Al’ummar Jihar Sakkwato na cike da fargaba da alhini bayan da wasu mazauna kauyuka da dama suka rasu a hatsarin kwale-kwale a Karamar Hukumar Sabon Birni ta Jihar Sakkwato.

Lamarin ya faru ne lokacin da jama’a ke tserewa daga wani sabon harin da ‘yan ta’addan Lakurawa suka kai, inda kwale-kwalen da ke dauke da mutane fiye da kima ya kife.

Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na Rundunar ‘Yan sandan Jihar Sakkwato, ASP Abubakar Rufa’i, ya tabbatar da aukuwar lamarin ga wakilin Rediyon Najeriya a jihar.

ASP Abubakar ya ce har yanzu ba a tantance adadin mutanen da suka shiga kwale-kwalen ba, yana mai jaddada cewa ana ci bincike da aikin ceto.

Wani shaidan gani da ido, wanda bai so a bayyana sunansa ba ya shaida wa Rediyon Najeriya cewa wadanda lamarin ya rutsa da su mutanen kauye ne da suka tsere daga matsin lambar ‘yan bindigar Lakurawa.

Wannan hatsarin shi ne na huɗu da ya yi sanadiyyar rasa rayuka a cikin watanni biyu a Sakkwato, lamarin da ya haifar da fargaba kan matsalar tsaro da kuma hatsarin shiga kwale-kwale a yankin.

Mazauna Sabon Birni da kauyuka makwabta na ci gaba da zama cikin zullumi, inda miyagu ke kafa shingayen bincike, kona gonaki da korar jama’a daga kauyuka.

Rediyon Najeriya ta ruwaito cewa iyalan da suka rasa ‘yan uwansu sun yi cirko-cirko a bakin kogin, yayin da masu aikin ceto ke ci gaba da nemo wadanda suka bace.

 

Daga Nasir Malali

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Hatsarin Kwale kwale Lakurawa Sakkwato kwale kwale

এছাড়াও পড়ুন:

Wata Mata Ta Ƙona Al’aurar Ƙaramar Yarinya A Bauchi

Rundunar ƴansanda a Jihar Bauchi ta tabbatar da kama wata mata, wadda ake zargi da yi wa wata yarinya ‘yar shekara bakwai mummunan rauni ta hanyar ƙona mata al’aura da wuka mai zafi a garin Magama Gumau, ƙaramar hukumar Toro.

Rahotanni sun ce matar ta zargi yarinyar da maita, lamarin da ya sa ta yi amfani da wuka da aka zafafata a wuta wajen ƙona jikinta. Ihun yarinyar ne ya jawo hankalin maƙwabta, inda suka yi gaggawar zuwa suka ceceta tare da sanar da ‘yansanda.

Gwamnan Bauchi Ya Gargaɗi Magoya Bayan Wike A PDP An Cafke Mutum Hudu Bayan ‘Yan Fashi 20 Sun Afka Wasu Gidaje A Bauchi

Wani mai fafutukar kare haƙƙin yara a yankin, Kabiru Mohammed Abdulkadir, ya bayyana cewa lamarin ya samo asali ne daga iƙirarin ɗiyar matar, wadda ta ce ta ga yarinyar cikin wata ƙungiyar mayu. Ya ƙara da cewa hakan ya haddasa munanan raunuka, inda aka samu al’aura da cinyoyin yarinyar sun ƙone har ma raunukan suka fara ruɓewa, lamarin da ya sa ta kasa yin fitsari da bayan gida yadda ya kamata.

Yarinyar ta na samun kulawa a asibitin koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBUTH), Bauchi, bayan an garzaya da ita domin ceto rayuwarta. Kakakin rundunar ‘yansandan jihar, CSP Ahmed Mohammed Wakil, ya tabbatar da cewa an fara bincike kuma za a gurfanar da wacce ake zargi a kotu domin fuskantar hukunci.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Mutum 9 sun rasu a hatsarin jirgin ruwa a Sakkwato
  • ’Yan bindiga sun kashe basarake, sun tarwatsa mutane a Sakkwato
  • Makarantun Da Ba Ƙwararrun Malamai Za Su Rasa Zama Cibiyar Rubuta Jarrabawar NECO
  • Wata Mata Ta Ƙona Al’aurar Ƙaramar Yarinya A Bauchi
  • An dakatar da shugabannin sakandare 6 a Sakkwato kan zargin cin amanar aiki
  • Mutum 1,666 ne suka kashe kansu a Legas cikin shekaru biyar – ’Yan sanda
  • An kashe ’yan ta’addan IPOB da yawa a Imo — ’Yan Sanda
  • Mataimakin Gwamnan Zamfara Ya Jajantawa Al’ummar Gumi
  • Eslami: Dole ne IAEA ta zama mai cikakken ‘yancin cin gashin kai