2025-12-11@07:52:53 GMT
إجمالي نتائج البحث: 3181
«Ya ce gwamnan»:
Daga Usman Muhammad Zaria Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu, Dr. Builder Muhammad Uba, ya umarci a gaggawata gyaran bututun da suka hada tashar tacewa da samar da ruwa yankunan Dutsawa da Kantudu. Wannan mataki ya biyo bayan matsalolin da ake yawan fuskanta sakamakon lalacewar wutar lantarki da na’urar janareto, wanda ke hana jama’a samun ruwa yadda ya kamata. Yayin da yake bayyana jimaminsa bisa wannan lamari, Dr. Muhammad Uba ya basu tabbacin cewa In Shaa Allahu matsalar ta zo karshe. A cewarsa, majalisar ta kudirin aniyar yin duk mai yiwuwa domin magance matsalolin da ake fuskanta tare da tabbatar da samun isasshen tsaftataccen ruwan sha ga al’umma. Ya yi alkawarin tura dukkan kayan aiki da ake bukata domin...
Shugaban kasar |iran Mas’ud pezeshkiyan da yake Magana a wajen taron ranar mata a kasar iran ya bayyana cewa maza ta da mata suna taka rawa iri daya wajen ciyar da alumma gaba, kan kyawawan ayyukan, kana ya jaddada cewa mata musamman iyaye suna taka muhimmiyar rawa wajen samar da matasa masu tasowa da kuma nusar da Alumma kyakkyawar makoma. Kyawawan halayen musulunci wasu ginshi kai ne da suke daidaita maza da mata, saboda Al’qur’ani yayi alkawarin kyakkyawar rayuwa ga wadanda suka yi kyawawan ayyuka, da gaskiya ba tare da la’akari da jinsin su suba, haka zalika ya jaddada wannan ka’ida inda aka tsara mata ba a matsayin na biyu ba, amma a matsayin muhimmin abokan hulda wajen gina ci...
Jami’ai sun ce mutane sama da dubu 500 ne kawo yanzu aka tursasawa barin muhallansu a Thailand da kuma Cambodia a yayin da rikicin kan iyaka tsakanin ƙasashen biyu ke ƙara ƙamari. Rundunar sojin Thailand ta ce Cambodia ta harba mata dubban makaman roka tun bayan da suka soma rikici da juna. Dubban mutane ne suke guduwa domin tserewa lugudan makaman roka da ake harbawa daga Cambodia. Kazalika Thailand ma na ci gaba da kai wa Cambodia hare-hare ta sama. Shugaba Donald Trump na Amurka ya ce yana kyautata tsammanin zai gana da shugabannin kasashen biyu ta wayar tarho, wanda ya matsa musu lamba aka cimma kwarya-kwaryar yarjejeniyar tsagaita wuta a watan Yulin da ya gabata. To sai dai ministan...
Taron kasa da kasa na musamman wanda aka gudanar a wata Jami’a a nan Tehran dangane da nasarar da JMI ta samu kan HKI da Amurka a yakin kwanaki 12 a cikin watan yulin da ya gabata ya jawo hankalin kasashen duniya da dama, sannan ya sauya yadda ake daukar HKI a yankin, musaman a matsayin kasa wacce ta fi ko wace kasa karfi soji a yankin. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa masu halattan taron sun bayyana muhimmancin wannan nasarar karkashin jagorancin Jagoran Juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khaminae a matsayin babban sauyi a yankin gabas ta tsakiya da kuma duniya gaba daya. Labarin ya bayyana cewa yan siyasa da sauran mahalatta taron...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A kwanakin nan, tawagar ’yan majalisar dokokin Amurka ta kawo ziyara Najeriya domin tattaunawa kan tsaro da tashin hankalin da ake ta fama da shi a yankunan Arewa da tsakiyar ƙasar, musamman rikice-rikicen da suka yi sanadiyyar kashe-kashe da duniya ke fargabar suna iya daukar salo na kisan kare dangi ga Najeriya. Ko wannan ziyarar da tawagar Amurka ta kawo zai kawo karshen matsalar tsaron da Najeriya ke ciki? NAJERIYA A YAU: Yadda Abincin Da Mutane Ke Ci Ke Zamewa Guba DAGA LARABA: Kalubalen Dake Gaban Janar Christopher Musa A Matsayin Ministan Tsaro Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai duba a kai. Domin sauke shirin, latsa nan
Jaridar Daily Trust da gidan talabijin na Trust TV, dukkansu mallakar kamfanin Media Trust, a bana ma sun sake yin fice bayan ’yan jaridansu suka lashe kyautar binciken kwakwaf ta Wole Soyinka ta bana. ’Yan jaridar na Daily Trust da Trust TV, Afeez Hanafi da Muslim Muhammad Yusuf, sun lashe gasar ne a matsayin zakaru a rukunin rahoton jarida da kuma na talabijin mafi daraja a bana a Najeriya. Majalisar Dattawa ta amince Tinubu ya tura sojojin Najeriya zuwa Jamhuriyar Benin Sojoji sun kashe ’yan bindiga 13, sun ceto ’yan kasuwa a Sakkwato Hanafi ya lashe rukuni na rubutu bisa labarinsa mai taken: “Bincike: Dan jarida ya samu ayyuka biyu da takardun bogi na Oluwole.” Wanda ya zo na biyu...
Kakakin rundunar sama ta tarayyar Najeriya, wato ‘Nagerian Air Force’ Ehiment Ejodame ya bayyana cewa jirgin wani jirgin saman rundunar dauke da mutane 11 ya yi saukan gaggawa a kasar Burkina Faso a ranr litinin da ya gabata. Jiridar Daily Trust ta Najeriya ta nakalto Ejodame yana fadar haka a yau Talata ya kuma kara da cewa kungiyar kasashen AES sun tilastawa jirgin sauka a Bobo Dioulasso na Burkina Faso bayan zargin cewa jirgin ya keta hurumin sararin samaniyar kasar ba tare da izini ba. A halin yanzu dai ana saran za’a warware matsalar da ke tsakanin kasashen biyu sannan jirgin zai kama hanyarsa zuwa kasar Portigal kamar yadda aka tsara. Labarin ya kara da cewa, jirgin ya tashi daga...
Gwamantin Nigeria ta aike da jiragen yaki zuwa kasar Benin domin taimaka wa gwamnatin farar hula domin dakile yunkurin juyin mulkin da aka yi a kasar. Aikin da jiragen yakin su ka fara yi, shi ne shimfida ikonsu a sararin samaniyar kasar Benin a ranar Lahadin da ta gabata,adaidai lokacin da sojoji da suke biyayya ga shugaba Patrice Talon su ka fafatawa da sojojin da suke kokarin mayar da doka da oda. Ofishin shugaban kasar ta Nigeria, Ahmad Tininu ya kuma yi bayanin cewa; Daga cikin ayyukan da sojojin na Najeriya su ka yi a tare da hadin gwiwar takwarorinsu na Benin masu biyayya ga gwamnati, shi ne sanya idanu da kuma zama cikin ko ta-kwana domin aikewa da sojoji...
A wani rahoton da jaridar Jerissalam Post” ta buga ta ambaci cewa; Tun bayan farmakin 7 ga watan Oktoba 2023, ana kara samun matalauta da talauci. Rahoton ya yi nuni da cewa karuwar talaucin yana da alaka ne da yadda farmakin 7 ga watan Oktoba ya yi tasiri a cikin tattalin arziki “Isra’ila”. Haka nan kuma rahoton ya ce, da akwai dubban iyalai yahudawa wadanda gabanin yaki, suke rayuwa cikin yanayi mai kyau ta fuskar tattalin arziki, yanzu sun zama matalauta. A dalilin haka cibiyar da ta shirya rahoton ta “ Latit” tana yin gargadi akan cewa; za a iya samun ci gaba da yaduwar talaucin, domin iyalai da dama suna gogoriyon yadda za su iya biyan bukatar yau da...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A yau al’ummar mu na fuskantar barazana ta wata siga da ba kasafai ake gane ta ba, wato guba da ke shiga jikin ɗan Adam ta hanyar abinci irin su nama, kifi, madara da sauran kayayyakin da muke ci a kullum. Sau da yawa dabbobi ko kifaye suna cin wasu tsirrai, ganye, ko ababen da ke dauke da sinadarai masu haɗari, waɗanda daga baya suke taruwa a jikinsu har su zama guba ga mutum idan aka ci su. Wasu lokuta ma waɗannan gubobi ba daga abincin dabbar suke fitowa ba, sai dai daga sinadarai da ake amfani da su wajen kiwon su kamar magungunan kiwo, sinadaran rigakafi, ko ma gurɓatattun ruwa da...
Daga Aliyu Muraki Gwamna Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa ya ce gwamnonin Arewa sun amince su sayi na’urorin zamani na tsaro da kuma daukar matasa aiki don tallafawa ayyukan tsaro domin magance matsalolin rashin tsaro a yankin. Gwamnan ya bayyana hakan ne a zaman Majalisar Zartarwa ta Jihar da aka gudanar a Lafia, babban birnin jihar. Gwamna Abdullahi Sule, wanda shi ne shugaban kungiyar gwamnonin Arewa ta Tsakiya, ya ce an cimma wannan matsaya ce a taron gwamnonin Arewa da aka yi a Kaduna kwanan nan. A cewarsa, gwamnonin Arewa sun amince cewa kowace jiha za ta rika bada gudummawar Naira Biliyan Daya a kowane wata na tsawon shekara guda domin samar da kudin da zai taimaka wajen magance...
Daga Nasir Malali An kashe ’yan bindiga guda goma sha takwas a wani samame da Rundunar Hadin Gwiwa ta Operation Fansan Yamma ta kai a kauyen Kurawa da ke Karamar Hukumar Sabon Birni ta Jihar Sokoto. A wata hira ta wayar tarho, wani shaida daga yankin, Malam Aminu Muhammad, ya shaida wa Rediyon Najeriya a Sokoto cewa, nasarar samamen ta fara ne bayan rundunar ta samu bayanin cewa wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da mazauna yankin da ke kan hanyarsu ta zuwa kasuwar mako-mako a kan hanyar Tarah zuwa Karawa a Sabon Birni. Sojojin sun garzaya cikin gaggawa bayan jin harbe-harbe, inda suka kusan awa guda suna musayar wuta da maharan. Shaidan gani da idon ya ce sojojin sun ...
Daga Bello Wakili Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi ganawar sirri da gwamnonin jihohi shidda daga sassan ƙasar a ci gaba da tattaunawar da ake yi domin ƙarfafa batun tsaro a ƙasa. Gwamnonin da suka halarci taron sun hada da Gwamna Monday Okpebholo na jihar Edo, Umar Namadi na Jigawa, Nasir Idris na Kebbi, Ahmed Ododo na Kogi, Lucky Aiyedatiwa na Ondo, da Ahmed Aliyu na jihar Sokoto. Taron, wanda ya ɗauki kusan mintuna 40, ya mayar da hankali ne kan muhimman matsalolin tsaro da ke shafar jihohinsu, duk da cewa ba a bayyana cikakkun bayanai ba. Wakilin Rediyon Najeriya da ke fadar shugaban kasa ya ruwaito cewa wannan zaman na daga...
Dakarun kare juyin juya halin musulunci na kasar Iran ya bayyana cewa makamai masu linzamu na dakarun sun fada kan matatar man fetur na Haifa a HKI har sau biyu a yakin kwanaki 12 da ta fafata da Iran a cikin watan Yunin wannan shekara. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Burgediya Janar Ali Mohammad Naeini kakakin dakarun ya na fadar haka a jiya Lahadi a wani taro, ya kuma kara da cewa makaman har’ila yau sun kashe jami’an hukumar leken asirin HKI MOSAD har 36 a wani hari kan ginin hukumar a cikin yakin. Naeini, ya kara da cewa HKI ta yi kuskuren lissafi a lokacinda ta farwa kasar Iran da yaki a cikin watan Yunin...
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bada sanarwan kubutar da yan makaranta 100 daga cikin wadanda ‘yan ta’adda suka sace a wata makaranta a jihar Naija a cikin watan Nuwamban da ya gabatata. Tashar talabijan ta almayadeen ta kasar Lebanon ta nakalto kamfanin dillancin labaran reuters na cewa jami’an tsaron kasar sun sami nasarar kubutar da yan makaranta har 100 daga cikin wadanda yan ta’adda suka sacesu a wata makarantar cocin Khatolica a cikin jihar Naija. Kafin haka an ce yara kimani 50 sun tsere daga hannun yan ta’addan bayan an sacesu. Tashar talabijin ta ‘Chennel TV ‘ ta bada labarin cewa sakin yan makarantan, amma bata nuna hotunansu ba kuma bata yi wani karin bayani ba. Sannan kungiyar kiristoci ta Najeriya...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Batun samar da ‘yansandan jihohi na ƙara ɗaukar hankalin ‘yan Najeriya, musamman a dai-dai lokacin da matsalar tsaro ke ƙara ta’azzara a sassa daban-daban na ƙasar nan. Sai dai, samar da ‘yansandan jihohi ba abu ne mai sauƙi Kamar yadda wasu ke tunani ba. Gwamnatocin jihohi na buƙatar abubuwa masu yawa kafin su iya ɗaukar wannan nauyi, banda batun samar da dokar samar da wadannan ‘yansanda, akwai batun samar da kayan aiki da horo da sauran abubuwa da ake bukata don gudanar da dawainiyar ‘yansandan. NAJERIYA A YAU: Abun Da Masu Ruwa Da Tsaki Ke Yi Na Dakile Laifuka A Wurin Matasa DAGA LARABA: Kalubalen Dake Gaban Janar Christopher Musa A Matsayin...
Masana harkokin siyasa, jakadu da ƙungiyoyin fararen hula sun bayyana cewa rashin shugabanci nagari da son mulki na dogon lokaci su ne manyan dalilan da ke haddasa yawaitar juyin mulki a yankin Afirka ta Yamma. Wannan na zuwa ne bayan yunƙurin juyin mulki da aka yi a Jamhuriyar Benin a ranar Lahadi, wanda ya jefa ƙasar cikin rudani. Gwamnatin Benin ta ce ta shawo kan lamarin bayan wasu sojoji sun bayyana a talabijin na ƙasar cewa sun kifar da Shugaba Patrice Talon. Wannan na zuwa ne makonni kaɗan bayan juyin mulki a ƙasar Guinea-Bissau. Majiyoyin tsaro sun tabbatar da kama sojoji kusan 12, ciki har da shugabannin yunƙurin da bai yi nasara ba. Talon, tsohon ɗan kasuwa mai shekaru 67,...
Rundunar Sojin Saman Najeriya (NAF), ta ce ta taka muhimmiyar rawa wajen daƙile yunƙurin juyin mulki a Jamhuriyar Benin, bayan wasu sojoji sun bayyana hamɓarar da Gwamnatin Shugaba Patrice Talon. Gungun sojojin, sun bayyana cewa ta rushe gwamnati tare da dakatar da kundin tsarin mulki, da rufe iyakokin ƙasar. An gano gawar malamin Islamiyya da ya ɓace a Neja Mutum 5 sun rasu sanadin gobara da faɗa wa rijiya a Kano Sun kuma ayyana Laftanar Kanar Tigri Pascal a matsayin Shugaban gwamnatin soja. Daga baya gwamnatin Benin ta sanar da cewa sojojin ba su yi nasarar yin juyin mulkin ba. Rahotanni sun nuna cewa jiragen yaƙin Najeriya sun shiga ƙasar domin kare dimokuraɗiyya, duk da cewa babu cikakkun bayanai ba....
’Yan bindiga sun kai sabon hari wasu yankuna na Jihar Sakkwato, inda suka kashe mutane huɗu tare da yin awon gaba da mata huɗu. Wani mazaunin Gatawa, ya shaida wa Aminiya ce harin ya faru ne a daren ranar Asabar, lokacin da ’yan bindiga sama da goma suka shiga garin a kan babura. Mutum 5 sun rasu sanadin gobara da faɗa wa rijiya a Kano Sojoji sun yi yunkurin juyin mulki a Jamhuriyar Benin A cewarsa, “Sun ratsa gefen gari suka dinga shiga gida-gida. Sun harbe mutane huɗu; uku sun mutu nan take, na huɗu kuma ya rasu a asibiti.” Ya ƙara da cewa bayan harin, sojoji sun isa garin wanda hakan ya sa maharan suka tsere, amma duk da...
’Yan bindiga sun kai sabon hari wasu yankuna na Jihar Sakkwato, inda suka kashe mutane huɗu tare da yin awon gaba da mata huɗu. Wani mazaunin Gatawa, ya shaida wa Aminiya ce harin ya faru ne a daren ranar Asabar, lokacin da ’yan bindiga sama da goma suka shiga garin a kan babura. Mutum 5 sun rasu sanadin gobara da faɗa wa rijiya a Kano Sojoji sun yi yunkurin juyin mulki a Jamhuriyar Benin A cewarsa, “Sun ratsa gefen gari suka dinga shiga gida-gida. Sun harbe mutane huɗu; uku sun mutu nan take, na huɗu kuma ya rasu a asibiti.” Ya ƙara da cewa bayan harin, sojoji sun isa garin wanda hakan ya sa maharan suka tsere, amma duk da...
Gwamnatin Jamhuriyar Benin ta bayyana cewa ta dakile wani yunkurin juyin mulki, bayan da wasu sojojin ƙasar suka sanar da cewa sun hambarar da shugaba Patrice Talon a gidan talabijin na kasar. Talon, mai shekaru 67, tsohon dan kasuwa ne wanda aka yiwa lakabi da “Sarkin Auduga na Cotonou”, zai mika mulki a watan Afrilun shekara ta 2025 dake ƙaratowa, bayan shafe shekaru 10 a kan karagar mulki wanda ke nuna samun ci gaban tattalin arziki mai inganci. Da sanyin safiyar Lahadi ne sojojin da ke kiran kansu da suna “Kwamitin Soji na sake farfado da ƙasa” (CMR), suka gabatar da wata sanarwa a gidan talabijin na kasar cewa sun gana kuma sun yanke shawarar cewa “An tsige shugaba Patrice...
An harbe wani jami’in ɗan sanda har lahira, yayin da yake tsaka da binciken ababen hawa a Benin a Jihar Edo. Kakakin rundunar, CSP Moses Yamu, ya ce lamarin ya faru da misalin ƙarfe 12 na ranar Juma’a, lokacin da jami’an rundunar suka tsayar da wata baƙar mota ƙirar Lexus, amma ta ƙi tsayawa. ’Yan sanda sun ceto yara 2 da aka yi garkuwa da su a Borno Ƙasashen waje na taimaka wa ’yan ta’adda a Najeriya —Sheikh Gumi Ɗaya daga cikin mutanen da ke cikin motar ya buɗe wa jami’an da ke shingen wuta, sannan suka tsere. A dalilin haka ne suka harbe wani ɗan sanda wanda ba a bayyana sunansa ba har lahira. Kwamishinan ’yan sandan jihar, Monday...
’Yan sanda sun ceto yara 2 da aka yi garkuwa da su, masu shekaru hudu da biyar, a Jihar Borno. An ceto yaran ne a yayin wani samame da ’yan sanda suka kai a Ƙaramar Hukumar Jere, inda masu garkuwar suka je karbar kuɗin fansa. Sanarwa da ASP Nahum Kenneth Daso, kakakin rundunar ya fitar ta ce, bayan sun sami rahoto a ranar 4 ga Disamba cewa yara uku sun bace, washegari masu garkuwar suka sako ɗaya daga cikin yaran da takardar neman naira miliyan 10 domin sakin sauran biyun. A ranar ce jami’an rundunar suka kai samame a wurin da aka ware don karɓar kuɗin fansar. Ganin hakan masu garkuwa da mutanen, suka farga da wannan tarko da aka...
Gwamnatin Kano ta tabbatar da kama Muhuyi Magaji Rimingado, tsohon shugaban hukumar yaƙi da cin hanci ta jihar ranar Juma’a, inda ta yi zargi wasu ‘yansiyasa da hannu a kamen nasa. Wata sanarwa daga ofishin Kwamashinan Shari’a Abdulkarim Maude ta ce jami’an ‘yansanda ne suka kama lauyan a ofishinsa da ke kan titin Zariya da misalin ƙarfe 5:30 na yamma, kuma suka tafi da shi hedikwatarsu da ke Bompai. Kwamashinan ya siffanta kamen da “abin damuwa sosai” wanda “ya yi kama da yanayin aikin soja”. Ya yi iƙirarin cewa dakaru kusan 40 ne ɗauke da makamai suka je kama Muhuyi. “Kwamashinan ya nuna cewa akwai yiwuwar lamarin yana da alaƙa da binciken da ake yi wa wasu manyan ‘yansiyasa,” in...
Makwanni biyu bayan da masu garkuwa su ka sace kananan yara ‘yan mamaranta an bayyana cewa;har yanzu da akwai 250 a hannun barayin mutanen. A ranar 21 ga watan Nuwamba ne dai masu dauke da makamai su ka kutsa cikin wata makaranta ta majami’ar Roman Katolika, su ka yi awon gaba da dalibai 300 da kuma malamai. Mahukuntan makarantar sun ce dalibai 50 sun iya tserewa daga hannun wadanda su ka yi garkuwar da su, don haka har yanzu da akwai wasu 250 da suke a hannun barayin. Sace daliban da aka yi na bayan nan, shi ne mafi muni,tun wanda aka yi wa daliban makarantar Chibok a 2014 da adadinsu ya kai 276 a hannun Bokoharam. Jami’an tsaron kasar...
Shugaban kasar Rasha Vladmir Putin wanda ya kai ziyarar aiki kasar India ya bayyana cewa kasar tasa da kuma abokiyar kawancenta India za su bunkasa kasuwancinsu. Ziyarar ta shugaban kasar Rasha a Indiya, tana a karkashin taron da kasashen biyu suke yi ne daga lokaci zuwa lokaci wanda wannan shi ne karo na 23 da ya kunshi ayyukan tattalin arziki, siyasa da al’adu. A yayin taron, kasashen biyu sun cimma matsayar bunkasa girman kasuwancinsu da zai kai dalar Amurka biliyan 100 daga nan zuwa 2030. A nashi gefen Fira ministan kasar India, Modi ya ce, duk da fadi tashin daake samu,amma alakar kasashen biyu India da Rasha tana nan daram. Taron na kasashen biyu dai ya damu Amurka tana mai...
Babban magatakardar kungiyar Hizbullah Sheikh Na’im Kassim wanda ya gabatar da jawabi a jiya Juma’a da marece ya yi suka akan yadda aka shigar da farar hula dan kasar Lebanon a cikin kwamitin dake sa ido akan tsagaita wutar yaki da Haramtacciyar kasar Isra’ila, yana mai bayyana hakan da cewa; ya sabawa dukkanin bayanan da su ka rika fitowa a hukumance na fada ganin an daina kawo wa Lebanon hari sannan ayi hakan. Jawabin na Sheikh Na’im ya yi shi ne adaidai lokacin da ake tunawa da kuma girmama malaman addini da su ka yi shahada, yana mai cewa abinda aka yi na tura wakilin Lebanon farar hula a cikin wannan kwamitin tsagaita wutar, tamkar bai wa Isra’ila kyauta ne...
Gwamnatin Iraki Ta Kore Saninta Da Shigar Da Sunayen Hizbullah Da “Ansarullah” A Cikin Na ‘Yan Ta’adda
Fadar gwamnatin kasar Iraki ta sanar da cewa ba ta masaniya akan yadda aka shigar da sunayen Ansarullah na Yemen da kuma Hizbullah ta kasar Lebanon a cikin jerin sunayen kungiyoyin ‘Yan ta’adda da aka rike kudadensu dake bankunan kasar. Bayanin fadar gwamnatin kasar ta Iraki ya kuma kara da cewa; Matakai irin wadannan da ake dauka a kasar ba a aike wa da su zuwa fadar shugaban kasa,abinda ake aikewa fadar shi ne dokokin da majalisar dokokin kasar ta yi, domin a sake tantancewa da kuma amincewa.” Haka nan kuma sanarwar ta ce; wasu daga cikin abubuwan da ake aikewa fadar mulkin kasar sun hada da tsare-tsaren fadar shugaban kasa,amma abinda ya shafi matakan majalisar ministoci, da na kwamitin...
Daga Usman Muhammad Zaria Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ya yaba da gagarumin cigaba a harkar noma da Gwamna Umar Namadi ya samar cikin shekaru biyu kacal na mulkinsa. Ya bayyana haka ne a masarautar Gumel cikin Jihar Jigawa, yayin kaddamar da sabon masallacin Juma’a da Gidauniyar Kashim Shettima ta gina a matsayin wani ɓangare na bikin zagayowar cikar Sarkin Gumel shekaru 45 a kan karaga. A cewarsa, abin sha’awa ne yadda Gwamna Umar Namadi ya mayar da harkar noma a jihar Jigawa zuwa ta zamani cikin shekaru biyu kacal. Ya jinjina wa Gwamnan da al’ummar Jihar Jigawa bisa wannan ci gaba mai armashi. Kashim Shettima ya kara taya Sarkin Gumel, Alhaji Muhammadu Sani, murnar cika shekaru 45...
Shugaba Bola Ahmad tinubu na tarayyar Najeriya ya nada wasu karin jakadu 65 wadanda suka hada da sanatoci masu ci da kuma tsoffin gwamnoni har’ila yau da kwararrun jakadu. Jaridar Premium times ta Najeriya ta bayyana cewa shugaban ya aikawa majalisar dokokin kasar wasika dangane da hakan, wasika wacce shugaba majalisar dattawa Godswill Akpabio ya karanta a gaban sanatoci a jiya Alhamis. Kafin haka shugaban ya gabatar da sunayen wasu yan siyasa 3 don nadasu jakadu. A cikin wasikar shugaban yace mutane 34 daga cikinsu kwararrun jakadune, sannan sauran 31 yan siyasa ne. Daga cikin wadanda shugaba yanada har da tsohon shugaban hukumar zabena kasar (INEC) Farfesa Mahmood Yakubu) sauran sun hada tsoffin gwamnonin jihohin. Enugu, Abia, tsohon mataimakin gwamnan...
Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnatin Jihar Jigawa ta gudanar da bikin bude tayin bada kwangilar samar da wutar lantarki a wasu garuruwa dake kananan hukumomin Jihar. A lokacin da yake jawabi a yayin gudanar da bikin daya gudana a sakatariyar Jihar dake Dutse, Shugaban hukumar, Injiniya Zubairu Musa ya bayyana cewar tayin bada kwangilar samar da wutar da gyara da fadadawa gami da kammala wasu ayyukan za a yi sune a garuruwa 17. Kazalika, Injiniya Zubairu Musa, yace wannan na daga cikin kudirori 12 na Gwamna Umar Namadi na hada wutar lantarki a kanana da matsakaitan garuruwan jihar da basu da wuta. A cewar sa, garuruwan da za’a samar da wutar lantarkin a Dutse sun hada da Sabuwar Takur...
Rundunar ’yan sandan jihar Borno ta kama matashin nan da ake zargi da kashe makwabciyarsa a unguwar Shuwari II, a garin Maiduguri babban birnin jihar, ta hanyar daba mata wuka. Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, ASP Nahum Kenneth Daso, ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:00 na dare a ranar Talata. Amurka za ta hana ’yan Najeriyar da ake zargi da yi wa Kiristoci kisan kiyashi biza Jirgin fadar shugaban ƙasa ya ƙi sayuwa wata 5 bayan saka shi a kasuwa Ya ce ana zargin matashin ne mai shekaru 17 da aka fi sani da Amir, wanda makanike ne da kashe matar ta hanyar daba mata wuka. Wani makwabcin wajen ya shaida cewa ana zargin matashin ne...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Masu iya magana kan ce banza ba ta kai zomo kasuwa. In ba haka ba, me ya kai matasan da ake zargi da aikata manyan laifuffuka ofishin ’yan sanda, suka kuma fit oba tare da wani ya harae su ko ya yi mutsu tsawa ba, balle ya saka su a cell? ’Yan sandan dai sun ce wannan wata dabara ce ta yakar aikata manyan laifuka irin su sata da fashi da makami da kwacen waya da fyade kai har ma da satar mutane don kudin fansa a tsakanin matasa. NAJERIYA A YAU: Matsalar Kansar Mama Da Hanyoyin Magance Ta DAGA LARABA: Kalubalen Dake Gaban Janar Christopher Musa A Matsayin Ministan Tsaro Ko yaya...
Dan wasan taekwando na kasar iran Abolfazl zandi ya samu lambar yazo ta zinariya a ranar farko ta gasar takwando ta duniya da ake gudanarwa a birnin Nairobi na kasar kenya , kuma ita ce lambar yabonsa na biyu a cikin kwanaki 35, Gasar tana gudana ne a filin wasa na moi international sport center dake kasar kenya kimanin yan wasa 452 da suka fito daga kasashen duniya 75 ne ke halartar gasar, kuma iran ta shiga gasar da yan wasa guda 16 da suka hada da mata 6 da kuma maza 8 da za su yi tasu karawar acikin kwanaki 4. Zandi da ya samu lambar yabo ta zinairiya a baya –bayan nan ya nuna gwaninta da ya cancanci...
Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya), ya ce ba zai bai wa ’yan Najeriya kunya ba, saboda ƙwarin guiwar da suke da shi a kansa. Musa, wanda Shugaba Bola Tinubu ya naɗa ministan tsaro, ya bayyana haka ne a ranar Laraba lokacin da aka tantance shi a Majalisar Dattawa. Tsaro: Gwamnonin Arewa na shirin dakatar da haƙar ma’adinai Ƙudirin dokar hukuncin kisa ga masu satar mutane ya tsallake karatu na biyu Ya gode wa Shugaban Ƙasa saboda zaɓarsa da ya yi a matsayin minista, sannan ya gode wa ’yan Najeriya saboda amincewa da suka yi da shi. Ya yi alƙawarin yin iya bakin ƙoƙarinsa domin tabbatar da zaman lafiya a ƙasar nan. Ya ce: “Da na ga irin martanin...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Yobe, ta ce ta samu rahoton laifuka 25 na cin zarafin mata da ƙananan yara a Ƙananan Hukumomin Jakusko, Fika, Potiskum da Tarmuwa, inda aka kama mutum 28 da ake zargi da aikata laifukan. Kakakin rundunar, SP Abdulkarim Dungus, ya ce an kama masu laifin ne cikin watanni uku da suka wuce, a wani yunƙuri na daƙile cin zarafin mata da yara a faɗin jihar. Tinubu ya san dalilin da ya sa na yi murabus daga muƙamin ministan — Badaru Ƙudirin dokar hukuncin kisa ga masu satar mutane ya tsallake karatu na biyu Daga cikin waɗanda aka kama akwai wani matashi mai shekara 23, Yusuf Garba, da ake zargi yi wa wata yarinya mai shekaru biyar...
Daga Bello Wakili Shugaba Bola Tinubu ya rantsar da Shugaban Hukumar Kidaya ta Kasa (NPC) da kwamishinoni biyu na hukumar, tare da sabbin manyan sakatarori guda biyar da aka nada a gwamnatin tarayya. Daga nan ya jagoranci taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) a fadar shugaban kasa da ke Abuja. Bayan karanta takardar tarihin rayuwarsu, manyan sakatarorin biyar Abdulkarim Ibrahim, Dr John Ezeamama, Dr Abdul-Sule Garba, Dr Isiaku Mohammed da Dr Ukaire Chigbowu, sun dauki rantsuwar kama aiki, sannan suka sanya hannu a kundin rantsuwa. An kuma rantsar da Dr Aminu Yusuf, wanda shugaban kasa ya nada a matsayin Shugaban NPC a ranar 9 ga Oktoba, da kwamishinoni biyu ciki har da Dr Tonga Betara daga Jihar. NPC ita ce...
Daga Ali Muhammad Rabi’u An samu mummunan rikici tsakanin mambobin ƙungiyoyin asiri wanda ya shafi tsofaffin daliban kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kwara da ke Ilorin, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum ɗaya. Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa dalibin mai suna Oyelade Olawale wanda ya karanci aikin Injiniya a fannin Gine-gine, ya rasu ne a yayin wannan rikici na kungiyoyin asiri. An samu labarin cewa an kama wasu daga cikin wadanda ake zargi da hannu a tarzomar da ta faru a Kwalejin. A cikin wata sanarwa, Jami’ar Hulɗa da Jama’a ta Kwalejin, Halima Garba, ta tabbatar da mutuwar matashin da kuma kama wasu mutane da ake zargi da hannu a rikicin. Sanarwar ta yi kira ga dalibai da al’umma...
Majalisar Dattawan Najeriya za ta tantance wanda Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa a matsayin Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa, a zamanta na yau Laraba. Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga ofishin Shugaban Masu Rinjaye na majalisar, Opeyemi Bamidele. Mako mai Majalisa za ta kada ƙuri’a kan ƙudurin ƙirƙirar sabbin jihohi DAGA LARABA: Kalubalen Dake Gaban Janar Christopher Musa A Matsayin Ministan Tsaro Sanarwar ta ce majalisar ta karɓi buƙatar Shugaban Ƙasa Tinubu na tabbatar da wanda aka naɗa Ministan Tsaro. Sanarwar ta ƙara da cewa za a karanta wasikar a gaban majalisar a ranar Laraba, sannan kuma za a ci gaba da tantance wanda aka naɗa nan take. Opeyemi ya bayyana cewa majalisar ba za...
Daga Bello Wakili Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada Janar Christopher Gwabin Musa a matsayin sabon Ministan Tsaro. A wata wasika da ya aike wa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, Shugaba Tinubu ya mika sunan Janar Musa domin ya maye gurbin Alhaji Mohammed Badaru Abubakar, wanda ya yi murabus a ranar Litinin. Janar Musa, mai shekaru 58, wanda zai cika 59 a ranar 25 ga Disamba, jajirtaccen soja ne da ya jagoranci rundunonin tsaro a matsayin Shugaban Hafsoshin Tsaro daga 2023 zuwa watan Oktoban 2025. An haifi Janar Musa a Sakkwato a 1967, inda ya yi makarantar firamare da sakandare kafin ya tafi College of Advanced Studies a Zariya. Ya kammala a 1986 sannan ya shiga Kwalejin Horas da...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Cutar kansar mama na ɗaya daga cikin manyan cututtukan da ke addabar mata a Najeriya da ma duniya baki ɗaya. An kiyasta cewa mata sama da dubu ɗari biyu na kamuwa da cutar a kowace shekara a Najeriya, yayin da miliyoyin mata a duniya ke fama da wannan cuta. Abin damuwa shi ne cewa yawancin lokuta ana gano cutar ne a kurarren lokaci, wanda hakan ke sa magani ya yi wahala kuma ya rage yiwuwar ceto rayuwar wanda ya kamu da shi. NAJERIYA A YAU: Halayen Da Ambasadoji Ya Kamata Su Mallaka Kafin Tura Su Wasu Kasashe DAGA LARABA: Shin Ya Kamata A Biya Kudin Fansa Ga Masu Garkuwa Da Mutane? Wannan...
Jagoran ‘Yan Jam’iyyar Democrat na Majalisar Dattawa Chuck Schumer ya zargi Shugaban Amurka Donald Trump da shirya yaƙi a ɓoye a kan kasar Venezuela, yana mai jaddada cewa ikon ayyana yaƙi ya rataya ne kawai a kan Majalisa, kuma dan majalisar ya bayyana cewa zai gabatar da kuduri don hana tura sojojin Amurka yaki a Venezuela. Schumer ya tabbatar da cewa Trump ba shi da ikon aika sojojin Amurka zuwa yaƙi ba tare da izinin Majalisa ba, yana mai bayyana cewa wannan ikon an keɓe shi ne ga Majalisa kaɗai. A cikin wata sanarwa, Schumer ya zargi Trump da shirin yaƙi a ɓoye da Venezuela, yana mai gargadin cewa Majalisa za ta ɗauki mataki nan take don gabatar da kuduri...
Daga Bello Wakili Ministan tsaron Najeriya, Alhaji Mohammed Badaru Abubakar, ya yi murabus daga mukaminsa nan take. Sanarwar da mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan yada labarai Bayo Onanuga ya fitar, ta ce wasikar da Badaru ya aika wa Shugaba Bola Tinubu mai dauke da kwanan watan 1 ga watan Disambar 2025, ta yi bayanin cewa, ya ajiye aikin ne saboda dalilan lafiya. Sanarwar ta ce Shugaba Tinubu ya amince da murabus ɗin tare da gode wa Badaru Abubakar bisa irin gudummawar da ya bai wa ƙasa. Ana sa ran Shugaba Tinubu zai sanar da Majalisar Dattawa sunan wanda zai maye gurbin Badaru nan da ƙarshen wannan makon. Badaru Abubakar, mai shekara 63, ya taɓa zama gwamnan jihar Jigawa har...
Daga Bello Wakili Ministan tsaron Najeriya, Alhaji Mohammed Badaru Abubakar, ya yi murabus daga mukaminsa nan take. Sanarwar da mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan yada labarai Bayo Onanuga ya fitar, ta ce wasikar da Badaru ya aika wa Shugaba Bola Tinubu mai dauke da kwanan watan 1 ga watan Disambar 2025, ta yi bayanin cewa, ya ajiye aikin ne saboda dalilan lafiya. Sanarwar ta ce Shugaba Tinubu ya amince da murabus ɗin tare da gode wa Badaru Abubakar bisa irin gudummawar da ya bai wa ƙasa. Ana sa ran Shugaba Tinubu zai sanar da Majalisar Dattawa sunan wanda zai maye gurbin Badaru nan da ƙarshen wannan makon. Badaru Abubakar, mai shekara 63, ya taɓa zama gwamnan jihar Jigawa har...
Paparoma Leo 14 wanda yake ziyarar aiki na kwanaki uku a kasar Lebanon ya gana da shugaban kasar Lebanon Josept Aun da kuma manya-manyan malamai da shuwagabannin kungiyoyin yan siyasa a kasar Lebanon. A jawabin da ya gabatar a gaban wadannan shuwagabannin kasar Lebanon Lio na 14 ya bukaci, su rungumi zaman tare da kuma hakuri wajen hada kai da kuma gina kasar Lebanon. Lio 14 ya ce mutanen kasar Lebanon sun sha wahala a tarihin kasar na zama, amma saboda gwazon da suke da shi wannan bai hana su zaman lafiya da juna ba. Wannan bai hanasu ci gaba da rayuwa ba. Duk da cewa akwai barazana mai yawa da ke fuskantar kasar. Yace, zama tare da wadanda kuke...
Anicen Ekane dan adawa na jam’iyyar African Movement for New Independence yana daga cikin fitattun yan siyasa a kasar Kamaru, kuma yana goyon bayan Issa Chiroma a zaben shugaba kasa wanda aka gudanar a kasar a cikin watan Octoban da ya gabata. Issa Chiroma dai ya shelanta cewa shi ya lashe zaben shugaban kasa wanda aka gudanar a cikin watan Octoban da ya gabata. Jami’an tsaro sun yi dirar mikiya kan masu goyon bayan Chiroma, kuma sun kashe mutane da dama sun kuma kama wasu Anicen Ekaney ana daga cikin wadan da aka kama a birnin Duala a ranar 24 ga watan Octoba. Kuma Ekane ya zargi jami’an tsaro da kwace maganin Oxigen dinsa, wanda ya jefa rayuwarsa cikin hatsari,...
Hukumar kididdiga ta HKI ta basa sanarwan cewa yawan yahudawa da suke ficewa daga haramtacciyar kasar . Tashar talabijin ta Almayadeen na kasar Lebanon ta nakalto hukumar na bada labarin cewa a shekara ta 2010 yawan masana wadanda suke da shahadar Jami’a ya karu ha rya kai kashi 46% sannan wannan adadin ya cilla sama a shekara ta 2023 bayan fara yakin tufanul aksa zuwa kashi 60.4 %. Har’ila yau kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya bayyana cewa a cikin yan shekarun da suka gabata, yahudawa masu ilmin Jami’a da dama sun bar kasar, saboda yana yaki wanda baya karewa a kasar. Hukumar kididdiga na HKI a cikin yan kwanakin da suka gabata ta yada rahoto dangane da...
’Yan sanda sun gano tare da miƙa wa wata mata zinarenta da kuɗinsu ya kai Naira miliyan 23 da suna ɓace a lokacin wani harin Boko Haram shekara 13 da suka gabata a Jihar Borno. Jami’an tsaro da ke sintiri a kan iyakar Jihar Borno da Nijar ne suka gano kayan zinaren da suka ɓace tuna shakarar 2012, waɗanda suka haɗa da sarƙoƙi da sulallan zinariya a yankin Ƙaramar Hukumar Abadam. Jami’an Ƙaramar Hukumar ne suka sanar a ranar Asabar a Malam Fatori cewa tsabar zinaren da aka gano, darajarsu ta kai Naira miliyan 23, mallakin wata uwa ce mai ’ya’ya shida. Matar, wacce ke zaune a gaɓar Tafkin Chadi, ta ce, “A yau ina cike da farin ciki game...
’Yan sanda sun gano tare da miƙa wa wata mata zinarenta da kuɗinwu ta kai Naira miliyan 23 da suna ɓace a lokacin wani harin Boko Haram shekara 12 da suka gabata a Jihar Borno. Jami’an tsaro da ke sintiri a kan iyakar Jihar Borno da Nijar ne suka gano kayan zinaren waɗanda suka haɗa da sarƙoƙi da sulallan zinariya a yankin Ƙaramar Hukumar Abadam. Jami’an Ƙaramar Hukumar ne suka sanar a ranar Asabar a Malam Fatori cewa tsabar zinaren da aka gano, darajarsu ta kai Naira miliyan 23, mallakin wata uwa ce mai ’ya’ya shida. Matar, wacce ke zaune a gaɓar Tafkin Chadi, ta ce, “A yau ina cike da farin ciki game da gano tsabar zinare na masu...
Daga Ali Muhammad Rabi’u ’Yan bindiga kimanin guda huɗu dauke da makamai sun kai hari a garin Eruku da ke ƙaramar hukumar Ekiti a jihar Kwara, inda suka sace wani manomi mai suna Mista Aasaru. Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa wannan hari shi ne na biyu da aka kai wa garin Eruku cikin wata guda, kuma ya faru ne kwanaki kaɗan bayan gwamnatin tarayya ta samu ’yantar da mambobin Cocin Christ Apostolic Church (CAC) 38 da aka yi garkuwa da su a yankin. Majiyar da ta yi magana da Rediyon Najeriya ta ce ’yan bindigar sun farmaki Aasaru ne a wani daji da ke kan hanyar Koro. Jami’ar hulɗa da jama’a ta rundunar ’yan sandan jihar Kwara, Toun Ejire-Adeyemi, ta...
’Yan bindiga sun yi garkuwa da wani fasto da matarsa da mabiyansa a yayin da suke tsaka da ibada a coci da ke a Jihar Kogi. Wani ganau da ke cikin cocin a lokacin da aka kai harin, Adegboyega Ogun, ya ce misalin ƙarfe 9.30 na safe ’yan bindigar suka kai harin suna bude wuta. “Mutane sun qarshe ta ko’ina, har da faston, wanda aka fi sani da Baba Orlando da matarsa da wasu masu ibada duk an yi garkuwa da su. Gaskiya harin ya yi muni, dukkanmu tserewa muka yi daga cocin.” Sace masu ibadar a ranar Lahadi a Cocin Cherubim and Seraphim ya auku ne bayan a kwanan nan Gwamna Usman Ododo, ya koka da cewa wasu manyan...
Ma’aikatar kiwon lafiya ta Falasdinu a Gaza ta sanar da cewa; An sami shahidai 3 da aka kai su asibitin a cikin sa’o’i 24 da su ka gabata. Shi kuwa ofishin gwamnati dake Gaza ya sanar da cewa, daga tsagaita wutar yaki zuwa wannan lokacin, sau 591 Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta keta wutar yaki. Ofishin gwamnatin a yankin Gaza ya yi tir da hare-haren na Haramtacciyar Kasar Isra’ila, tare da yin kira ga kasashen duniya da su yi matsin lamba akan ‘yan mamaya masu keta dokokin kasa da kasa. Kididdiga ta bayyana cewa daga tsagaita wutar yaki a ranar 11 ga watan Oktoba 2025, adadin Falasdinawa da su ka yi shahada sun kai 356,yayin da wadanda su ka jikkata sun...
Hukumar Agaji ta MDD ta sanar da cewa, kasar Somaliya ta shiga cikin wani mawuyacin yanaki saboda fari, da yanki mai yawa na kasar ya bushe bayan da aka dauki shekaru hudu a jere babu ruwan sama. Hukumar ta MDD ta kuma ce, da akwai miliyoyin mutanen kasar da suke fuskantar yunwa mai tsanani, yayin da wasu kuma suke ficewa daga garuruwan nasu. A can kasar ta Somalia, gwamnati ta shelanta shiga ” halin- ko- ta- kwana’ saboda farin, tare da yin kira ga kungiyoyin kasa da kasa da su kai dauki na gaggawa,musamman a yankunan Arewa da Kudancin kasa da kuma tsakiya.” Yankin Portland ne ya fi cutuwa daga fari, inda gwamantin Somaliya ta yi kiyasin cewa da akwai...
’Yan bindiga sun shiga garin Chaco da ke Ƙaramar Hukumar Wurno a Jihar Sakkwato, inda suka sace amarya da ƙawayenta guda 14. Yayin da mutane ke tsaka shagalin bikin auren, sai ’yan bindigar suka afka musu tare da tarwatsa komai. Mutum 6 sun jikkata a rikici manoma da makiyaya a Jigawa Sojoji sun ceto mutum 7 da ’yan bindiga suka sace a Kano Sun shigo garin a ƙafa, inda suka wuce kai-tsaye zuwa gidansu amaryar ba tare da sun taɓa kowa ba. Wani daga cikin iyayen ƙawayen amaryar ya shaida wa Aminiya cewa ba a tantance adadin waɗanda aka sace ba, amma wasu na cewa 15 ne, wasu kuma na cewa 13, amma amaryar da ’yarsa na cikin waɗanda aka...
’Yan bindiga sun harbe wata tsohuwa har lahira a wani sabon hari da suka kai ƙauyen Yankamaye da ke Ƙaramar Hukumar Tsanyawa a Jihar Kano. Sun kai harin ne a daren ranar Asabar, a lokacin da mutanen ƙauyen ke kwance. Likitoci sun gindaya sabon sharaɗi bayan janye yajin aiki Tinubu ya sake aike wa majalisa ƙarin sunayen jakadu 32 Yayin kai harin, ’yan bindigar sun kuma sace aƙalla mutum uku. Yankamaye, wani ƙaramin ƙauyen manoma ne, ’yan bindiga da ke tserewa daga maƙwabtan jihohin Kano ne suka fara kai musu hare-hare. Kakakin rundunar ’yan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an tura jami’ai domin bin diddigin maharan. Mazauna ƙauyen sun ce ’yan...
Rahotanni sun bayyana cewa shugaban kasar najeriya Bola Ahmad tunubu ya mika sunayen mutane 32 ciki har da tsohon shugaban hukumar zabe ta kasa mahamud yakubu da tsohon ministan sufurin jiragen sama femi kayode ga majalisar dokokin kasar domin a tantancesu kwanaki bayan tura sunayen mutane 3 a fara da su. Mai magana da yawun shugaban kasar bayo Onanuga shi ne ya fitar da sanarwa, a cikin wasu wasiku ma banbanta da shugaban kasar ya turawa shugaban majalisa Godswill Akpabiyo ya bukaci majalisar ta amince da sunaye 15 a matsayin jakadun aiki da kuma wasu 17 da bana aiki ba, Akwai mata guda 4 daga cikin sunayen a matsayin jakadu na aiki da kuma wasu guda 6 a matsayin jakadu...
Antonio Guterres babban sakataren majalisar dinkin duniya yayi kira da a kawo karshen mamayar yankunan falasdinawa da isra’ila ke yi da ya sabama doka, kuma yace babu ja da baya game da kudurin kafa kasashe biyu masu cin gashin kai Sakataren ya sake yin kira ne saboda ya nuna irin bukatar da ake da ita wajen kare hakkin falasdinawa da kuma matsa kaimi wajen warware rikicin ta hanyar siyasa, adaidai lokacin da Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare a yankin Gaza da labanon da kuma kasar siriya, Wannan bayanin yana zuwa ne adaidai lokacin da zaman dar-dar da cin zarafin dan adam ke kara Kamari a yankin Gaza da kuma gabar yammacin kogin Jodan, inda hankalin duniya ya tashi...
Gwamnatin kasar Iran ta bada sanarwan cewa ta kakkabo jiragen yakin HKI fiye da 196 a cikin yakin kwanaki 12 da aka dora mata a cikin watan Yunin da ya gabata. Daga ciki har da jiragen yaki samfurin Heron da Hermes -900 wadanda ke aiki da kayakin zamani. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto wata tashar talabijin ta cikin gida tana fadar haka a yau Asabar ta kuma kara da cewa Sashen garkuwar sararin samaniya na sojojin sama sun nuna hutunan lokacin da suke kakkabo jiragen yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa na HKI a lokacinda suka shigo sararin samaniyar kasar kafin su kai ga bararsu. Burgediya Janar Reza Khajeh mataimakin kwamandan garkuwar sararin samaniya na sojojin...
Ma’aikatar Harkokin Wajen Lebanon ta sanar a ranar Juma’a cewa ta shigar da kara a kan Isra’ila gaban kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya dangane da gina katanga biyu na siminti a cikin yankin Lebanon da ke kudu da garin Yaroun (yankin Bint Jbeil). A cikin wata sanarwa da ta fitar, Ma’aikatar ta ce tawagar Jakadancin Lebanon ta Dindindin a Majalisar Dinkin Duniya da ke New York ne ta shigar da ƙarar gaban membobi 15 na kwamitiin Tsaron. Labanon ta yi kira ga kwamitin Tsaro da Sakatariyar Majalisar Dinkin Duniya da su ɗauki matakan gaggawa don hana Isra’ila keta hurumin Lebanon. A cewar ƙarar, keta hurumin ya kunshi gina katanga biyu da Isra’ila ta yi a kudu maso yamma da kudu...
A baya, samun fara da yawa a shekara abin tsoro ne ga kowa, dalilin ɗab’arta ta lalata amfanin gona, sai dai a yanzu ta zamo hanyar samun abincin mutanen da dama, musamman ma mata a Jihar Kano. Duk da cewa a baya ma akwai tsirarun mutane da ke cin fara dace kuma halaccin cin ta a Musulunce, masu ƙyamar ta sun fi yawa, har ma wasu ke ganin masu cin ta za su iya cin kyankyaso. Sai dai a yanzu wannan ɗabi’a ta kusa zama tarihi, saboda fara ta zamo abincin taɓaka-lashe ba ga mata kaɗai ba da aka saba gani a baya, har ma da maza da masu kuɗi, inda ake mata mazubi na musamman da tsarabe-tsarabe, har...
A baya, samun fara da yawa a shekara abin tsoro ne ga kowa, dalilin ɗab’arta ta lalata amfanin gona, sai dai a yanzu ta zamo hanyar samun abincin mutanen da dama, musamman ma mata a Jihar Kano. Duk da cewa a baya ma akwai tsirarun mutane da ke cin fara dace kuma halaccin cin ta a Musulunce, masu ƙyamar ta sun fi yawa, har ma wasu ke ganin masu cin ta za su iya cin kyankyaso. Sai dai a yanzu wannan ɗabi’a ta kusa zama tarihi, saboda fara ta zamo abincin taɓaka-lashe ba ga mata kaɗai ba da aka saba gani a baya, har ma da maza da masu kuɗi, inda ake mata mazubi na musamman da tsarabe-tsarabe, har...
Shaikh Naim Qasim babban sakatare janar din kungiyar hizbullah ta kasar labanon ya bayyana cewa kisan babban kwamanda Haitham Ali tabataba’I da isra’ila ta yi bai zai sa ta cimma manufofinta ba, don haka hizbulla za ta mayar da martani a lokacin da ya dace, Wadanan kalaman suna zuwa ne a lokacin da ake zaman dar-dar tun bayan kisan gillan da isra’ila ta yi wa babban kwamandan hizbulla , kuma wani mataki ne kamar yadda shaikh naim Qasem ya bayyana ta yi kisan ne don karya bangaren soji na kungiyar sai dai hakarta ba za ta cimma ruwa ba, Babban sakataren ya bayyana jin dadinsa game da sakonnin ta’azziya da aka aiko daga bangarorin shuwagabannin jam’iyun siyasa a ciki da...
Rundunar “Sarayal-Quds” ta kungiyar Jihadul-Islami ta sanar da shahadar mayakanta biyu a yammacin kogin Jordan sanadiyyar harin da sojojin mamaya na Haramtacciyar Kasar Isra’ila su ka kai. Daya daga cikin shahidan shi ne Yusuf Ali Asa-Asa, dan shekaru 37, da kuma Mahmud Abdullah dan shekaru 26, sun kuma yi shahadar ne a jiya Alhamis. Sanarwar ta kuma ce,an yi batakashi a tsakanin shahidan biyu da kuma ‘yan mamaya gabanin su kwanta dama a unguwar Abu Dhahir dake Jenin a yammacin Kogin Jordan. Wasu rahotanni daga yankin da lamarin ya faru sun ce, sojojin Haramtacciyar kasar Isra’ila sun kutsa cikin unguwar tare da shiga cikin wani gidan sannan kuma su ka kama wani saurayi Bapalasdine daya. Gabanin su yi awon gaba...
Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bayar da umarnin a fara tsara yadda za a shigar da kungiyar “Muslim Brotherhood” a cikin jerin kungiyoyin ta’addanci na waje. Kungiyar ta ce, babu wani dalili da Amurkan za ta iya samu da zai tabbatar mata da cewa kungiyar tana ayyukan ta’addanci. Haka nan kuma kungiyar ta ce, abinda Amurkan take yi, ba komai ba ne sai kokarin yin matsin lamba akan kungiyar. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kasashen Qatar Da Jordan Sun Yi Allawadai...
Jagoran juyin musulunci na kar iran Ayatullah sayyid Ali Khamna’i ya bayyana cewa kasar Amurka bata ji da dadi ba a yakin kwanaki 12 da ta kaddamar a kan kasar iran a watan yuni, duk da amafani da ta yi da manyan makaman yaki na zamani da suka hada da jiragen yaki da kuma makaman kariya . Har ila yau jagoran yace Amurka da isra’ila sun sha kashi a yakin kwanaki 12 da suka kaddamar kan kasar iran, sun kai harin ne don su ci blus, sai suka koma da borin kunya, basu iya tabuka komai ba, wannan babban shan kashi ne a garesu, Yace wasu rahotanni sun nuna cewa gwamnatin sahyuniya ta shirya yakin shekaru 20, ta shirya tunzura...
Gammayar ministocin harokin wajen kungiyar tarayyar Turai sun fitar da wata sanarwa da aciki suka soki hare haren da yahudawa yan share wuri zauna suke kai wa falasdinawa a gabar yammacin kogin Jodan da isra’ila ta mamaye kuma yake kara ci gaba fiye da kowanne lokaci a baya, Sanarwar ta fito ne daga minsitocin kasashen birtaniya, jamus , faransa da kuma italiya inda manyan jami’an diplomsiyarsu suka bayyana hare-haren a matsayin mataki ne na tada fitina da kuma ta’addanci. Haka zalika sun yi kira ga fira ministan isra’ila Benjamin na tanyaho da yayi aiki da nauyin da ya rataya a wuyansa karakshin dokokin kasa da kasa, kuma ya kiyaye hakkin falasdinwa dake zaune a bangarorin da aka mamaye. Daga karshe...
Sanatan Borno ta Kudu, Ali Ndume, ya ce Najeriya na iya ajiye biliyoyin naira a duk shekara idan aka rungumi tsarin majalisa ta wucin gadi. Yayin da yake magana a gidan talabijin na Channels ranar Alhamis, Ndume ya ce kuɗin da ake kashewa wajen kula da Majalisar Dokoki a tsarin zama kodayaushe ba zai dore ba, musamman a wannan lokaci da ƙasar ke fama da matsalolin kuɗi da tsaro. An janye ’yan sanda 11,566 daga yi wa manyan mutane rakiya – Egbetokun An gano gawawwakin mata uku ’yan Kamaru da aka sace a Anambra “Kudin gudanar da gwamnati ya yi yawa sosai. Idan ’yan majalisa suka zauna na wucin gadi, gwamnati za ta ajiye biliyoyi,” in ji shi. Ya ce...
Ministan yakin Isra’ila ya yi barazanar kai wa kasar Lebanon hari gadan-gadan, inda ya bukaci kungiyar Hizbullah ta kwace damarar makamai. Ministan yakin Isra’ila, Isra’ila Katz, ya yi gargadin cewa Tel Aviv a shirye take ta kaddamar da wani sabon yaki kan kasar Labanon matukar kungiyar gwagwarmayar Hizbullah ta ki mika makamanta zuwa karshen shekarar 2025. Da yake jawabi ga Knesset na Isra’ila, Katz ya yi ikirarin cewa Washington ta ba Beirut wa’adin kwance damarar Hezbollah zuwa karshen shekara, amma ya ce ba ya tsammanin kungiyar za ta mika makamanta. “Ban yi imani cewa Hizbullah za ta mika makamanta bisa radin kanta ba,” kamar yadda ya shaida wa ‘yan majalisar. “Idan Hezbollah ba ta yi watsi da makamanta a karshen...
Daga Sani Sulaiman Gwamnan Jihar Taraba, Dr. Agbu Kefas, ya yi jimami kan rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, wanda ya rasu a ranar Alhamis 27 ga watan Nuwamban 2025, yana da shekaru 102. Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai bai wa gwamnan shawara na musamman kan Yada Labarai da Hulda da Jama’a, Mista Emmanuel Bello, ya sanyawa hannu. Gwamnan ya ce rasuwar wannan babban malami babban rashi ne ga kasa, yana mai nuna cewa a wannan lokaci ne ake matuƙar bukatar irin gudummawar da yake bayarwa, duba da kalubalen da kasar ke fusfuskanta. Ya kara da cewa marigayi Sheikh ya koyar da ilimi da zai ci gaba da jagorantar kasa kan...
Daya daga cikin ‘ya’yan babban malamin addinin musulunci a Najeriya Sayyid Ali Dhahiru Usman Bauchi ne ya tabbatar wa da jaridar “Daily Trust” rasuwar malamin. Sayyadi Ali ya furta cewa: ” Tabbas Shehi ya koma ga mahaliccinsa, mu duka daga Allah muke, kuma zuwa gare shi za mu koma.” Haka nan kuma ya kara da cewa, Lokaci ya yi da shehun malamin zai huta,kuma mun gode wa Allah da ya yi mana komai, ya tsawaita rayuwar shehi har zuwa wannan lokacin. Shi dai Shehu Dhariu Usman Bauchi an haife shi ne a 29 ga watan Yuni na 1927, ya kuma rasu yana dan shekaru 97 a wannan Alhamis din 27/ ga watan Nuwamba 2025. Gabanin rasuwarsa ya kasance daya daga...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, ta gano harsasai 210 da aka jefar a kan babbar hanyar Zariya zuwa Funtuwa, a unguwar Dogo Itace da ke Samaru, Zariya. Lamarin ya faru ne lokacin da DPO na Samaru tare da tawagarsa suke sintiri a kan hanyar. Allah Ya yi wa Sheikh Dahiru Bauchi rasuwa Juyin mulki ya rutsa da Jonathan a Guinea-Bissau Jama’ar yankin ne suka kira rundunar cewar fasinjojin wata mota ƙirar Volkswagen Golf mai launin baƙi sun jefar da wata jaka, sannan suka tsere. Da jami’an rundunar suka isa, sun tarar da jakar da aka jefar. Bayan gudanar da bincike, sun gano harsasai 210 na ɗangon 7.56mm. DPO ɗin yankin ya sanar da sauran jami’an rundunar da ke kan hanyar...
Fitaccen malamin addinin Musulunci nan daga Jihar Bauchi, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya rasu. Ɗansa, Sayyadi Ali Dahiru Usman Bauchi ne, ya tabbatar wa Aminiya rasuwar malamin. Juyin mulki ya rutsa da Jonathan a Guinea-Bissau Ɗan bindiga ya harbe sojoji 2 a fadar shugaban Amurka Ya ce sun karɓi wannan ƙaddara tare da gode wa Allah bisa rayuwar da malamin ya yi. “Tabbas Sheikh ya koma ga Mahaliccinsa. Daga Allah muke, kuma gare Shi za mu koma,” in ji Sayyadi. “Lokacin Sheikh ya yi. Mun gode wa Allah Maɗaukaki. Ya bai wa Sheikh tsawon rai, kuma rayuwarsa ta yi kyau. Alhamdulillah,” in ji shi. Sayyadi, ya ce zuwa yanzu ba su yanke inda za a yi jana’izar malamin ba.
Ma’aikatar Ma’adinai da wutan lantarki a yankin Kurdistan na kasar Iraki ta bada sanarwan cewa an dakatar da tura iskar gas zuwa cibiyoyin samar da wutan lantarki a yankin saboda hare-haren da aka kai kan wata cibiyar hakar iskar gas a yankin. Tashar talabijan ta Almayadeentv ta kasar Lebanon ta bayyana cewa wani jirgin yaki wanda ake sarrafashi daga nesa ne ya fada kan cibiyar hakar iskar gas ta Kurmur, ta kuma jawo dakatar da tura iskar gas din. Labarin ya kara da cewa jirgin ya fada kan cibiyar hakar iskar gas ta kurmur a bangaren Chemchel na lardin Sulaimaniyya ne, ya kuma haddasa barna mai yawa, wanda mai yuwa har da rasa rai ko rayuka. A halin yanzu dai...
Daga Isma’il Adamu Gwamna Dikko Radda na Jihar Katsina ya sanya hannu kan kudirin kasafin kudin jihar na 2026 na Naira Biliyan 897, makonni uku bayan gabatar da shi a gaban majalisar dokokin jihar. Yayin rattaba hannu a Fadar Gwamnati da ke Katsina, a gaban ‘yan majalisar dokokin jihar, gwamnan ya jinjinawa majalisar bisa gaggawar amincewa da kasafin, tare da tabbatar da cewa za a aiwatar da shi yadda ya dace. Ya bayyana cewa kashi 82 cikin ɗari na kasafin an ware shi ne ga manyon ayyuka(capital expenditure), yayin da kashi 18 cikin ɗari aka ware ga ayyukan yau da kullum(recurrent expenditure), rabo wanda ya ce ya fi abin da doka ta baya ta tanada, wadda ke bukatar kada kudaden gudanarwa...
Rahotanni sun bayyana cewa kididdigar da ma’aikatar harkokin wajen yankin falasdinu ta fitar ya nuna cewa sojojin Isra’ila sun kashe akalla yan mata 33000 a ci gaba da yakin kare dangi da take yi kan alummar Gaza. Ma’aikatar fa fitar da wannan sanarwar ce a wajen taron ranar kawo karshen hare-hare kan mata ta duniya . kuma tayi kaca-kaca da gwamnatin sahayuniya game da irin muggan laifukan yaki da ta tafka, inda ta rika amfani da makamai na zamani kan alummar falasdinu Kididdigar ta nuna cewa sama da mata 12500 da kuma yara 20,000 ne Isra’ila ta kashe a harin da ta kai tun daga watan oktoban shekara ta 2023. Har ila yau ma’aikatar ta bayyana cewa lallai a kwai...
Jami’an tsaro na kasar Siriya karkashin gwamnatin rikon kwarya ta HKI sun budewa masu zanga zangar lumana wuta a yankunan bakin ruwa na kasar. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa a jiya Talata ce, a garuruwan Tartus, Lazikiyya da lardin Lantakiya mutane suka fito zanga zanga ta lumana inda suke neman adlci ga Alawiyawa da sauran kananan addinin da mazhabobi a yankin. Har’ila yau da sakin wadanda gwamnati take tsare da su. Amma jawabin gwamnatin Jolani ga masu zanga-zangar shi ne aman wutan bindigogi da hayaki mai sa hawaye a kama masu zanga-zangar da dukan wasu daga cikinsu. Labarin ya kara da cewa matsalolin tsaro sun tarbarbare a yankin bakin ruwa na kasar Siriya sosai, tare...
Jami’an tsaro na kasar Siriya karkashin gwamnatin rikon kwarya ta HKI sun budewa masu zanga zangar lumana wuta a yankunan bakin ruwa na kasar. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa a jiya Talata ce, a garuruwan Tartus, Lazikiyya da lardin Lantakiya mutane suka fito zanga zanga ta lumana inda suke neman adlci ga Alawiyawa da sauran kananan addinin da mazhabobi a yankin. Har’ila yau da sakin wadanda gwamnati take tsare da su. Amma jawabin gwamnatin Jolani ga masu zanga-zangar shi ne aman wutan bindigogi da hayaki mai sa hawaye a kama masu zanga-zangar da dukan wasu daga cikinsu. Labarin ya kara da cewa matsalolin tsaro sun tarbarbare a yankin bakin ruwa na kasar Siriya sosai, tare...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A cikin ‘yan shekarun nan, batun garkuwa da mutane ya zama babban kalubale ga tsaro a Najeriya da wasu ƙasashen duniya. Lokacin da mutane suka fada hannun masu garkuwa, iyaye da ‘yan uwa sau da yawa suna fuskantar babban zabi mai wahala: biyan kudin fansa don sakin wanda aka sace ko tsayawa da kafafun tsaro har zuwa samun taimakon hukumomi. Shin ko ya kamata alumma su cigaba da biyan kudin fansa idan an yi garkuwa da ‘yan uwansu? NAJERIYA A YAU: Irin Radadin Da Masu Cutar Amosanin Jini Ke Fuskanta DAGA LARABA: Hanyoyin Da Suka Kamata A Bi Wajen Ceto Daliban Kebbi Da Aka Sace Wannan shine batun da shirin Najriya A Yau...
’Yan bindiga sun yi garkuwa da aƙalla mutum 11 mazauna garin Isapa da ke kusa da Eruku a Ƙaramar Hukumar Ekiti ta Jihar Kwara. Harin ya faru ne sa’o’i kadan bayan sakin wasu masu ibada da aka yi garkuwa da su suna tsaka da ibada a coci. An haramta cin naman Kare da Kyanwa a Indonesia An sako ɗalibai 25 da ’yan bindiga suka sace a Kebbi A cocin CAC da ke Ekuru, ana gudanar da bikin godiya domin murnar ’yantar da mambobi 18 da aka yi garkuwa da su kusan wata guda da ya gabata, sai ’yan bindiga suka kutsa suka yi garkuwa da mutum 38 bayan sun harbe uku har lahira. Sabon harin, wanda ya faru da misalin...
Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya gabatar da kasafin kuɗi na shekarar 2026 na sama da naira biliyan 900 ga Majalisar Dokokin jihar. Yayin gabatar da kasafin da aka lakaba wa suna “Kasafin Kirkire-kirkire da Sauyi Don Cigaban Jigawa II,” Gwamna Namadi ya ce za a ware sama da naira biliyan 693.4, wanda ya kai kimanin kashi 76 cikin 100, don ayyukan raya kasa. Gwamnan ya kuma ce sama da naira biliyan 208 za su tafi ne ga ayyukan yau da kullum. A cewarsa, an ware sama da naira biliyan 310 ga bangaren ilimi da lafiya, yayin da kimanin naira biliyan 186 za su tafi ga hanyoyi da sufuri. Malam Umar Namadi ya ƙara...
’Yan Majalisar Tarayya daga yankin Kudu sun yi kira ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya yi wa jagoran ƙungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, afuwa bayan da kotu ta yanke masa hukuncin ɗaurin rai da rai. Kungiyar ’Yan Majalisar Wakilai daga yankin Kudu maso Gabas ta yi kira ga Shugaba Tinubu da ya yi amfani da ikon da kundin tsarin mulki ya ba shi, wajen yi wa Nnamdi Kanu afuwa wanda kotu ta same shi da laifin ta’addanci. Alƙali James Omotosho na Babban Kotun Tarayya da ke Abuja ne ya yanke hukuncin, inda ya same shi da laifi a kan tuhumar da ake masa guda bakwai, sannan ya yanke masa hukuncin daurin rai da rai. Tuni aka tura Nnamdi Kanu...
Rahotanni na cewa ’yan bindiga sun sace wasu mutum takwas a garin Biresawa da ke Karamar Hukumar Tsanyawa ta Jihar Kano a daren jiya na Litinin. Wata majiyar da ta tabbatar da lamarin ta shaida wa Aminiya cewa maharan sun shiga garin tsakanin 11 na dare zuwa 12 na tsakar dare, inda suka yi awon gaba da maza biyu da mata shida. ’Yan bindiga sun yi yi garkuwa da mutane 11 a Kwara Chelsea za ta kece raini da Barcelona a Gasar Zakarun Turai Wani ɗan uwa ga waɗanda aka sace, Kabiru Usman, ya ce maharan sun zo ne a ƙafa ɗauke da makamai, suka kuma yi garkuwa da matarsa Umma, ɗiyarsa mai shekara 17, da matar ɗan’uwansa da wasu...
’Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane 11, ciki har da wat mai juna biyu da ƙananan yara Jihar Kwara. Maharan sun kai farmaki tare da sace mutanen ne a yankin Eruku da ke Ƙaramar Hukumar Ekiti da ke jihar. Ƙarin bayani na tafe…
A jiya Litinin ne dai mahukuntan kasar ta China su ka yi Allawadai da yadda kasar Japan din ta girke makamai masu linzami a wani tsibirinta da yake kusa da yankin Taiwan, tare da bayyana hakan a matsayin kokarin tayar da hargitsi a cikin yankin. Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar China Máo Níng ta bayyana cewa: Daukar mataki irin wannan, wanda kuma ya zo bayan furucin Fira Ministar kasar ta Japan Sanae Takaichi,wani yanayi ne mai hatsarin gaske wanda yake da bukatuwa da kasashen yankin su kasance a cikin fadaka, haka nan kuma kungiyoyin kasa da kasa. Shi kuwa ministan tsaron kasar Japan ya bayyana cewa; Girke makamai masu linzami da kasarsa ta yi a tsibirin Yonagoni...
’Yan Majalisar Wakilai daga yankin Kudu sun yi kira ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya yi wa jagoran ƙungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, afuwa bayan da kotu ta yanke masa hukuncin ɗaurin rai da rai. Kungiyar ’Yan Majalisar Wakilai daga yankin Kudu maso Gabas ta yi kira ga Shugaba Tinubu da ya yi amfani da ikon da kundin tsarin mulki ya ba shi, wajen yi wa Nnamdi Kanu afuwa wanda kotu ta same shi da laifin ta’addanci. Alƙali James Omotosho na Babban Kotun Tarayya da ke Abuja ne ya yanke hukuncin, inda ya same shi da laifi a kan tuhumar da ake masa guda bakwai, sannan ya yanke masa hukuncin daurin rai da rai. Tuni aka tura Nnamdi Kanu...
Shugaban kasar Sudan kuma babban kwamandan sojojin kasar Janar Abdulfattah Alburhan, ya yi watsi da shawarar Amurka ta kawo karshen yaki a kasarsa wanda ya lakume rayukan mutane da dama, ya kuma raba kasar gida biyu a cikin watanni kimani 30 da suka gabata. Shafin yanar gizo na labarai ‘AfricaNews’ ya nakalto Burhan yana fadar haka a ranar Lahadi jim kadan bayan ganawarsa da tawagar kasar Amurka wacce ta gabatar masa da shawarar, ya kuma bayyana ta a matsayin mafi munin shawarar tsagaita budewa juna wuta da aka gabatar masa ya zuwa yanzun. Burhan ya zargi Massad Boulos mai bawa shugaban kasar Amurka a kan al-amuran nahiyar Afirka da da kokarin rusa sojojin kasar Sudan da kuma bawa yan tawaye...
Shugaban kasar Sudan kuma babban kwamandan sojojin kasar Janar Abdulfattah Alburhan, ya yi watsi da shawarar Amurka ta kawo karshen yaki a kasarsa wanda ya lakume rayukan mutane da dama, ya kuma raba kasar gida biyu a cikin watanni kimani 30 da suka gabata. Shafin yanar gizo na labarai ‘AfricaNews’ ya nakalto Burhan yana fadar haka a ranar Lahadi jim kadan bayan ganawarsa da tawagar kasar Amurka wacce ta gabatar masa da shawarar, ya kuma bayyana ta a matsayin mafi munin shawarar tsagaita budewa juna wuta da aka gabatar masa ya zuwa yanzun. Burhan ya zargi Massad Boulos mai bawa shugaban kasar Amurka a kan al-amuran nahiyar Afirka da da kokarin rusa sojojin kasar Sudan da kuma bawa yan tawaye...
Gwamnonin jihohin kudu maso yammacin Najeriya sun bada sanarwan cewa lokacin kafa yansandan jihohi ya yi, har’ila yau dakuma karfafa kula da dazuzzukan kasar saboda magance matsalolin tsaro da suka addabi kasar. Jaridar Daily Trust ta nakalto gwamnonin na fadar haka a jiya Litinin bayan taron gwamnonin shiyar kudu maso yammacin kasar da suka gudanar a birnin Ibadan na jihar Oyo. Gwamnonin 6 sun yi kira ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya aika masu gadin dazuzzuka a shiyar kudu maso yammacin kasar don tabbatar da tsaronsu , sannan gwamnonin jihohin guda shida ne zasu dauki nauyin kula da jami’an tsaron. Labarin ya kara da cewa shugaban gwamnonin kuma gwamnan jihar Lagos Babajide Sanwo-Olu ne ya karanta jawabin bayan taron...
Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnan Jihar Jigawa, Umar Namadi, ya kaddamar da titi mai tsawon kilomita 13 da rabi, da ya tashi daga Sada zuwa Danakari zuwa Unguwar Malam Kuda, zuwa Magina, a Karamar Hukumar Yankwashi ta jihar. A jawabinsa wajen bikin kaddamarwar, Namadi ya bayyana kudirin gwamnatinsa na ci gaba da samar da muhimman abubuwan more rayuwa a karkara domin inganta harkokin tattalin arzikinsu. Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa Gwamna Umar Namadi ya ce titin, wanda aka gina akan kudi Naira biliyan 1 da miliyan 690, na daga cikin manyan ayyukan gine-ginen hanyoyi 48 da gwamnatinsa ta bayar a shekarar 2024. A cewarsa, titin zai hada al’ummomin karkara na Sada, Danakari, Unguwar Malam Kuda da Magina. Ya...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A shekarar 2014, bayan tashin hankalin da ya biyo bayan sace ɗaliban Chibok da kuma yawaitar hare-hare kan makarantun yankin Arewa maso Gabas, gwamnatin tarayya tare da haɗin gwiwar ƙasashen duniya ta ƙaddamar da wani muhimmin shiri mai suna Safe School Initiative. Manufar wannan shiri ita ce tabbatar da cewa dalibai suna iya zuwa makaranta cikin tsaro ba tare da fargabar hare-hare daga ‘yan ta’adda ko ‘yan bindiga ba. NAJERIYA A YAU: Ba A Yi Ma Nnamdi Kanu Adalci Ba- Emmanuel Kanu DAGA LARABA: Hanyoyin Da Suka Kamata A Bi Wajen Ceto Daliban Kebbi Da Aka Sace Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne akan wannan shiri da...
Ana zargin wasu ’yan bindiga da kashe wani fitaccen ɗan kasuwa, Alhaji Muhammad Bakoshi, lokacin da suka kai hari garin Zalau da ke Ƙaramar Hukumar Toro a Jihar Bauchi. Bayan kai hari, sun sace ɗaya daga cikin matansa, Hannatu Muhammad. Tinubu ya dakatar da ’yan sanda daga tsaron manyan mutane a Najeriya An ceto mutum 38 da aka sace a cocin Kwara — Tinubu Wani mazaunin yankin, Shamsuddeen Hashimu Zalawa, ya shaida wa Aminiya cewa ’yan bindigar sun je gidan mutumin da tsakar dare. Ya ce sun dinga harbe-harbe ba ƙaƙƙautawa, lamarin da ya jefa al’ummar yankin cikin firgici. Ya ƙara da cewa sun nufi gidan Bakoshi kai-tsaye, wanda hakan ya sa wasu ke zargin ko turo su aka yi....
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe, ta ce labarin da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta na kai wa cocin ECWA da ke Kashere hari, ba gaskiya ba ne. Kakakin rundunar, DSP Buhari Abdullahi ne, ya bayyana haka, inda ya ce sun bincika tare da gano cewar jita-jita ce. Ya ce DPO na Pindiga da shugaban ofishin ’yan sanda na Kashere, sun tuntuɓi wani dattijo da ya halarci cocin domin yin addu’a a ranar Lahadi. Dattijon ya shaida musu cewa babu wani abu da ya faru, kuma ’yan sanda suna harabar cocin tun safe a domin kula da sha’anin tsaro kamar yadda suka saba. Rundunar ta ce yaɗa irin wannan jita-jitar na iya tayae da hankalin jama’a. Ta kuma ce ta...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi, ta tabbatar da mutuwar wasu jami’anta guda biyar a ƙauyen Sabon Sara da ke Ƙaramar Hukumar Darazo, sakamakon harin da wasu ’yan bindiga suka kai. Kakakin rundunar, CSP Ahmed Wakil ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a ranae Lahadi. An ceto mutum 38 da aka sace a cocin Kwara — Tinubu Ɗalibai 50 da aka sace a Neja sun kuɓuta — CAN “‘Yan sanda biyar sun rasu, biyu sun jikkata, amma an yi nasarar kashe wasu daga cikin ’yan bindigar a ƙauyen Sabon Sara, Ƙaramar Hukumar Darazo, a jihar Bauchi.” Wakil, ya ƙara da cewa, “Ma’aikatanmu suna jajircewa kuma sun samu nasarar kashe wasu daga cikin ’yan bindigar yayin musayar wuta.” Ya bayyana ’yan...
Babban magatakardar MDD Antonio Guterres ya yi kira ga shugabannin kasashen duniya da suke taro a birnin Johannesburg na kasar Afirka Ta Kudu da su warware matsalar rashin daidaito a cikin harkokin kasuwanci a tsakanin kasashe. Babban magatakardar MDD wanda ya gabatar da jawabi a wurin taron na G 20 ya yi Ishara da gibin kasuwanci da ake da shi a tsakanin kasashen da su ka ci gaba da masu tasowa wanda ya kamata a san yadda za a magance shi. Antonio Gutrres ya kuma ce: “Wani abu guda daya wanda zan iya bayar da tabbaci a kansa shi ne cewa ofishin babban magatakardar MDD zai yi duk abinda zai iya yi domin yin gyara a cikin rashin daidaito da...
Zabebben magajin garin birnin NewYork na kasar Amurka Zohran Mamdani, a haduwarsa ta farko da shugaban kasar Amurka Donal Trump a birnin Washington ya bayyana cewa HKI tana aikata kissan kiyashi a gaza, sannan mutanen NewYork basa son ganin gwamnatin Amurka tana amfani da kudaden harajin da suke biyu wajen tallafawa gwamnati wacce take aikita kissan kiyashi a duniya. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto magajin garin birnin NewYork musulmi na farko na cewa yana son shugaban Trump ya karkata kudaden da yake kashewa kan sojojin Amurka wadanda suke yake-yaken da masa da wani amfani ga mutanen kasar Amurka zuwa magance talaucin da Amurka suke fama da shi a cikin gida musamman masu kwana a waje a...
Gwamnatin Tarayya ta bada umarnin rufe makarantu arba’in da daya saboda matsalolin tsaro. A wata takardar sanarwa da aka aikewa dukkan Shugabannin makarantu, wadda Daraktan Makarantu Manyan Sakandare na Ma’aikatar Ilimi ya sanya wa hannu, gwamnati ta bayyana cewa sakamakon ƙalubalen tsaro da ake fuskanta a wasu sassan ƙasar nan da kuma buƙatar kare duk wani yunkurin hari, Ministan Ilimi ya amince a rufe makarantun nan dltaje. Ga jerin makarantu da abin ya shafa: Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya, Minjibir, Jihar Kano Kwalejin Fasaha ta Tarayya, Ganduje, Jihar Kano Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya, Zariya, Jihar Kaduna Kwalejin Fasaha ta Tarayya, Kafanchan, Jihar Kaduna Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya, Bakori, da wacce ke Bwari, Abuja. Kwalejin Fasaha...
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na duniyar mu a yau. Shiri wanda yake kawo maku labarai masu muhimmanci a makon da ya gabata wadanda suka shafi siyasa, tattalin, arziki, zamantakewa tsaro da sauransu, inda muke masu Karin bayani sannan daga karshe mu ji ra’ayin masana dangane da su da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu nay au /////… Madalla, masu sauraro zamu fara shirimmu da labarimmu na farko wanda yake cewa majalisar gwamnoni a hukumar IAEA ta amince da wani kuduri na takurawa JMI a taron da ta yi a ranar Alhamis 22 ga watan Nuwamban da muke ciki. Kuduri wanda kasashen E3 ko Traiko na...
Shugaban kasar Ukrain Volodymyr Zelensky ya fito fili ya bayyana cewa bai amince da sabon shirin shugaban kasar Amurka Donal Trump na kawo karshen yaki a kasarsa. Ya kuma bayyana cewa kasar Ukraine tana cikin mafi munin hali a tarihin kasar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana fadar haka a jiya Jumma’a ya kuma kara da cewa shugaban kasar Amurka yana takurawa kasarsa ta amince da al-amura guda 28 da ya gabatar wanda a fadinsa zai kawo karshen yakin shekari kimani 3 wanda kasarsa take fafatawa da kasar Rasha. Labarin ya kara da cewa daga cikin al-amuran da shugaban ya gabatar a wannan shirin kawo karshen yaki a Ukraine sun hada da amincewa da zaben...
Yan wasan kasar Iran sun kammala gasar wasannin sada zumunci na kasashen musulmi wanda aka kammala a birnin Riyad na kasar Saudiya tare da lambobin yabo har 81. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa wannan ya nuna cewa kasar Iran na daga cikin kasashen musulmi wadanda suke da kwarewa a wasannin motsa jiki daban daban. Labarin ya kara da cewa an gudanar da wasannin ne daga ranar 6 ga watan Nuwamba zuwa 21 ga watan. Tare da fara wasu wasannin daga ranar 3 ga watan. Kasar Saudiya wacce ta dauki bakwancin wadan nan wasannin motsa jiki ta sami nasarar tattara yan wasannin motsa jiki na kasashen musulmi a duniya a cikin kwanaki kima 20 da suka...
Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnatin Jihar Jigawa ta tabbatar da bada cikakken goyon bayanta ga Kwalejin Aikin Noma ta Gwamnatin Tarayya da ke Kirikasamma. Gwamna Umar Namadi ya bayar da wannan tabbaci ne lokacin da ya karɓi tawagar gudanarwar kwalejin ta farko, ƙarƙashin jagorancin shugabanta, Dr. Muhammad Yusha’u Gwaram, yayin ziyarar girmamawa da suka kai Gidan Gwamnati da ke Dutse. Ya taya shugaban kwalejin da tawagarsa murna, inda ya bayyana nadin nasu a matsayin tarihi kuma mai matuƙar muhimmanci. Malam Umar Namadi ya ƙara da cewa kafa sabuwar cibiyar ilimi aiki ne babba, yana mai bayyana tabbacin cewa mutanen da aka zaba don fara gudanar da kwalejin za su taka rawar gani. “Kafa sabuwar cibiyar ilimi ba abu ba ne...