Aminiya:
2025-09-18@14:09:00 GMT

Yadda jariri ya rasu a bayan mahaifiyarsa yayin tsere wa harin ’yan bindiga a Neja

Published: 18th, September 2025 GMT

Wani jariri ya rasu a bayan mahaifiyarsa lokacin da take kokarin tserewa daga harin ’yan bindiga a ƙauyen Allawa da ke ƙaramar hukumar Shiroro ta Jihar Neja.

Hakkin ya fito ne daga bakin Hakimin Bassa, Bagudu Amos, yayin wani taron tattaunawa da mata kan rikici da zaman lafiya mai taken: “Ƙarfafa Matakan Kare Fyade da Cin Zarafin Mata a Jihar Neja”.

Gwamnatin Gombe ta gyara hanyoyin kiwo domin daƙile rikicin manoma da makiyaya HOTUNA: Yadda dubban magoya baya suka yi dafifi don tarbar Fubara

Taron dai wata kungiya mai zaman kanta mai suna Tunani Initiative ce ta shira shi, tare da hadin gwiwar gidauniyar Dorothy Njemanze Foundation da kuma gidauniyar Foundation, domin ƙarfafa gwiwar mata wajen magance cin zarafin jinsi a jihar.

Hakimin ya ce mahaifiyar ta yi tafiya mai nisa domin tserewa daga farmakin ’yan bindigar, ba tare da ta san cewa jaririn da ke bayanta ya riga ya mutu ba.

Ya ce lamarin da ya faru a shekarar 2023 na daga cikin abubuwan da ke ci wa mata ’yan gudun hijira tuwo a ƙwarya a kullum, inda ya ƙara da cewa yawancin matan ba su da gogewar ilimin da zai ba su damar tinkarar cin zarafin jinsi da ke tasowa sakamakon rashin tsaro.

Shugabar ƙungiyar Tunani Initiative, Maryam Mairo Ibrahim, ta ce ana buƙatar a ba mata dama wajen samar da zaman lafiya da warware rikice-rikice a Jihar Neja.

Ta yi kira ga mata da su haɗa kai don karya shingen da ke hana su yin tasiri a rayuwa.

Ta ce, “A Jihar Neja, kamar yadda ake fama da rashin tsaro a wasu wurare, mata su ne suka fi shan wahalar mafi yawan hare-hare da kashe-kashen da ake yi. Idan ’yan bindiga suka kai hari, yawanci maza ne ake kashewa, sai matan da aka bari su ɗauki nauyin sake gina iyali.

“Wadannan rawar da mata ke takawa ba a lura da ita yadda ya kamata. Saboda haka, wannan tattaunawa ta mayar da hankali ne kan ƙarfafa rawar da mata ke takawa wajen samar da zaman lafiya da kuma magance cin zarafin jinsi a Jihar Neja,” in ji ta.

Daraktan Hukumar Kare Haƙƙin Dan Adam ta Jihar, Nuhu Muhammad, ya jaddada buƙatar ƙara yawan mata a majalisar dokoki ta jiha da ta ƙasa, domin samar da dokoki da manufofi da suka dace da bukatunsu.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Bindiga Jariri a Jihar Neja

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnatin Kano Ta Inganta Cibiyoyin Horas Da Sana’o’i Domin Dakile Aikata Laifuka Tsakanin Matasa

Gwamnatin Kano ta raba kayayyakin aiki na zamani na kimanin Naira Miliyan 250  ga cibiyoyin horas da sana’o’in hannu biyu da ke Kofar Mata da Gwale, domin yaƙi da shan miyagun kwayoyi da aikata laifuffuka a tsakanin matasa, ta hanyar samar da aikin yi.

Kwamishinan Kimiyya da Fasaha, Dakta Yusuf Kofarmata, ya ce an amince da tallafin ne bisa umarnin Gwamna Abba Kabir Yusuf don bunƙasa tsare-tsaren ƙarfafa matasa a jihar.

Ya bayyana cewa an samar da injinan sarrafa fata guda 26 domin cibiyoyin wadanda al’ummar yankunan suka kafa, amma ba su da isassun kayayyakin aiki.

Ya ce Gwamna Yusuf ne ya gina Cibiyar Horaswar ta Gwale  kasancewar nan ce mazabarsa, yayin da Dakta Yakubu Adam ya taka rawa wajen gina ta Kofar-Mata.

Ya ce cibiyoyin za su samar da daruruwan ayyukan yi tare da rage matsalolin zaman kashe-wando da ta’addanci a tsakanin matasa.

 

A nasa jawabin, Ali Musa Kofar-Mata na ƙungiyar IKMA ya gode wa gwamnati bisa wannan gudummawar da ya kira mai sauya rayuwa.

Ya ce cibiyar ta fara ɗaukar matasa maza da mata, kuma horon zai ɗauki watanni uku kafin a shiga sabon zagaye.

 

Abdullahi Jalaluddeen 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Yadda Ribas Ta Yi Cikar Ƙwari Yayin Da Gwamna Fubara Ya Koma Ofis
  • HOTUNA: Yadda dubban magoya baya suka yi dafifi don tarbar Fubara
  • Yadda Jama’a Ribas Ta Yi Cikar Ƙwari Yayin Da Gwamna Fubara Ya Koma Ofis
  • Uwargidan Shugaban Kasa, Oluremi Tinubu Ta Yi Kira Ga Zaman Lafiya A Duniya
  • ’Yan bindiga sun sako ma’auratan da suka sace a Katsina bayan biyan N50m
  • Karamar Hukumar Malam Madori Ta Horar Da Mata Kare Kai Daga Cututtukan Mahaifa
  • An tattauna yadda za a inganta walwalar malamai a Gombe
  • Gwamnatin Kano Ta Inganta Cibiyoyin Horas Da Sana’o’i Domin Dakile Aikata Laifuka Tsakanin Matasa
  • ’Yan bindiga sun kai wa sojoji hari a ranar da ake zaman sulhu