2025-06-15@23:27:17 GMT
إجمالي نتائج البحث: 22

«manoma da makiyaya»:

    Jami’an tsaro sun isa yankin domin hana rikicin ci gaba da kuma tabbatar da zaman lafiya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Wasu ’yan bindiga sun kashe wasu makiyaya biyu da suka haɗa da: Mudda Shannon da Suleiman Bello, yayin da suka raunata ɗaya a ƙauyen Kurmin Lemu da ke ƙaramar hukumar Kagarko ta Jihar Kaduna. Wani ɗan unguwar Kurim Lemu mai suna Shuaibu Ibrahim ya ce, lamarin ya faru ne a ranar Alhamis da misalin ƙarfe 12:07 na tsakar dare. Ɗalibai sun maƙale lokacin da gini ya rufta suna jarrabawa Ko kwabo ban ciyo bashi ba tun da na zama Gwamnan Kaduna – Uba Sani Ya ce, ’yan bindigar da suka zo adadi mai yawa tare miyagun makamai sun mamaye sansanin makiyayan inda suka buɗe wuta, inda suka kashe biyu daga cikin makiyayan nan take. Ya ce, ɗaya daga cikin makiyayan...
     Rhotanni daga jihar ta Beneu sun ce a wani hari da makiyaya su ka kai a yankin Gwe ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 42. Mahukunta a yankin sun sanar da cewa; an gano gawawwakin mutane 32 da aka kashe sanadiyyar harin da aka kai kauyukan Ahume da Aodona, yayin da aka gano wasu gawawwakin mutane 10 a kauyukan Tyolaha, Tse-Ubiam, kamar yadda shugaban karamar hukuma   Gwer ta yamma Victor Omnin ya bayyana. Shugaban karamar hukumar ya bayyana wa ‘yan jarida abinda ya faru da cewa; na takaici ne, domin a wannan lokacin da muke Magana ana ci gaba da gano gawawwaki.” Jahar Benue tana tsakiyar kasar Nigeria ne a yankin da ake kira : Middle-Belt”. An kuma dauki shekaru masu...
    Wasu makiyaya biyu sun rasu bayan da wasu da ba a san ko su wane ne ba suka buɗe musu wuta a kusa da ƙauyen Tahore, da ke Ƙaramar Hukumar Bokkos, a Jihar Filato. Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne yayin da mamatan ke dawowa daga kasuwar Maikatako a kan babur. Yadda ’yan sanda suka kashe dan fashi suka kwato bindigogi 7 a Abuja Harin ’yan bindiga ya sa Zamfarawa sun koma kwana a jeji Shugaban Ƙungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah a Jihar Filato, Ibrahim Yusuf Babayo, ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya bayyana sunan mamatan a matsayin Umar Sa’idu da Rashida Yakubu. Ya ce lamarin ya faru ne da yamma, kuma ya sanar da manyan jami’an tsaro ciki...
    Ana zargin wasu makiyaya sun kashe mutane 15 a yankunan Ogwumogbo da Okpo’okpolo na ƙaramar hukumar Agatu dake jihar Benuwe. Majiyoyinmu sun bayyana cewa waɗanda aka kashe sun kasance ‘yan kasuwa ne da ke dawowa daga kasuwar Oweto a Agatu lokacin da maharan suka fito daga daji suka harbe su, inda suka kashe 15 nan take. An Gudanar Da Taron Zaman Lafiya Tsakanin Manoma Da Makiyaya Ƙungiyar Fulani Makiyaya Ta Nuna Damuwarta Na Ɓacewar Mataimakin Shugabanta Tsohon mataimakin shugaban ƙaramar hukumar Agatu, John Ikwulono, ya tabbatar da harin da aka kai wa ‘yan kasuwar a ranar Asabar da yamma, inda ya bayyana cewa maharan sun kwace kuɗaɗe da kayayyakin waɗanda aka kashe kafin su gudu cikin daji. “Har yanzu wasu...
    Wani rikici da ya ɓarke tsakanin manoma da makiyaya a ƙauyen Chikuriwa da ke Ƙaramar Hukumar Nangere a Jihar Yobe, ya yi sanadin mutuwar mutum ɗaya tare da jikkata wasu. Rahotanni sun nuna cewa rikicin ya faru ne da yammacin ranar Litinin, 13 ga watan Mayu, 2025 bayan da wani makiyayi ya shigar da shanunsa cikin gonar wani manomi, abin da ya tayar da rikici. Yajin aiki: Jami’ar KASU ta shiga rudani BUA ya yi alkawarin karya farashin shinkafa A lokacin da rigimar ta ɓarke, an harbi wani manomi mai suna Babayo Maina Osi da kibiya a goshinsa, wanda hakan ya jikkata shi. Wata majiya daga ƙauyen ta ce rikicin ya ƙazanta sosai har ya rikiɗe zuwa faɗa tsakanin manoma...
    A wasu rahotanni sun ce an kashe makiyayi guda ɗaya da shanu sama da 100 a wasu hare-hare da aka kai hari kan makiyaya a wasu ƙauyuka biyu da ke ƙananan hukumomin Jos ta Kudu da Jos ta Arewa a Jihar Filato. Hare-haren da ake zargin wasu ’yan bindiga ne da suka buɗe wa makiyaya wuta a lokacin da suke kiwo, wanda ke nuna rashin tsaro a yankunan da aka daɗe ana fama da rikice-rikice tsakanin manoma da makiyaya, lamarin da ke janyo asarar rayuka. Dalilin da ya sa gwamna Bala ya yi ƙoƙarin mari na – In ji Minista Wuta ta kashe ɓarawon wayar lantarki a Jigawa Sakataren Ƙungiyar Miyetti Allah Ƙungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti Allah (MACBAN) na...
    Shugaban kungiyar ya yi magana Ibrahim Yusuf Babayo,Shugaban kungiyar  Miyetti Allah masu kiwon dabbobi na kasa ya bayyanawa jaridar karshen mako cewar dukkan hare- haren da ake kaiwa dabbobin da kuma kashesu an sanar da jami’an tsaro daban- daban,da suka hada da Kwamanda na rundunar soja ta,3 kuma kwamandan Operation Safe Haben (OPSH), Manjo- Janar Foluaho Oyinlola,Kwamishinan‘yansanda na Jihar, Emmanuel Adesina,da kuma darekta na bangaren jami’an farin kaya DSS. Ya ce jami’an tsaro da suke a bangaren Karamar Hukuma an kai su can wuraren da aka kai hare- haren domin su ganewa idanunsu yadda lamarin yake. Sa Wa Shanu 110 guba Kamar yadda jagorancin kungiyar MACBAN a Jihar yace,an kashe Shanu a kalla 110 ta hanyar guba a hare- haren...
    Mazauna gundumar Kufana a Ƙaramar Hukumar Kajuru ta Jihar Kaduna sun shiga cikin fargaba sakamakon jerin hare-haren ’yan bindiga da ya yi sanadiyyar sace mutane biyar da kuma kwashe shanu 1,200 cikin kwanaki hudu. Babban Jami’in Gundumar, Mista Stephen Maikori, ya tabbatar da faruwar hare-haren a ranar Laraba. A cewarsa, lamari na farko ya faru ne a daren Talata, 8 ga Afrilu, 2025, lokacin da ’yan bindiga suka kai hari kauyen Mashigi Boka-Libere, wani matsugunin Fulani, da misalin karfe 10 na dare. Maikori ya ce maharan sun kwashe garken shanu guda 12, inda kowanne garke yake da kimanin shanu 100, wanda ya kai jimillar dabbobi 1,200. Dangote: Har yanzu gidajen mai ba su rage farashin mai ba Najeriya da gwamnatin...
    Kungiyar Afica city of Refugee ta gabatar da taron bukatar da kuma muhimmancin samun zaman lafiya a tsakanin Makiyaya da Manoma a garin Saka wanda ya ke karkashin jagorancin gundumar ci gaba ta Karshi da Uke,Karamar Hukumar Karu ta Jihar Nasarawa saboda a tattaunakan lamarin daya shafi zaman lafiya tsakanin Fulani Makiyaya da kuma Manoma. Mutane da dama ne suka samu halartar taron wanda aka yi a Saka a makarantar Sakandare ta Saka daga cikin Shugaban kungiyar zaman lafiya tsakanin Musulmi da Kirista na Karamar HUkumar Karu Reberend Timothy. Sin Ba Za Ta Razana Da Zuwan Yakin Cinikayya Ba Huawei Ya Daddale Yarjejeniya Da Kenya Don Habaka Kwarewar Ma’aikatan Kasar A Fannin Dijital Reberend Justin darekta wanda kuma shi...
    Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang ya ce hare-hare da kashe-kashen da ake yi a wasu sassan jihar wasu ne ke ɗaukar nauyinsu ba rikicin manoma da makiyaya ba ne. Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin bikin baje kolin kayayyaki da fasaha da ƙungiyar Tincity Fashion Week ta shirya a daren Juma’a a Abuja. An ceto fasinjoji 14 a hannun ’yan bindiga, 3 sun rasu a Benuwe Sabon harajin Trump zai jefa tattalin arziƙin duniya cikin matsala — WTO Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya NAN ya bayar da rahoton cewa, a ranar 2 ga watan Afrilu, wasu ’yan bindiga sun kai hari a ƙauyukan Manguno, Daffo da Josho na ƙaramar hukumar Bokkos  ta jihar. Maharan sun kashe mutane da dama tare...
    A Bikin Yawan Sallah na Jafi da aka yi a fadar Sarkin Gombe, Mai Martaba Alhaji Abubakar Shehu Abubakar III, ya yi kira ga manoma da makiyaya da su zauna lafiya da juna. Sarkin ya ce zaman lafiya shi ne ginshiƙin ci gaba, kuma haɗin kai tsakanin manoma da makiyaya zai hana rikice-rikice da ke barazana ga jihar. Matashi ya kashe jami’in tsaron Sarki Sanusi II a Kano Gwarzon gasar Alƙur’ani ya kuɓuta daga hannun ’yan bindiga a Katsina “Ina roƙon manoma da makiyaya da su zauna lafiya don guje wa rigingimu. “Kowa yana da haƙƙin tabbatar da zaman lafiya domin hakan na kawo ci gaban tattalin arziƙi da walwalar al’umma,” in ji Sarkin. Haka kuma, ya tabbatar da cewa...
    Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada bukatar bin dokar da ta hana kiwon dare da makiyaya ke yi a fadin jihar domin rage hadurra a tituna, wanda ke haddasa asarar rai ko shiga mawuyacin hali a sanadiyar raƙuman da ke bi ta manyan tituna. Gwamna Umar Namadi ya bayyana hakan yayin da ya karbi bakuncin tawagar Kungiyar Makiyayan Raƙuma ta Yammacin Afirka a ziyarar girmamawa da suka kai Fadar Gwamnati a Dutse.   Ya ce gwamnatin ta himmatu matuka wajen ganin ta kula da lafiyar al’ummar jihar. Malam Umar Namadi ya kara da cewa, wannan gwamnati tana da masaniya kan haramtattun ayyukan wasu makiyaya, musamman waɗanda ke shigowa daga ƙasashe makwabta. Ya bayyana shirin gwamnatin jihar na...
    Domin tabbatar da zaman lafiya, an tura ƙarin jami’an tsar tare da haɗin gwiwar sojoji domin daƙile tashin hankali. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    “Wasu masu kiwon, suna zuwa shagunan sayar da magani ne su sayo su rika bai wa dabbobin da suka harbu da wata kwayar cuta, ba tare da yin la’akari kan adadin magungunan da ya kamata su ba su ba”, in ji Ngulukun. Ana kuma bukatar masu kiwon su dakar da bai wa dabbonin nasu magunguna daidai da lokacin da misali, kajin gidan gona ke shirin fara yin kwai ko kuma lokacin da shanu ke shirin fara samar da madara, domin kare lafiyar mutane. Sai dai, abin takaici shi ne, akasarin masu kiwon; ba sa kiyaye irin wadannan lokuta, wanda hakan ke shafar lafiyar mutanen da suka yi amfani da irin wadannan dabbobi. Kazalika, yawan bai wa dabbobin magungunan barkatai don...
    Gwamnatin jihar Jigawa ta ce daga cikin wuraren kiwo guda 400 da ke jihar, ta duba 57 domin dakile rikicin manoma da makiyaya a jihar.   Gwamna Umar Namadi ya bayyana haka ne a wajen bude taron tuntubar masu ruwa da tsaki kan sauye-sauyen kiwo tare da hadin gwiwa da kwamitin shugaban kasa na aiwatar da gyara harkokin kiwon dabbobi da aka gudanar a Dutse, babban birnin jihar.   Ya ce baya ga samar da tsarin doka na kare wuraren kiwo, manufar za ta kuma tabbatar da amfani da albarkatun kasa mai dorewa a jihar.   Gwamnan ya ce gwamnatin sa ta kuma dauki ma’aikatan kiwon lafiyar dabbobi 300 na al’umma domin su samar da ayyukan ci gaba ga manoma...
    Wani matashi ɗan shekara 32 ya soka wa ɗan uwansa wuƙa ya saboda Naira 700 a Unguwar Zara da ke Yankin Babban Birnin Tarayya. Wani shaida a unguwar ya bayyana cewa lamarin ya faru ne bayan wanda ake zargin ya kutsa ɗakin yayan nasa ya ɗauke masa Naira 700 daga aljihunsa. Ana zargin wanda a ya yi aika-aikan ya shiga dakin ne bayan wan nasa ya tafi Sallar Isha’i Bayan ya dawo bai ga kuɗin ba, ya yi zargin ƙanin nasa da ɗaukar, ya bi sahunsa, inda ya riske shi a wata mashaya ya je sayen tabar wiwi. Ba ni lokacin cacar baka da El-Rufai —Nuhu Ribadu NAJERIYA A YAU: Azumin Ramadana: Ko Kun San Dabinon Da Kuke Shan Ruwa...
      Kungiyar Tarayyar Makiyaya ta CORET ta ce zata tallafawa yara makiyaya 1,600 a makarantun makiyaya guda shida a Jihohin Kaduna da Jigawa a wani yunƙuri na rage ƙarancin abinci da rashin ingantaccen abinci.   Sakataren Janar na CORET, Mohammed Bello Tukur ne ya bayyana hakan a lokacin ƙaddamar da shirin ciyar da ɗalibai na haɗin gwiwa a Laddauga, wurin kiwon dabbobi na Kachia a Jihar Kaduna.   Ya bayyana cewa, manufar wannan shiri ita ce tallafa wa shirin ciyar da ɗalibai na makarantun makiyaya.   Sakatare Janar ya ƙara da cewa kashi 60 na waɗanda za su amfana ‘yan mata ne, kuma shirin zai ƙarfafa ilimin kyawawan ɗabi’u a fannin abinci mai gina jiki, tsafta, tsabtace muhalli, da kuma...
    Ƙungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah (MACBAN) ta yi iƙirarin cewa wasu ’yan bindiga sun sace sama da shanu miliyan huɗu na mambobinta musamman a yankin Arewa maso Yamma. Shugaban Ƙungiyar MACBAN na ƙasa, Baba Usman ne ya bayyana hakan a yayin ƙaddamar da sababbin zaɓaɓɓun shugabannin ƙungiyar na jiha a Jihar Kebbi. ’Yan bindiga sun kashe mutum 12, sun sace wasu a Zariya Hisbah ta rufe gidajen rawa a Katsina Ya ce, ɓarayin shanu na yawan kai wa Fulani makiyaya hari, lamarin da ke haddasa asarar rayuka da dukiyoyi. Usman ya jaddada cewa, ana yawan sauya fahimtar Fulani makiyaya da kuma yin kuskuren sanya su a matsayin masu tayar da fitina, inda ya buƙaci jama’a su riƙa ganin su...
    Gwamnatin Jihar Gombe ta horar da makiyaya 684, ciki har da nakasassu, mata, matasa, da tsofaffin ma’aikata, kan sabbin dabarun kiwon awaki da kasuwancinsu. Wannan horo ya gudana ne ƙarƙashin shirin Livestock Productivity and Resilience Support (L-PRES). Rigima ta sake kaurewa tsakanin PDP da APC a Zamfara Mutum 11 sun kuɓuta daga hannun Boko Haram a Borno Kwamishinan Aikin Gona, Kiwo, da Hada-hadar Ƙungiyoyi na Jihar Gombe, Dokta Barnabas Malle ne, ya jagoranci ƙaddamar da horon a Gombe. Yayin da yake jawabi, ya jaddada ƙudirin gwamnatin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, na inganta kiwon dabbobi da tallafa wa al’umma. Ya ce: “Shirin ya dace da manufofin gwamnati na bai wa kowa damar cin gajiyar shirye-shiryen da ake gudanarwa.” Shugaban shirin L-PRES...
    Makiyaya sun koka bisa abin da suka kira tsangwama da tsana da wasu manoman tabar wiwi ne suke nuna musu tare da yi musu barazanar ƙone gidajensu a inda suke zaune shekaru aru-aru. Makiyaya Fulani sun yi ƙorafi ne bayan manoman tabar wuri sun kafa musu ƙahon zuƙa a inda suke zaune a yankin Oja-Badun da ke Ƙaramar Humumar Eleyele a Jihar Oyo, daura da garin Ogumaki na Jihar Ogun. Shugaban Fulanin yankin, Alhaji Muhammadu Wakili ya shaida wa Aminiya cewa, jagoran manoman tabar wiwi a yankin ya sa wa Fulani makiyayan karan tsana, bayan da suka bai wa jami’an tsaro bayanan cewa, suna noma tabar wiwi a yankin. Ya ce lamarin ya kai ga ’yan sanda sun kama yaran...
    An shawarci gwamnonin jihohin Arewa da su yi koyi da gwamnatin jihar Neja wajen magance matsalolin rikicin makiyaya da manoma a yankin domin samun ci gaba mai dorewa. Shugaban kungiyar Miyetti Allah ta kasa MACBAN, Dokta Baba Usman Ngelzarman ne ya bayar da wannan shawarar a wajen wani taro na musamman na karramawa  tare da tabbatar da lakabin gargajiya ga wasu fitattun Fulani guda biyu a jihar Neja, da aka gudanar a fadar Sarkin Minna. Dokta Baba Usman Ngelzarman ya bayyana cewa, hanyar da Gwamna Mohammed Umar Bago na Jihar Neja ya bi na samar da sakamako mai kyau, ta yadda za a rage yawan rikicin makiyaya da manoma a jihar abin a yaba ne matuka. A cewarsa hakan ya...
۱