gwiwar Iran da Rasha ya cimma abin koyi mai nasara

A yayin ganawarsa da ministan makamashin kasar Rasha Sergei Tyswell da tawagarsa, shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa: Nasarar da aka samu na hadin gwiwa tsakanin kasashe masu cin gashin kai kamar Iran da Rasha, ya tabbatar da cewa zamanin kebe kai a duniya ya kare.

Ya kuma jaddada cewa, wadannan kasashe suna iya samun ci gaba da bunkasa ba tare da bukatar ko dogaro da karfi mai amfani da bangare guda.

Shugaban na Iran ya bayyana jin dadinsa da ci gaban hadin gwiwar kasashen biyu, musamman a fannin sufuri, makamashi, da ayyukan samar da wutar lantarki. Ya kara da cewa, Iran ta dora aiwatar da yarjejeniyoyin da aka kulla da kasar Rasha a kan muhimman abubuwan da ta sa a gaba, da cewa, dukkan muhimman ababen more rayuwa na hadin gwiwa suna nan, kuma babu wani abin da ke kawo cikas ga hanyar hadin gwiwa tsakanin Iran da Rasha.

Pezeshkian ya kara da cewa, tilas ne a fassara sakamakon tarurruka na fasaha cikin sauri, yana mai bayyana cewa, nufin bangarorin biyu, tare da muhimmin alkiblar shugaba Vladimir Putin, na tilasta wa ministoci da kungiyoyin fasaha su hanzarta saurin aiki, da kuma kammala ayyukan hadin gwiwa.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Ce: Iran Ta Sauke Hakkin Da Ya Hau Kanta Sauran Bangaren Turai September 18, 2025 Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ya Ce: Masu Goyon Bayan Isra’ila Suna Da Hannu A Laifukanta September 18, 2025 Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Cika Kwanaki 713 Suna Kisan Kiyashi A Zirin Gaza September 18, 2025 Harin Makami Mai Linzami Yemen Ya Tilastawa Jirgin Fira Ministan Gwamnatin Isra’ila Saukar Gaggawa September 18, 2025 Eslami: Dole ne IAEA ta zama mai cikakken ‘yancin cin gashin kai September 18, 2025 Rahoto: An yi tattaunawa mai tsawo tsakanin Syria da Isra’ila a Landan September 18, 2025 Sheikh Qassem: Harin Pager jarabawa ce wadda ta kara wa masu gwagwarmaya kwarin gwiwa September 18, 2025 Pezeshkian: Iran da Masar suna da tsohon tarihi a duniya September 18, 2025 Iran ta samu Zinariya, Azurfa, da Tagulla a Gasar Kokawa ta Duniya September 18, 2025 Iran Ta Yi Nasarar Gwajin Tauraron Dan’adam Da Zai Samar Da “Internet” Ga Yankunan Karkara September 17, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: Iran da Rasha hadin gwiwa

এছাড়াও পড়ুন:

Eslami: Dole ne IAEA ta zama mai cikakken ‘yancin cin gashin kai

Shugaban Hukumar Nukiliya ta Iran ya ce barazanar da makiya Jamhuriyar Musulunci ta Iran ke ci gaba da yi tun bayan harin ba-zata da Isra’ila da Amurka suka kai kan cibiyoyin nukiliyar kasar, na kara nuni da cewa dole ne hukumar IAEA ta zama mai cikakken ‘yancin cin gashin kai, ba wurin aiwatar da siyasar adawa da kasar Iran ba.

Mohammad Eslami, wanda shi ne shugaban hukumar makamashin nukiliya ta Iran (AEOI), ya bayyana hakan ga kamfanin dillancin labarai na Kyodo na Japan a wata rubutacciyar hira da aka buga a ranar Laraba.

Ya kara da cewa halin da ake ciki na tsaro na cikin hadari, domin kuwa yanayi da ya yi kama da lokacin yaki saboda irin barazana da gwamnatin Isra’ila ke ci gaba da yi a kan Iran.” in ji shi.

A cikin watan Yuni ne gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila  ta kallafa wa Iran yaki, inda ta kai munanan hare-hare kan cibiyoyin nukiliyarta, da kayayyakin kariya, da jami’an soji, da masana kimiyyar nukiliya, da kuma fararen hula.

Kimanin mutane 935 da suka hada da kananan yara ne suka yi shahada a yakin da aka kwashe kwanaki 12 ana yi.

Amurka ta shiga tsaka mai wuya, bayan da ta kai hari kan wasu muhimman cibiyoyin nukiliyar Iran.

A cewar Eslami, “Wannan shi ne karo na farko a tarihi da aka kai wa tashoshin nukiliyar kasar hare-haren soji.”

Ya sake jaddada cewa, wannan zaluncin ya sanya Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba za ta iya ci gaba da yin hadin gwiwa da Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA) kamar yadda ya gabata ba.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Rahoto: An yi tattaunawa mai tsawo tsakanin Syria da Isra’ila a Landan September 18, 2025 Sheikh Qassem: Harin Pager jarabawa ce wadda ta kara wa masu gwagwarmaya kwarin gwiwa September 18, 2025 Pezeshkian: Iran da Masar suna da tsohon tarihi a duniya September 18, 2025 Iran ta samu Zinariya, Azurfa, da Tagulla a Gasar Kokawa ta Duniya September 18, 2025 Iran Ta Yi Nasarar Gwajin Tauraron Dan’adam Da Zai Samar Da “Internet” Ga Yankunan Karkara September 17, 2025 Za A Kada Kuri’ar Raba Gardama Akan Sabon Tsarin Mulki A Kasar Guinea September 17, 2025 Larijani: Iran Da Saudiyya Za Su Bunkasa Aiki Tare A Fagagen Kasuwanci Da Tsaro September 17, 2025 Hukumar Tarayyar Turai Ta Gabatar Da Shawarar Jingine Aiki Da Yarjejeniyar Kasuwanci Da HKI September 17, 2025  Gaza: HKI Tana Ci Gaba Da Yi Wa Falasdinawa  Kisan Kiyashi A Gaza September 17, 2025 Ma’aikatar Shari’ar Iran Ta Sanar Da Rataye Dan Leken Asirin Hukumar Mossad Ta Isra’ila September 17, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Eslami: Dole ne IAEA ta zama mai cikakken ‘yancin cin gashin kai
  • Sheikh Qassem: Harin Pager ya kara wa masu gwagwarmaya a Lebanon kwarin gwiwa
  • Iran Ta Bayyana Abubuwan Da Bata Amince Da Su Ba A Jawabin Bayan Taro Na Kungiyar OIC A Birnin Doha
  • Iran da Saudiyya sun bukaci hadin Musulmi game da halin da ake ci a yankin
  • Kungiyar Human Rights Watch; Isra’ila Ta Kashe ‘Yan Jarida Fiye Da 30 A Kasar Yemen Ne Da Gangan  
  • Hadin Gwiwar Raya Tattalin Arziki Da Cinikayya Da Makamashi Tsakanin Sin Da Rasha Ba Abun Zargi Ba Ne
  • Bayanin Bayan Taron Doha Ya Yi Kira Da A Kafa Runduwar Hadin Gwiwa Ta Kare Kai
  • Shugaban Kasar Iran Ya Gana Da Sarkin Kasar Qatar A Birnin Doha
  •  Dan Kasar Iran Mai Kirkira Ya Sami Kyautar Yabo A Kasar China